🥬🥬🥬🥬🥬🥬

94 12 0
                                    

☘️☘️☘️☘️☘️
*WATA MIYAR*
         ☘️☘️☘️☘️☘️

𝗪𝗿𝗶𝘁𝗶𝗻𝗴
            𝘉𝘺
𝑺𝒂𝒅𝒊𝒚𝒂 𝑴𝒖𝒔𝒂 𝑹𝒊𝒎𝒊

*PERFECT WRITER'S*
*ASSOCIATION*🌞

(𝕎𝔼 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 𝔹𝕌𝕋 𝕎𝔼'ℝ𝔼 𝔸𝕃𝕎𝔸𝕐𝕊, 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 𝕆𝕌ℝ 𝔹𝔼𝕊𝕋 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍
__________________________________
🥬🥬🥬wata miyar...🥬🥬
    🥬🥬🥬10🥬🥬🥬
🥬🥬kuskure da qaddara🥬🥬🥬
Dariya kawai dady yayi,mamakin mugun halin Fannan fal a cikin zuciyarsa da rashin kunyarta,me zataji Dan ta cutar da qaramar yarinya Kamar Maryama?.
     " Wuce ciki wajan maminki ki zauna babyn Aliyun! Ina Nan Zan sake ganin Mai taba min ke a cikin fadin duniyar Nan,duk ta in da mutum ya bullo Ina nan Ina jiransa nima.
    Malam Manu ya matsa kusa da Dadi bayan Maryama ta garzaya gida da saurinta tana tsalle tsallenta;a hankali ya risinar da kanshi a gaban Dadi din yace.
     "Alhaji da wani shishshigi nakeson nayi ma,me zai Hana a tura yarinyar Nan can wajan su Malam Liman su gyara Mata jikinta maimakon a barta a hakan sakaka shi mugu da kake gani yasan duk ta hanyar da zai cutar da Kai,idan ka ganeshi ta nan ne a fannin cuta shi kuma sai ya koma ta wani gefen Yana jifan ka irin jifan da ba zaka iya ganewa ba,shiyasama bahaushe yace idan kasan halin mutum maganin Zama dashi kakeci.
      Ni Ina ganin barinta hakan ba tare da daukan wani mataki ba ba dabara bace,bayan kisan fili Alhaji akwai kisan mummuqe a wajan mugu,shi kuma.kaga ai dukan cikine ba kowa ke fahimtarsa a.
   Dadi yayi dariyar manya a hankali yace.
    "Kada ka damu Manu,duk masu irin wannan halin barinsu da akeyi ba'ayi musu magana shike sawa suci gaba dayi,Amma itan data San idan ta shiga gonar kan ta Kai kunyar tsakiya an ganeta ta barta kenan ba zata sake waiwayanta ba.
    To hakan dai aka tafi !sannu sannu rayuwa ta tura,babu wani lamari daya sake faruwa da Maryaman,karatunta Yana ta miqewa yayinda shaquwa Mai yawa take dada Shiga tsakaninta da Mami da kuma Innarta da qanwarta d Innarta ta sake Haifa idan taje gidansu Mai suna Jidda.
   Maryaman nada farin jinin jama'a sabida kyanta surutunta da kuma kazar kazar dinta,dangin Mami kaf dake zuwa gidan babu wani Wanda ya sake magana ko tari akan zaman Maryaman agida ,yayin Bamanga ya dauki son duniya ya Dora àkan Maryaman.
    🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
Tana j s 3 Aliyu ya Dawo gidan bayan ya Zama cikakken kuma qwararran likita,tun bayan barinsa qasar ko a waya baya magana da Maryama Wanda shi din bai taba neman a hadashi da ita ba kuma Suma iyayan babu Wanda ya taba yunqurin hadasu.
   🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
Shiri sosai Mami keyi Dan dawowar Aliyun gida bayan shekaru shida da ya kwashe a qasara ta ingila,ta hana kowa sakat a cikin rayuwarsa a kafatanin mutanan gidan, maryama.data soma budewa Mai shekaru Sha hudu ga tsayi wani irin sanyayyan kyau da tayi sai bin Mamin take da kallo kawai tana murmushi, tayi waya maiduguri duk wani abokin arziqi yasan da zuwan Haidar din gidan a safiyar ta washe gari.
    Yammacin ranar maryama.da malan Manu suka Isa nan udb Dan amso alkaki da dubulan da Inna tayi na tarar Aliyun baki dayan ahalin gidan ta samu sun kacame da Shirin tafiya Roma daurin auren diyar baba Ali da za'a yishi jibi,Maryaman ta tsaya cike da Doki tana duban Innarsu data futo da kayanta Nan tsakiar gida wajan da ake shirya Kaya,mutum biyune zasuyi tafiyar it's  da kanta sai Lantana ne zasu a gidan sai kuma yayin Maryaman fa'iza maimu da kuma dija.
   Nima Zan biku Innarmu Kinga na dade banje Roma ba,Dan Allah ki barni na biku kinji.
   Innar ta dubeta a hankali da sanyi ta tace
"Ko ance za'aje dake dadinki ba Bari zaiyi ba,musamman da ya San Haidar na dawowa a gobe dan haka ki Bari idan ya dawo jibi sai kibi Malam ya tafi dake wajan daurin auren ko?.
   Maryaman ta zunbura baki a hankali tace "Dadi baya nan Innarmu yaje taho da Yaya Haidar din Dan Allah Ni dai ki barni na biku nasan idan naje na fadawa Mami ba zata Hana niba kinji,Lantana data shigo tana Jin qarashen maganar ta dubi Innarsu Maryaman ta tabe baki tace.
    "Ni ban taba ganin a wajan da samun guri yasa kake ture Dan daka Haifa da gano dangin kaba sai a kanki Dija,yarinyar nan yaushe rabanta da zuwa Roma sabida Allah da annabi uhim! Duk zuwa sai ta nuna tana San taje Amma sai kiyi fici fici ki hanata bayan kuma kina da uwa da uba a Raye ai kodansu Kya Kai yarinyar Nan ta gano su suma.suma su ganta ko.
   Inna Dija da magana kan Mata wahala tayi murmushi tace "ba hakan bane Yaya,idan ana janyota Nan din sai dadin Nasu yaga kamar munason amsheta me balle a irin wannan lokacin da  suke ganin yaransu zai dawo gida bayan tsawan lokacin daya dauka bayanan ya Kamata ta zauna ya dawo inyaso in Malam ya tashi tafiya jibi sai ta bishi su tafi tare.
   Iye! Idan kuma yaran da kike mararin ta zauna sabida shi din kuma ya Zama ya manta da rayuwarta fa,shekararshi nawa da tafiya yabar qasar ca nake har Nan yake kiran ki a salula ki gaisa da Malam kuma wani lokacin yarinyar nan tana gidan nan yake Kira Amma sau guda na tabajin yace Ina Maryama take ku bani ita mu gaisa?ke ko Yana cewa baki waya ki gaisa dashi idan ya Kira gidan naku? Ta juya tambayi Maryaman tana neman qarin bayani,da sauri Maryaman ta girgiza kai cike da quruciya tace bai taba cewa a bani ba Inna babba,to wuce kije ki hado kayanki ki fadawa uwarsa gida zakije wajan bikin 'yan uwanki idan da gaske Dan nasu ya damu dake ai shekara shida ba kwana shida bace da zai kasa Neman ki kema ki nuna Masa yadda bai damu Dake ba kema qurar data debo shima baki damu da ita ba balle shi.
    A gurguje ta Shiga cikin falon tana gaba riqe da wani babban bokitin roba dake rinjayarta Manu na riqe da waSu guda biyu duk na tarar Aliyun ne da Inna tayisu.
