Part 26

72 10 0
                                    


*RIJIYA TA BA DA RUWA...?*

*©️OUM_MUMTAZ* 

_WANNAN LITTAFIN TIN DAGA FARKON SA HAR K'ARSHEN SA NA SADAUKAR DASHI GA ~MSS FLOWER🌸🌸~ MARUBUCIYAR:_
~LAFAZI~
~AR SO~
~SARKI~
~GUMBAR DUT'SE~
_SON SO FISABILILLAH❣️💃🥰❣️❣️_                             
   
           *Charter 26*

******** Ai kuwa sosai mutunci mai kyawun gaske ya wanzu t'sakanin KAUSAR (AMMIH) da HALIMATU (ALINA) kwarai da gaske,ga kuma yadda gaba d'aya ma YAYA ya tattare kayan sa zuwa gidan Uncle d'in nasa sabida yadda jinin su ya masifar had'uwa! A kuma dai-dai wannan lokacin ne Allah yayi na UMMA rasuwa,mutuwar data girgiza family na YUSUF SHUWA ba kad'an ba,sbd rashin mahaifiya,wanda ita kanta Alina ma mutuwar ta kusan zautar da ita.

Tin daga lokacin da UMMA ta rasu sai ya zamana YAYA babba shine bangon su,wanda dik wani abinda zasu zartas t'sakanin su shine mai cewa eh ko ah ah a mat'sayin sa na magajin uba! Kuma suma sosai suke girmama shi tinda dama a haife ma zai iya haifar tasu.

AMMIH kuwa ta maida AMMAH(Halimatul Alina) mat'sayin kanwar ta,kuma abokiyar shawarar ta akan abubuwa na yau da gobe! Shekara na zagayo wa AMMAH ta haifi d'iyar ta mace mai kyan gaske son kowa k'in wanda ya rasa,wanda tin ranar da aka haife ta YAYA yabi ya kanainaye ta ya hana kowa ya d'auke ta in ba shi ba! Ranar suna na zagayo wa aka rad'a ma yarinya suna ASMA'U (HUSNAH) mai sunan MARIGAYIYA UMMA kenan!

Wanda dik wani d'awainiyar Husnah na wajen Yaya ne,sam
-sam bai son abinda zai tab'a ta tin tana k'ank'anuwarta!
Kowa kuwa son ta yake cikin dangin baji ba gani! A lokacin da ta kai 2yrs ne AMMIH ta haifo d'iya mace bayan t'sawon lokaci,wacce taci sunan HAJJA suna k'iran ta da MIMA!
Bayan wani 2yrs d'in ta sake haifar d'iya mace mai sunan mahaifiyarta HIDAYA!
Wani 2yrs d'in na zagayo wa cikin month guda suka haifu tare da Ammah! Wanda a wannan lokacin suka haifo yara maza dikkan su,AMMAH ta sama
WAALI takwara ne,wato ABDULWAALI,amma suna k'iran sa da WALEED! Inda yaron AMMIH kuma sunan sa AHMAD wato HAMAD!! Daga kansu kuma basu sake haihuwa ba wanda suka zamtoh sune y'an auta! Watoh fa akace jini ba wasa bane muddin ya shata layi,domin kuwa wani irin masifaffen kamar WAALI WALEED ya d'auko kamar shine mahaifin sa! Wanda hakan yasa a kullum idan Alina ta kalli fuskar Waleed d'in takan tuno da Waali da kuma d'iyarta,takan kuma yi addu'a da fatan Allah ya k'addara saduwar su kamin ta Allah ta kasance mata ta naimi yafiyarsu!
Takan k'ira Waleed da yayana kuma magajin ubana a lokuta da dama da su kuma basu san ma'anar haka d'in ba!!!

Wanda kuma a lokacin ne akayi auren KHADEEJA autar YAYA da suka kasance sa'anni da yaya domin kuwa shekara guda ta basa kwata kwata!!! wanda itama harda guzirin yaron ta guda watoh NURAAZ.

HUSNAH kuwa tin tana k'aramar ta tana da problem na jinnu,sannan kuma tana da skiller da yasa kwata kwata bata son sanyi ko kad'an,sai kuma abin ya had'u mata guda biyu dake matik'ar bata wahala!
Shekaru na jaa,lokuta na tafiya,wanda abubuwa da dama sun faru cikin wannan shekarun masu dad'i,da kuma akasin haka! Batare da doguwar jinya ba shekaru uku da suka gabata Allah yayi ma HIMU rasuwa,wanda mutuwar tasa ta kusan zautar da Alina tare da yaran ta harma da sauran dangi!!!

Sannan kuma sanadiyyar hakan ne YAYA ya had'e aure t'sakanin BABI DA AMMAH sbd gujema yaran k'anin nasu rayuwar agolanci a dik lokacin da suka wayi gari mahaifiyar su tayi auren wani gidan!! Wanda saida YAYA yakai ruwa rana da AMMIH kamin ta saduda,amma kuma ta rik'e su a zuciya,sabida gani take kamar bai k'aunar ta kamar baya shiysa yayi mata kishiya da girman ta da kuma wacce tasan komai na sirrikan ta! A tak'aice dai kishi ne kawai ke azalzalarta,wanda hakan har ya kusan shafar dangantakar dake t'sakanin yaranta da kuma su HUSNAH d'in,domin kuwa wani irin rikitaccen rashin kunya suke zabga ma ALINA da HUSNAH,su kuma hantari Waleed idan babu idon Yayaaa ko Babi a gidan.

