Part 2

271 13 1
                                    

*RIJIYA TA BA DA RUWA...?*
     _GUGA YA HANA_
                              
*MALLAKAR:-OUM MUMTAZ* 

*WATTPAD@ Oum-Muntaz123*
*INSTAGRAM @itz_me_real_oum_mumtaz*      

           *charpter 2*

********Wanka ta fara gabatarwa,sannan ta shafe jikinta da daddad'an lotion nata mai sanyin k'amshi had'i da fesa turaren ta body spray,sannan ta sanya riga da wando matsattsu da suka kama jikinta sosai,wanda hakan ya taimaka wajen bayyanuwar surar jikinta da kan iya girgiza zuciyan 'yan maza idan suka yi katari da shi.

Gashin kanta kuma ta raba su kashi biyu ta kuma tufke shi da ribbon,sannan ta fito daga d'akin nata hannun ta rik'e da laptop nata samfarin apple da kuma wayar ta samfarin Samsung da ba ta cika amfani da shi ba.

Zaune ta tadda wata hamshak'iyar mata akan wani kujera na alfarma da ke cikin babban parlon gidan nasu,wacce kallo d'aya mutum zai yi mata ya fahimci tsantsar wadatar da ke tattare da ita na arzikin duniya saboda yadda 'yay'an banki suka ratsa ta,tana sanye ne da wani d'anyen leshi y'an ubansu,sannan fuskarta kuma sanye yake da wani glashin ta mai karama idanuwa (medicated).

"Momina sannu da hutawa" Zulaykha ta fad'a a lokacin da ta yi ma kanta mazauni a gefen wannan matar data kira da Mamy , "yawwa sannu da dawowa uwar masu gidan,kin dawo lafiya?"  Matar ta tambayi Zulaykha da ke danna wayarta.
"lafiya" Zulaykha ta fad'a ba tare da ta kalli matar ba,wanda hakan ya sa matar yi ma Zulaykha wani irin kallo an kasar ido tana taunar labbanta.

Sun yi zaman kurame ne a wajen ko waccen suna famar danna waya inda daga k'arshe ma dannar system nata Zulaykha ta fara yi inda take ta faman settling na wasu files da Musty ya aiko mata tun daren jiya,bacci ne ya d'auke ta a wajen ba tare da ta ankara ba,wanda hakan ya sa Mami mik'ewa daga kan kujerar ta gyara mata kwanciyar ta badan ranta ya so ba,sai dan babu yadda ta iya,ta yi wucewarta d'aki.

******** Wata mata ce fara tas da ita kyakkyawa na k'in k'arawa ke tsaye bakin wani madafa ta langa- langa da hayaki yabi ya turni ke cikin madaidaicin gidan take ta faman zuba sababi da ke had'e da madarar tsiwa ma mijinta mai suna Waali da shi kuma yake rakube a gefe d'aya kaman wanda yake tsoron ta fuskarsa na bayyana tsananin tashin hankalin da yake ciki kamar ya yi kuka saboda soyayyar matar tasa da ke ta faman azaftar da shi da ya sa shi gagara d'aukan mummunar mataki akan ta dangane da irin cin kashi da take masa.

"Wallahi ni ban ta'ba ganin mutum mai mataccen zuciya irin taka ba Wali ,ga wannan shegen bakin talaucin naka da nake da tabbacin harda shi wajen ba da gudun mawar mutuwar zuciyarka,aure ne na ce ba na yi ka ba ni takarda ta in tafi inda ake maraba da ni,da za a ba ni na ci mai kyau,na sha mai kyau na kuma kwana a mai kyau idan da hali ma har na tsakuro maka wani abin da zai fishe ka a rayuwa amma kana man wannan bakin ciki mararan a filin Allah? Gaskiya ni kam na gaji ka san yadda za ka yi da ni ehe! Aure ne na ce a yi a a sauwak'e mini na huta da wannan azababbiyar talaucin da ya-k'i-ci-ya-k'i- cinyewa!"

Wannan matar ke fadi tana ta faman girgiza kwankwaso had'i da murguda baki ga kuma uban gumin da ke tsatstsafo mata ta farar fatar ta saboda hayak'in itacen daya tirnike gidan da kuma zafin ranar da ta hade wuri guda ya had'e kuma da yanayin zafin cikin garin Maiduguri da ake ya ba da wani irin fitinannen zafi mai gasa ma mutum aya a hannu.

"Haba ~ALINA~! dan Allah ki yi hak'uri akan wannan k'udirin naki,na san Allah ba zai barni haka nan ba,sabida ke ma shaida ce dangane da yadda nake ta fafutukar neman aiki amma abin ya-k'i-ci-ya-k'i- cinyewa saboda yanayin hali irin na k'asar mu! Idan kika matsa mini na sake ki ya kike so na yi rayuwa ne? Kin san ba ni da kowa! Mamana,Babana da kuma yan uwana duk ban da su sai ke kad'ai kika rage man idan ke ma kika kufce mini wa zan nuna ma duniya a mazaunin nawa Alina? Dan Allah ki rufa mini asiri na rok'e ki ba dan ni ba sai dan Allah ki dubi girman irin maraicin da zan afka idan ke ma kika guje ni"

Wali ne ya yi wannan maganar wasu irin hawaye masu zafin gaske na zubowa daga cikin idanunsa a lokacin da yake durk'ushe a wannan guri yana bai ma Alina hak'uri kan kar ita ma ta tafi ta bar sa maraicin ya yi masa yawa.