    "Mami zanbi su Innarmu wajan bikin yaran baba Ali kinji"Maryaman ta fada cike da Doki a cikin muryarta, Mami Dake waya da Fanna àkan dawowar Aliyun ta cire wayar da sauri daga cikin kunnanta tace
   "Rabani da masifar Dadin ku Maryama ba Zaki bisu wajan bikin nan ba ,ki jira Haidar ya dawo tunda ba gobe ake daurin auren ba nasan zai iya zuwa ayi dashi kodan yaje wajan baba Liman inyaso idan yazo sai ku tafi tare.
   Daga cikin wayar Fanna dakejin komai da yake faruwa tace Fadila! Fadila ta ambaci sunan sau uku kafin Mamin ta maida wayar kunnanta bayan taga fitar Maryaman dake zunbura baki daga cikin kicin din.
   "Ki barta ta tabi iyayanta suje ba wajan danginta zasuje ba?"
  Fannan ta tambaya daga cikin wayar, da saurin Mami Dake Jin zuciyarta na fat fat tace can zasuje Amma kinsan Dadi...
    Babu wani Abu da zai faru sai abinda aka dade ana jira,jeki sallemata taje ta gaida ahlinta,ta hada kayanta sosai yadda zasuyi amfani Suma su Yaba da irin ruqon da kukeyi Mata"to Mami ta ambata gami da hutawa ta fita daga cikin kicin din ta haye sama zuwa dakin Maryaman tana qudundune a gado tana. Faman cin uban kuka Kamar tayi Yaya.
   "Haba Mana baby na Ina abin kukan dan nace ki zauna sai Haidar ya dawo duk kike nema ki sanyawa kanki damuwa?ya Isa  maza tashi ki Shiga wanka ki shirya Ni kuma sai na hada Miki kayanki kije ki tafi dogon direba ya kaiku ke dasu din baki daya shikenan kuka ya qare ko?da sauri Maryaman ta tashi ta shiga wanka da tayishi a gurguje ta futo ta tadda Mamin ta hada Mata kaya maqil a cikin qatuwar jaka hadda safaya ta kayan kwalliya ta debo kudi a dakinta damqam ta Danna Mata a cikin jakar duk Maryaman na dubanta bayan ta gama ta dubi Maryaman da murmushi a fuskarta tace to babyn Mami Kaya ya hadu ko,Maryaman baki sake tace "duka wannan kayan Zan tafi dasu can Mami Kamar Zan zauna bayan an gama bikin?"
  Itanma Mamin kayan ta duba Kamar wata sakara ko kuma wadda ba ita ta hada kayan da hannayanta ba tace sunyi yawane baby na? To ai babu Wanda zai karbe Miki Kira Manu ko wani a waje sufitar Miki dashi.sukuku Maryaman da jikinta yai wani irin sanyi ta fita ta Kira Manu ya kwashe Mata kayan harda gudunmawar da Mamin ta bada Suka wuce udb ya kwashe su baki daya suka tafi.
    Innartace kawai ta lura da sanyin da jikinta yayi Amma kuma bata da bakin da zata bude tace wani Abu sabida Lantana.
    Kowa yayi murna da zuwansu musamman Maryaman da rabanta da garin tun tana shekaru takwas da aka kaita da lalurar jinya sai yanzu da ta girma tayi wayo kuma ta Zama budurwa Nan dakin innarta da babansu ya gyara musu wajansu kowacce mace take sauka a wajanta ta tile kayanta magariba ko tana gidan kakaninta na uwa kowa Yana gaba gaba da ita,yayin da Malam inuwa ya zauna duk wani jiqe jiqe da ya ke da burin Bata tun bayan yin jinyarta ya Fara harhadawa Yana Bata.