Girman Yayaaa da HUSNAH shak'uwar dake t'sakanin su ne ta rikid'e izuwa zazzafar soyayya da babu algus! Sosai yake masifar sonta tin tana k'ank'anuwarta,da kuma ta girma sai abin ya girmama fiye ma da baya! Cikin wannan lokutan UNCLE J ya kammala karatun nasa,sannan kuma ya naimi aiki acan kuma sun basa tare da albashi mai t'soka,ya kuma yi aure tare da wata abokiyar karatun ta mai suna RUSHNI da ta kasance cikakkiyar ba indiya ce gaba da baya,amma kuma musulma ce!

Wanda auren nasu ma saida aka kai ruwa rana kamin both family nasu suka amince sabida rashin dai dai tuwar al'adar dake t'sakanin su,wanda a halin yanxu ma suna da yaron su namiji guda,wanda daga kansa basu sake wata haihuwar ba,hakan kuwa dik cikin nasu t'sarin ne!

Sannan kuma mijin Anty Khadee Allah yayi masa rasuwa ya barta da yara guda biyu Nuraaz da Aymana,wanda shine har Dad na Jidda yayi mata tayin auren aminin sa WAALI.

Ga kuma HUSNAH da Yayaaa k'ark'ashin inuwar aure guda mat'sayin mata da miji da ya kasance shine mafarkin su. Ga kuma mat'salar su dake t'sakanin su sabili da rashin son haihuwa da Yayaaa keyi!

Shin ko yaya zasu kasance?? Shin burin ZULAYKHA (UMMI) zai cika na auren ZULAYM AHMAD SHUWA dake mat'sayin mijin k'anwarta da suka kasance uwa d'aya,wanda kallo guda tayi masa cikin photo yayi nasarar sace zuciyarta dik da tarin masoyan da take dashi ciki harda d'an gidan Yaya wato UNCLE J...? Ya kuma had'uwar Alina da kuma Waali zai kasance bayan t'sawon shekaru 24 da suka d'auka basu tare da junan su...? Ina kuma labarin soyayyar da Musty kema Ummi? Shin mahaifiyar sa zata bari burin sa ya cika ko kuwa zata hana shi kamar yadda ta saba fad'a masa...? Waima shin ina su dangin mahaifin Musty ne? Kuna gani kuwa akoi uban da zai so ya aura ma y'arsa yaron da aka same shi ta hanyar da babu aure sannan kuma bashi da dangi...?
Tambayoyin akoi kaca kaca,wanda kuma nasan zaku so ku sami amsar tambayoyin ku! wanda idan kuwa kuna son hakan sai kun fara k'arfafa man gwiwa ta hanyar zuba sharhi zaku ci gaba da samun post akai akai kamar yadda kuka ga nakeyi akan Book d'innan.

_So masu karatu da fatan kun fahimci cikakken labarin wannan ahali guda biyu? daga yanxu zamu fad'a cikin labarin gadan gadan insha Allah🌸🌸🌸🌸🌸_

…… ……

K'ura ma fuskar Waleed Abbah yayi na cikin hoton a lokacin da ya karb'e wayar daga hannun ta sabida ta shanye shayin cikin lokaci k'ank'ani,ganin yadda mood na Abbahn nata ya chanza lokaci guda ne yasa ta mat'sowa had'i da kwantar da kanta a jikin sa,cikin muryar k'asa k'asa tace " Abba na kaima kaga yadda wannan yaron yake kama da kai ko??"

Cikin d'an muryar sa da ta fara shak'ewa Abbah yace "wannan d'an gidan wanene a ina kika samo shi?" da shike Ummi bata san komai dangane da gidan su Yaya d'in ba,saita masa bayani iya sanin ta "Kaga wannan kyakkyawan matan? itace maman way'annan dikkan su,kuma akoi ma wani yayan su da yayi aure kwanaki shima d'an ta ne,wanda har kuka je d'aurin auren!!" cikin son gaskata kalaman ta Abbah yace "kin tabbata Mamana?" "kwarai ma kuwa Abba na!" Ta kuma tabbatar masa da hakan iya gaskiyarta,domin kuwa dik tunanin ta Ammah d'in da suke ta faman ambata itama y'ar Ammih ce.

... ...

Washe gari da safe,tare da Abbah Zuly suka fita wurin aiki kamar ko yaushe!! Inda Musty ma ya wuce wajen nasa aikin dake kan kujerar Ummi d'in a halin yanzu.

Acan gida kuwa bayan fitar su Abbah abinda ya faru shine.........✍🏽

*vote*
*comment*
*share*
  
*OUM MUMTAZ✍🏿*

RIJIYA TA BA DA RUWA???? Where stories live. Discover now