Tabbas idan ta ce ba ta ji tausayin sa a lokacin ba ta yi zuciyarta karya,amma kuma sai dai kwad'ayin son abin duniya da kuma hangen nesa na rud'ar ta, har ma yake ingizata izuwa ga hanyar da zata yi da-na-sani daga baya,wanda hakan ya sa ta d'an shafa kanta lafiya ta buga wani uban tsaki ta fad'a d'akin ta ba tare da ta sake wai wayar tuwon dawar da take yi ba cikin madafar.

********Sai wuraren la'asar kamin ta farka daga baccin da take yi wanda a lokacin ma wajen karfe hud'u da kwata,d'akin ta wuce sannan ta shiga bayi ta d'auro alwala tare da shifida sallayarta a d'aki ta tada sallar la'asar nata.

Dirin motocin da ta jiyo ne a lokacin da a idar da sallah ya sa ta fitowa da gudun ta saboda ta san Abbanta ne ya dawo gida,haka nan ta mak'alk'ale Abban nata tun daga filin gidan nasu da ke kawace da shukoki na fulawowi masu kyan gaske kamin suka shigo. A falo suka tarda mamy ta sake shek'o wani wankan sai zuba k'amshi take abinta fuskarta na fidda zallar murmushi tana yi ma mijin nata sannu da zuwa,sai kuma ta gintse sa a lokacin da ta ga yadda Zulaykha ta mak'alkale mahaifin nata kamar za ta koma cikinsa shi kuma yana biye mata.

"Maman Abbanta ki bar shi haka nan ya huta mana idan ya so sai ki dawo ku sake gaisuwar ko?" Mamy ta fad'a fuskarta da murmushi zuciyarta ba ki kirin kamar ya yi bindiga.

Aiko da shagwaba Zalaykha ta turo baki ga ba idanunta na tara ruwan hawaye wai akan mi Mami za ta ce tabar Abba ya huta bacin ta san yadda ta yi missing nasa da yawa.

Take kuwa Abba ya rik'e wa ya fara lallashin ta yana fad'in "yi shiru babynah,rabu da Mami yau tunda ta saman ke kuka sai na yi maganinta!! maza share hawayen ki"

Haka nan Abba ya samu da 'kyar Zulaykha ta yadda ta yi shurun kamin ya kallo inda Mami take da niyyar sauke mata bala'i amma kuma sai dai wayam bai ga komai kama da ita ba a wurin sai ma'aikatan suna cikin gidan da ke ta faman kai kawo saboda hada- hadar girkin dare.

K'wafa ya yi kamar wanda aka masa wani babban laifi kamin ya kama hannun Zulaykha har d'akin ta ya kai ta ya kuma tabbatar da cewa ta shiga wankan da ta ce masa za ta yi kamin ya wuce zuwa tasa turakar da ya tadda Mami ta cika ta yi fam kamar filowar da aka sama yis saboda haushin da su Abba suka ba ta yau d'in nan daga shi har yar tasa.

Harara Abba ya watsa mata ya ce "Allah idan ba ki kiyayi ba ta ma Mamana rai ba a cikin gidan za a jimu da ke _AISHATU_ dan kawai yarinya ta ma mahaifinta oyoyo sai ki bi ki wani nuna cewa kamar ba daidai ta yi ba? Kin fa san hali na akan Zulaykha Allah zan iya 'batawa da koma wane ne! Dan haka sai ki kiyaye ni na fad'a maki"

Abba ya yi maganar bakinsa har kumfa yake yi saboda masifar da ke cin shi wai an ta'ba masa 'yar lele! Hmm wani irin takaici ne ya lullube Mami ita ma cike da hasala ta ce "ai da ma dole ka ce haka Alhaji,idan ba haka ba kawai dan na yi magana na ce ta bar ka ka huta ka ci abinci idan ya so sai ku yi zaman naku shi ne na yi laifi ita kuma har da 'bare baki kuma a ce ba zan yi magana ba??? Akan ka aka fara haihuwa ne da ma duk wanda ka ga dama rashin mutunci akan yarka? Ko aka ce maka ni d'in ma ban san zafin haihuwar ba ne da kake k'ok'arin gaya mini magana?? Idan ka san haka nan za kana mini akan 'yarka mai zai hana ka sauwak'e mini na tafi inda za a yi maraba da ni ba wai a wulak'anta ni ba?"

Mamy ta karashe maganar cike da tsantsar masifar da ke cinta tintini dangane da Zulayka tare da mahaifinta. Abba kuwa kalamanta sun yi tasiri a zuciyarsa, amma kuma soyayyar da yake ma 'yar tasa ba zai sa ya iya goyon bayan wani ya bar nata ba ko da kuwa a ce ita ce mai laifi,dan haka sai kawai ya buga tsakin sa ya wuce ainahin bedroom nasa da ke mak'waftaka da na Mami.

*vote*
*comment*
*share*
  
*OUM Mumtaz ✍️*

RIJIYA TA BA DA RUWA???? Where stories live. Discover now