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
Alqawarin Allah🥬🥬
    Jirgin su Aliyu ya sauka da misalin qarfe takwas na dare Mami da dogon direba sai Nasma sukaje da ta iso ranar daga bauci sukaje taro shi,Dadi ya Fara futowa daga departure sai Aliyu daya Zama wani ingarman namiji jajir dashi da kebantaccen gashin kansa dayasha gyara ga wani saje kwata miliyan daya ajiye gwanin sha'awa Yana sanye cikin wasu lafiyayyun suits army color fatarshi ta kwanta lif tamkar Mai rayuwa a yankin shoredith ta East london idanshi sanye da wani irin glass Mai zagaye da ruwan zaiba agogonshi na sallar azurfa da zobuna uku na zurfa Dake sanye a hannayanshi sai fidda wata irin wuta Mai haske sukeyi, daukacin jama'ar Dake jiran 'yanuwansu a departure din sai binshi suke da kallo kowa Yana inama-inama.
   Qaunar sa dabance a wajan iyalansa,Nan da Nan Mami taji idanta ya cika da wata irin qwalla tamkar zata zubo mata,itanko me zata cewa Allah Banda godiya,cikin daukacin dubban jama'ar Dake cikin airport din Allah ya Zabe Mata Haidar dinta ya dagashi da kyawun sura da haiba da kwarjinin da bai iya boyuwa ko a cikin dubu,Haidar top class man ne one in million.
  Sassanyan qamshinsane ya Fara Shiga cikin hanci ta kafin daga baya Shidin baki daya ya kama Mamin nashi ya rungumeta tsab a qirjinshi Yana shaqar qamshin ta gami da Kiran sunanta da wata irin cool voice da Mamin kadai kan iya jinshi.
   Maminah !ya ambata Yana sake rungume Mamin Dake Jin tamkar ta mayar dashi cikin jikinta.
   "Haidar!ka girma da yawa haka when last muka hadu dakai a Richmond Amma ka sake sauyawa Kamar Wanda ke hadiyar wahainiya?
    Wani irin sanyayyan killer smile ya Mata bayan ya Bata fake a goshinta ya rungumeta wajen side dinshi na dama ya Kai dubanshi ga Nasma da tayi wata irin mutuwar tsaye tana dubanshi yayin da ruwa da numfashinta ya tsaya cak da aiki sai bugun zuciyarta Dake tashi cike da so da qaunar haidar din data hudata a lokaci guda irin Mai tsananin Nan.
    Mami data maida hankalinta wajan da yake kallo tayi murmushi ta kamo hannun Nasman ta hada da nashi ta riqe tace 'baby Nasma kenan,I hope baka manta da ita ba ko?diyar Yaya Fanna ta Bauci, a hankali ya saki wani smile tare da janye hannunshi daya  daskarar da Nasman sabida taushi ya maida hannayanshi kan kafadar Mamin a hankali ya tsareta da idonshi Dake cikin glass alamar tambaya.
   Dadi da isowarshi kenan sabida ya tsaya gaisawa da wasu shima ya rungume Mami dake kallanshi tana murmushi tare da dafa kan Nasma Dake kallanshi tana sunkuyawa da yunqurin gaisheshi ya dagota Yana dariya da tambayarta yaushe tazo garin da kuma Babanta.
     "Baby fa? Ya tambaya Yana duban fuskar Mamin,Mami tayi dariya tace  "babynka tayi tawaye Dadi sabida bikin yaran Aliyu Roma dajin 'yan gidansu zasuje ta maqale ta bisu da farko Dana Hana hadda yimin kuka Kamar zata mutu.
    Dariya Dadi yayi yace "bansan ya baby keji ba ai akan occasion amma inda ta Bari munzo ai muma zamuje da ba gobe sai mu wuce tare da ita ba? Muje son gida ka huta ga kuma yanayin sanyi da garin ke ciki"ya fada Yana kafadar Aliyun.
    Aliyun yaja ya tsaya ba tare da yabi bayan Dadi dinba,Dadi ya juyo ya kalleshi a hankali ya dawo ya riqo hannayanshi duka biyun a cikin nashi mamima dawowa tayi ta dafa kafadarshi cike da alamun tambaya.
