*RIJIYA TA BA DA RUWA**charpter 6*
********Janye idanunta da suka fara tara ruwan hawaye ta yi daga kallon pic na Zulaym da ke tare da wannan yarinya da a kullum,kuma a koda yaushe,take ganin su tare ta yi,tana mai jin yadda zuciyarta keta faman kai kawo.
Flat ta kwantar da kanta bisa ga table d'in da ke gaban ta bacin ta ture kwamutsan kai a gefe guda,wasu irin zafafan hawaye ne suka safkowa daga cikin idanunta saboda wahalalliyar soyayyar mutumin da bai san zaman ta a fad'in duniya ba ya cika mata zuciya kamar wacce ba za ta kai labari ba.
Sosai take kuka k'asa-k'asa saboda jin yadda zuciyarta ke mata zafi dangane da ganin yadda duniyar Zulaym ke cike da soyayyar wannan yarinya da ko sunan ta ba ta sani ba,kishin wannan yarinya ya samu mahalli mafi girma cikin zuciyarta k'warai da gaske! Amma kuma sai dai soyayyar yarinyar da ke dank'are cikin zuciyarta tun a kallon farko da ta yi mata a photo bai gushe ba.
Sai da ta yi kuka ta gaji dan kanta kamin ta tsagaita tana mai jin tsananin ciwon kai na rufe ta,da k'yar ta samu damar gabatar da sallar azahar a wannan ranar saboda yadda kan ta ke masifaffen yi mata ciwo kamar ya rabe gida biyu dalilin kukan da ta yi.
Ga shi kuma babu wanda ya san halin da take ciki ballantana a kawo mata agajin gaggawa,ji da ta yi numfashin ta na k'ok'arin barin jikin ta ne ya sa ta danna k'ararrawa dake gefen ta da zai isar na sako na neman gaggawa zuwa ga office na P A da ke mak'waftaka da office d'in nata.
Sai kuma akaci rashin sa'a a lokacin,domin kuwa Musty bai nan,ya tafi cin abinci na lunch cikin restaurant da ke ma'aikatar,wanda hakan ya sa tun tana fahimtar inda take,har ta kai ta daina fahimtar komai saboda yadda zuciyarta ke faman ciwo kamar ranta zai fita,da kad'an-kad'an numfashin ta ya fara barin jikin ta har ma ya zamana komai ya k'are babu Zulaykha babu dalilin ta.
********Sunkuyar da kan sa ya yi a gaban mahaifin nasa da ke kallon dan nasa cike da tsantsar so da kuma kauna,fuskar dattijon kuma cike take da murmushi na zallar farin ciki kamar me?
"Ban fa ji abin da ka ce ba *Yaya*,ko za ka sake maimaita mani?"*Babi* ya fad'a yana mai kafe dan nasa da ke ta faman sussunne kai kamar wani tsohon Bafilatani saboda kunyar sa,duk da kasancewar sa d'a namiji, gimtse dariyar da ke neman zuwar masa Babi ya yi ya ce "Kai nake sauraro fa Yaya?"
Sumar kansa da ke kwance lup-lup Yaya ya tusa hannun sa yana susawa had'i da hargitsa su,suna koma wa su sake kwanciya kamar ba a lokacin yake hargitsa su ba,kamar ya nitse cikin kasa,yau shi kam *HUSNA* ba k'aramin sashi a uku ta yi ba wallahi,da ya san haka ne da bai kawo kansa wajen Babi ba yau d'in nan sai idan ya shirya.
"So tunda da ma zuwa ka yi ka sa ni a gaba kana man susar kai kamar sabon kamu ka iya tashi ka yi tafiyarka ni ma ina da abinyi ko?" Babi ya fad'a a lokacin da yake k'ok'arin mik'ewa.
Cike da marairaicewa ingarman matashin da zai kai kimanin 34yrs a duniya ya rik'o k'afar mahaifin nasa,yana kwabe fuska kamar ya fashe cike da kasalalliyar muryarsa mai dad'in sauraro ya ce "Babi ka tsaya mana waii!"Dawowa ya yi kuwa ya zauna had'i da fad'in "na ba ka mintu biyu ka yi magana da wuri saboda ina da wurin zuwa."
"Babi dama..dama...dam..." Katse shi Babi ya yi da sauri ya ce "Da ma me Yaya?"
"Husna ce ta ce wai in ce maka a yi a mana aure." Maganar ta fito a fusge ba tare da ya shirya ba, wanda yana gama fada da sassarfar sa kuwa ya ida ficewa daga d'akin mahaifin nasa bacin ya dire batun sa saboda masifaffen kunyar da ta kama sa."Ja'irin yaro!! Wannan kunya haka na rasa daga inda ka samo shi wallahi,a ce mutum sai kunyar tsiya kamar Fulanin farko?" Babi ke maganar yana mai sakin dariya saboda abin da Yaya ya gama fad'a masa a yanzu,wanda kuma ya jima yana mararin jiran wannan ranar dama.
Fitowarsa a d'akin ne kamar wanda aka hankado sa suka ci karo da *HUSNA* da duk abin da aka fad'a karaf a kan kunnen ta. Wani irin rikitaccen kallo ta jefa masa hawaye na taruwa cikin idanunta saboda jin irin sharrin da yaya ya mata wurin Babi.
