🥬🥬🥬🥬Wata miyar🥬🥬🥬🥬

149 10 2
                                    

Sadiya Rimi:
🥬🥬🥬🥬 WATA MIYAR...🥬🥬🥬🥬

            Na

SADIYA MUSA RIMI

           🥬6🥬
 
🥬🥬 ASALIN AL'AMARIN🥬🥬

Gwani Maina Bukur Kacalla, Malami kuma masarauci har ila yau dan kasuwa fitaccene a garin na Maiduguri da kewayenta, Gwani Maina nagartaccen mutum ne mai nagarta da tarin yalwar ilimi na addini dana zamani, domin shi din ya gogu da ilimi ne a wajan mahaifinsa da yake a tarin ilimi da lakaninnika kala kala, mutum ne mai zafin yawa da ko kadan bai daukar raini, kuma shugaban matasa dake rike da sarautar kacalla.

Kasuwanci ko ya koyeshi ne a hannun kakarshi Hajiya Falmata mahaifinyar gyatumarshi kaltum, duk da mahaifinshi Bukur kacalla yake dan kasuwa mai rufin asiri da tarin yara ashirin da biyar. Gwani Maina daya taso sai yace ma mahaifinshi matsa bani waje a komai. Dan ko shi din ido ne daya budi da horo mai tarin yawa na bangarori da dama, kyara da tsangwama daga wajen 'yan uwanshi da suke uba daya musamman a bayan idon mahaifinshi kasancewar sa shi kadai kwal a gaban gyatumarshi kaltoom da ta Zamo saniyar ware a wajen kafatanin matan gidan a dalilin dinbin kaunarta da Bukur kacalla bai iya hadiyewa ko a gaban waye,wanda suka dauki hakan a matsayin wani cin fuska ko cin kashi da shi din ke musu duk da adalcin daya kanyi kokarin kwatantawa a tsakaninsu.
     Shi din yakanji tausayin kaltoom dinne ganin ya daukota kankanuwar yarinya ya hadeta da matansa da suka zamo iyaye a wajanta ta bangaran shekaru sai itan kuma ta kasance mai tsananin hakuri, juriya da kauda kai ga al'amuran gidansa, ta sanya rigar kyautata mai da son dukkanin wani abu da yake so.
Sannan auranta yazo masa da wani irin budi mai tarin yawa ta kowanne fanni, yana kasuwanci amma kasuwancinsa baiyi karfi ba sai bayan auransa da kaltoom, kasancewar ta futo daga gida na kasuwanci da yafi karfi sama da malanta, sai surukutarshi da gidan ta sanya suka rika buda mishi hanyoyi kala kala da kasuwancinsa zai bunkasa musamman a lokacin zuwan turawan mulkin mallaka daya kasance gidansu shine gida da yayi karfi a wajan huddar kasuwanci dasu.
     Kuma kaltoom da kaninta mudan su kadai ne 'ya'ya ga mai malam gwani, mahaifinsu, haihuwar Maina sai ta zame musu tamkar wani tsani na tashi da burin kasa a idon duniya.
      Kacokan gidajan biyu suka dauki soyayyar duniya suka dorawa Maina,sai dai hakan bai sa an bashi soyayya irin ta zamani da za'a sakarma da ragamar rayuwa ta duka abinda yayi dai dai ne ba, a maimakon haka se aka horar dashi da ilimimmika da lakane lakane daya gada na gidajannan guda biyu.
      Fara tasowarsa da yadda ya faso kuma lokaci guda sai ya fidda wata magana da ta fara tashi da kadan kadan daga nan gidan Bukur kacalla har ta watsu a gari, cewa Dukiyar gidan mai mala gwani alkawarine na wata aljanna da take wadatasu da ita take dafa Dukkanin wani abu na saidawa da suka sanya a gaba, shi yasa shima malam Bukur daya auri diyarsu sai al'amuran sukayi ta buda masa.
   
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬

To magana ance idan kayita a waje daya takanyi yado ta watsa kanta har wasu guraren sujita, karshe kuma ta kanyi kafa tayi fiffike har ta kai kanta ga wanda akayi maganar domin shi, cikin hakan zancan yaje har kunnan da duka duka ma yaushe ya fara kasuwancin amma har ace ya taso baki daya haka.
         Dariyar manya yayi ya dubi mai bashi labarin yace " komai zaka yi gwani yahuza mutane suna da abinda zasuce a kanka, shi ya sanya komai zaka yi to kayi kokari kayi shi domin Allah kuma ka barshi domin sa. Ni na sani kai ka sani Maina dan baiwa ne, ko ni ban hada ilimi a irin dai dai shekarun da Maina ya haɗa ba, Maina Allah na saukaka mai duk wani abu da ya sanya a gaban shi, kuma banga samun da yakeyi na ban mamaki da har ya haurema kashe kashen kasuwancin da yakeyi ba.
     To rayuwa na tafiya al'amura na zuwa suna wucewa har Allah ya nufi kulluwar aure a tsakanin Maina da Falmata.

Karamar diyar muda kanin kaltoom, cikin hukuncin Allah sai dukiya ta sake bubbukowa kamar mai yasa da bakin katafila, haihuwa ce shiru Allah bai kawo ba har zuwa kulluwar aure a tsakanin shi da zara, a lokacin auranshi da Falmata karama shekaru biyar cif, shekarar zara uku ya auri yagana, ita kan tsiransu ko shekara bai rufa ba a tsakanin auranta da yana.

🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬

Taku akoda yaushe
SADIYA MUSA RIMI

Muje zuwa 📝📝📝

Muna godiya ga dukkan addu'oinku, Allah ya saka da mafificin Alkhairi, ya gafartawa dukkan wa'yanda suka rigayemu gidansu na gaskiya ya kyautata makwancin.
AMIN THUMMA AMIN
BISSALAM

🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬

wata miyarWhere stories live. Discover now