    "Meyasa Kika barta ta tafi wani wajan ba tare da ta tsaya nazo ba Mami?" ya tsare Mamin da tambaya
   Dadi yayi dariyar yace "kadaici ke damun baby son,Dan haka duk lokacin da taji wani Abu na occasion jikinta har Bari yake taje kayi haquri gobe Zaku hadu da ita ai Roma taje ba wani wajanba.
    "Kenan zuwa Roma yafi ta tsaya ta ganni Dadi?.
    Ya sake tambaya muryarshi na cracking Kamar zaiyi kuka.
   " Be a man Mana son,kada ka Zama Mai rauni a kan abinda kasan already naka be Kuma ikon Kane said yadda   kayi dashi uhim"babyn kace she is all yours babu wani Abu da zai sameta sai ma mamaki da zakayi na yadda ta qara girma tamkar ba wannan small babyn daka tafi ka Bari ba,dadin ya Kai kunnanshi yayi Mai wata Rada a kunnanshi data Sanya Aliyun yayi hugging nashi Yana dariya lokaci daya tare da daga yatsanshi Dan Ali yace ma dadin promise! Dadin da shima cikin mood din dadin yake ya saqale nasu a hannun yace pinky promise baba oya smile mu wuce ko.
   Mami ta kame haba fara'a fal fuskarta tace " har yanzu Ni ban girma da a ware Ni ana nuna mini bangarancin Nan ba ko shikenan babu laifi".ta fada tare da juyawa tamkar tayi fishi.
    Da sauri Haidar din ya matso ya sake rungumeta Yana Mata magana a hankali cike da qauna ta kama kunnanshi ta girgiza sannan ta lakace Masa hanci ta riqe hannunsa Suka juyo,har su. Fara tafiya ta juyo taga Nasma na tsaye a wajen cike da tashi hankali,hannun Haidar din ta saki Suka wuce da dadinshi ita kuma ta dawo ta daga Nasman da maganganun Bamanga suka sanyata wata irin mutuwar tsaye da sagewar gwiwa tamkar ta mutu.
   Dafa kafadunta tayi ta dago idanuwanta da sukayi wani irin ja cike da hawaye tace "Mami wannan Karan ma broh ba zai kalleni a matsayin mace ba nima har  yanzu xuciyarshi na akan waccan yarinyar da Bata ma damu da rayuwarshi ba,lectures da test duka na saki na zo Dan na tareshi Amma ita a time din Da zai dawo a time din take barin garin amma duk da hakan hankalinshi na kanta wanne irin tsafine wannan sukayimaa da kuka Gaza yin komai a kanshi.
   Mami da hakannan kawai taji wani irin tsoron Nasman ya shigeta ji take Kamar idan bata Bata abinda takeso ba komai zai iya faruwa da zuciyarta ta dafa Nasma da sigar rarrashi race.
     "Kada ki Bari hawayanki ya zuba akan wannan baby,yanzu bada bace'ke din kin girma girman dako  wanne namiji kike so Zaki karbeshi da kyau da Surar da Allah ya Miki balle Haidar da yake Dan uwanki da kike damu garkuwar da zata tayaki yaqin qwatarsa koma a hannun wa yake,Dan haka kada ki Bari wani shirme nashi Kona dadinshi ya dameki,alqawari na ne wannan Haidar nakine kuma ba zai koma ko inaba sai tare dake,Dan haka goge fuskarki kadama su fahimci wani abu yarinya ta tafi danginta kenan har abada ba zata sake dawowa garin Nan ba alqawarina ne wannan.
    Da wannan lallashin ta samu ta jan yota suka taho motoci da sukazo domin daukarshi Dan haka ko mota shi Haidar bai kuma hadawa dasu Mamin ba har Suka futo suka wuto gida.