Waigawa gefe da gefe ya yi,ya tabbatar babu mai kallonsu cikin gidan,bai bari ta yi maganar da ke k'ok'arin fitowa cikin bakin ta ba,ya toshe mata baki had'i da janyo hannunta suka fad'a d'akin sa da ke madaidaicin cikin gidan nasu saboda ganin ana k'ok'arin bud'e labulen d'akin *AMMA*.
Ai kuwa suna idasa shigewa cikin d'akin kamin ya ce wani ta fashe masa da wani irin kuka,da mutum na gani zai gano na tsantsar jin haushi ne mai tafe da zazzafar soyayya take masa. Marairaice fuska ya yi sosai had'i da rik'o dukkannin hannayen ta,yana lalumo cikin idanunta amma ta k'i yarda su hada ido. Saboda kukan da take masa,wanda mutum ko kana cikin d'akin ba za ka fahimci cewa kuka take yi ba,sai shi d'in da ake yi dominsa.
********A haka nan sukaci gaba da rayuwar su dadi da babu dad'i,wanda kuma a wannan lokacin ne Alina ta sake fito da mugun halinta na kwad'ayi da son abin duniya,duk abin da Wali ya kawo mata da sunan ya birge ta sai ta kushe abin da sunan sam bai birge ta ba,saboda ita ai ba haka nan ta saba gani ana kawa ma wasu k'awayen ta ba,ga shi kuma a wannan lokacin kamar abin sihiri sam babu riba mai kyau dangane da shagon war kasuwancin sa.
Wali yana sayar da takalma da ke cikin kasuwa ta Sunday market da ya gada daga wurin mahaifinsa.A wannan lokacin ne kuma Maman Wali ta fara fama da matsala ta ciwon koda,an je asibiti an mata duk wasu abin da ya kamata saboda yadda abin ya girmama har ana k'ok'arin yi mata dacen ko da,kuma kodar Wali guda d'aya za a saka mata,sai dai kuma matsalar da suke ciki na rashin kud'in aikin ne ke masifar daga masu hankali,wanda sai an saka ranar da za a yi aikin sai kuma matsalar rashin kud'i ya sako su a gaba a sake dagewa.
Inda ta kai ta kawo sai da Wali ya ciyo ma kansa zunzurutun kud'i na ba shi da za a yi ma mahaifiyarsa aiki da shi,da shike Allah bai yi kan za a yi wannan aikin ba,shi da Iyami(mmn Alina) sun yanke kan washe gari zai je ya yi payment na kud'in cikin dare Allah Ya anshi ran mahaifiyar tasa.
Hankalin su Iyami a lokacin ba k'aramin tashi ya yi ba k'warai da gaske! Ba ma kamar Wali da ya zama marayan Allah gaba da baya,babu uwa babu uba,gashi kuma babu dangi! Wayan da suka rage masa a yanzu da zai iya buga kirji ya kira a mazaunin nasa matar sa ne da kuma Iyami.
A wannan ga'bar kam sosai Alina ta tausaya ma mijin nata,wanda ita ce ke kwantar masa da hankali idan hadi da tausar zuciyar sa,wanda kuma dama tun can fa tana son mijinta,kawai kwad'ayin abin duniya ne ke rud'arta tana yi masa iya shege son ranta.
An kai Mamansa gidan ta na gaskiya,inda aka yi zaman makoki na tsawon kwanaki bakwai kowa ya watse. Wanda a lokacin ne kuma abubuwa ke sake dame ma Wali ta fannin tattalin arzik'insa suna sake komawa baya,wanda hakan ya sa shi fara raba takardunsa wajen neman aikin gomnati ko Allah zai sa ya dace ta wannan fannin.
Shi ne ke kula da ci da sha na iyami tare da matar sa,da bayan mutuwan ta sake fito da sabon salon ta kullum cikin shuka masa rashin mutunci take,shi kuma bawan Allah ban da hak'uri babu abin da yake bata,saboda gani yake kamar rashin arzikin nasa laifin sa ne,ba Allah ba ne ya so ya gan sa a hakan. A halin yanxu shekara biyar kenan da auren nasu amma ko 'batan wata ba ta ta'ba yi ba.
Wannan kenan!
Ajiyar zuciya mai karfi ya sauke bacin ya gama tunanin asalin su daga shi har matar tasa,wanda shi bai san ta inda Alina ta d'auko wannan halin nata ba kwata-kwata.
Tsakin da ya ji k'asa-k'asa ne ya sashi kallo kyakkyawar fuskarta da sauri,zaune ya gan ta akan gadon nasu tana ta faman yatsina fuska alamun yunwa ce ke kwakular ta,amma tsabagen taurin kai irin nata ita ta rantse yau ba za ta ci tuwon dawa ba,in ba shinkafa da miya ba.
*vote*
*comment*
*share*
*OUM MUMTAZ✍🏿*
YOU ARE READING
RIJIYA TA BA DA RUWA????
ActionChakwakiya ne Wannan labarin kawai ku bibiye alk'alamina.