* MURAYU A TARE *
Mom Islam
Book2 chapter 1-2
https://arewabooks.com/chapter?id=64ae79a61bfbeb67a19dea9e
Kafin su fita a ƙauyen kan Prince ya fara hayaƙi saboda ihu da jagulen maganar ta, sbda ba ko wacce yake ganewa ba,
Tunda suka hau titi ta kamo masa hannu saura kaɗan motar su ta juye, sai cewa take "anguwar joma ki mayar dani gida inga halin da akuyata take ciki hay yanzu na tuna"
Wani banzan kallo Prince ya bita dashi, sbda ta gama cika masa ciki,
Har sukayi rabin tafiya suka zo gidan waya batace dashi ƙala ba, sai kumbure-kumbure take ita a dole sunyi faɗa, shikam yaji daɗi sosai dan koba komai ze samu ya huta da wannan surutun nata, parking yayi a gurin masallaci harda inda mata suke sallah, cikin sanyin muryarsa yace "ki fito kizo muje kiyi alwalah lokacin Azhar yayi"
"Aradun Allah sai anyi la'asar saboda sunfi zumunci"
Dan Allah kuyi following ɗina
https://arewabooks.com/u/momislam11