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
   🥬Zakaran da Allah ya nufa da cara
     Shiri sosai aka tashi dashi na daurin auran yaran na baba Ali maryama tayi Cara's cikin shigarta ta shaddarta gizner saban dinkine daga cikin dinkunan da Dadi yai Mata sabida yima Aliyu kwalliya Kamar yadda yake fada,Tasha lallanta da haliman diyar Yayar Inna tayi Mata ja da fari tayi kyau tamkar itanma amaryace,tun asuba baba Aliyu sukayi waya da Malam na maiduguri da kuma Bamanga lamarin daya Sanya aka daga daurin auren daga qarfe Tara Kamar yadda aka shirya aka maidashi zuwa bayan azahar Wanda su Mata na cikin gida Basu San  dalilin daya Sanya akayi hakan ba balle kuma su 'yan Mata Dake can gidan talatun baba dini suna zaman 'yan matanci domin itace mawankiyar yaran baki daya,yayin Maryama da ladidin baba Suka tafi gidan baba sani yayan mahaifintane da shi ya samu ya fita daga gidansu ya gina gidanshi a gefe guda ,can sukaje kallan dakan ruwan Zuma a matsayinshi na waliyin amaran komai na bikin ya qayatar da Maryaman yake,shine kallanta na farko da yadda ake biki a qauye
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
Shiri sosai akeyi a gidan Alh.bamangan na zuwan su malam,hajiya Fadila tayi mamaki sosai da yace Mata a shirya abinci domin su malam zasuzo wajan daurin auren yaran baba Ali da za'ayi a Roma ta tsaya kawai tana duban Bamangan wani irin,bakiji abinda nace Miki bane a shirya abinci su malam zasu iso a jirgin safe mu wuce wajan daurin auren Nan ko.
     Abinne ai yaban mamaki Dadi meye matsayin mutanan Nan a wajankane haka da ka daukesu da kima da martaba haka da har su malam zasu taso Dan kawai zasu aurar da diyoyinsu,koni banji Zan iya zuwa bikin ba balle a taso mutane daga maiduguri kawai Dan sabida wannan auren.
     Ke kikace,ni kuma Ina da banbanci Dake,shiyasama ai Kinga bance a cewa Malam na bullunkutu yazo ba,sabida nasan kudin Baku da alaqa da hakan,Dan haka maganace guda ta abinci zaki iya a hada musu abinci a wuce dashi quest house ko kuma na nemo musu a wani wajan na Kai musu suci suyi abinda ya kawosu garin su juya nima nazo na wuce na bar garin zuwa yamma Dan Ina da Zama da president a daran yau ko kuwa.
    "Uhim ayi dai mugani idan tusa tana hura wuta Dadi".
    Ta fada tare ta juyawa zata fita daga dakin
   Fadila! Ya Kira sunanta,ta juyo cike da Dan tsoro tana dubanshi.
   "Bar aikin abincinki ko kinyi wallahi ba za'a Kai musu ba kin wahalar da kanki a banza a wofi kuma kinyiwa kanki,banaso da kudina a jikina fa yadda duk nakeso irin hakan Zan sauki mahaifina ba tare da kuma wani Abu ya Bata min rainaba,yau farin ciki nake kuma ranace Mai kima a wajena ke da shirmanki Baku Isa ku Bata min mood din yau ba idan kinso kina iya hadamin kayana ba ta gidan nan Zan dawo ba daga can Abuja Zan wuce Kai tsaye ta airport idan na ajiye su malam son ne kawai zasu dawo gida da sauran ma'aikatan gida.
   🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
Jerin gwanan jama'ar maiduguri da abokanan Dadi na kusa sai abokan Aliyu tun na secondary da wadanda akan hadu tare a London haka Suka cika garin na Roma da yaga baqin 'yan Boko ko ta Ina.Buba bai Sami zuwa daurin auren ba duk yadda yakai da son halatta sabida lissafin  da aka turashi fatakwal na wasu Kaya da Suka Bata.
   Jama'ar Roma sunga gaiyar 'yan Boko yayin da Haidar ya shige cikin gidan dashi da abokanansa har dakin Inna dije dakin da yasha dabdalar quruciyarshi a cikinshi tun kafin haihuwar Maryama,duban innar yake da wata irin jin kunyarta da bai taba tunanin zaiji taba a duniya,Jidda diyar inna dijen qanwar Maryama ya kama ya riqe lokacin da innan keta bigijejen hada musu abinci.
    "Ina Maryama ne bangantaba jidda batasan na shigo Nan din bama"ya tambayeta Kamar zaiyi kuka.
   Jidda din da tafi Maryam Baki ta dubeshi fuka fal fara'a tace.
     " Ba Nan gidan Suka kwana ba suna can gidan kwanan amare sai an jima zasu dawo Nan daga gidan mawankiyar.
  A nitse yace 'kina jina ko,kije maza gidan kice Aliyu yace tazo,pls ta bar kome take a gidan tazo I want to see her madly pls ai nayi haquri idan ba kasheni takeson tayi ba.
    Jiddan ta miqe tana Mai dariya yayin da nabil ke ta faman tsokanarshi a hankali yace.
   "Am serious man iya kacin haqurin da Zan iya kenan na kuma yishi,nayi Imani na samu iya ladan da Zan samu a cikinsa so hakan ya Isa,tazo kawai Ni naganta a idona hakan zai sa na samu relief sosai a zuciyata.
    Salman abokinshi da sukayi zaman shekaru hudu a London yace.
   "Haba man Fadi gaskiyarka kawai kaidai kace.... Suka kwashe da dariya baki daya Banda Aliyun daya jingina kanshi da bango ya lunshe ido xuciyarshi na wata irin bugawa,shi kadai yasan a yadda ya rayu a tsayin shekarun Nan Amma a yanzu ji yake idan babu babyn to komai na iya faruwa
dashi a yau dinnan.
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
Zuwa bayan sallar azahar ana idarwa aka daura auren amarem Baki dayansu yaran baba Aliyu su biyu baba Sani ya daura musu aure bayan an qare kuma baba Aliyu ya zauna da kan shi ya daura auren da jama'ar da Suka taru kawai a wajan sukaji daurin auren Banda su da abin ya shafa kuma Suka shiryawa abin dauri aure Mai daraja da kima da aka biya sadakinshi da silallan gwal na Maryama Buba Roma da Aliyu Bamanga Maina da kakanshi ya amsar mishi daurin auren da kanshi.
Hadin Allah kenan abinda kowa ke Kira kenan.
Maryama matar Aliyu dama tsohon hadin Allah da sudin Suka shaida Suka kuma tabbatar dashi cewar Malam na maiduguri.
    Idan Aliyu ya cika da wani irin hawaye,Maryaman kawai yakesan gani a idanshi.
    Zagayan Jidda hudu gidan mawankiyar Amma Sam babu Maryaman babu alamunta har su Alhaji Bamanga Suka gaji zasu tafi baba Ali yasa Suka zagaya gidan da Aliyun ya gina a Roma baba Aliyu ya bashi filing da gona yayin da ya riqa turowa nabil da komai akayi gini aka gama kowa ya Sanya albarka a gidan gida tamkar baka cikin nigeriya,pent house lafiyayye 'yan uwan Aliyun kaf sun Jin jina irin qaunar da dangin Malam buban kema Aliyu.
   Tunda yazo garin ko ruwa baisa a bakinshi ba Banda a wajan alwala,Maryaman kawai yakesan gani Kamar xuciyarshi zata fita daga jikinshi,a hankali wani irin zazzabi ke Neman rufeshi da qyar ya riqa daurewa har su Dadi Suka tafi yayin da abokanshi Suka wuce gidanshi inda akayi reception bayan la'asar Suka sake dawowa ko amayar tasu ta dawo su samu su ganta Kamar yadda suke fada,Aliyu dai babu magana sai ido kawai yake bin kowa dashi yayin da idan kanqura mishi ido zaka lura da yadda jikinshi ke barin zazzabi ta cikin gezner din dake jikinshi da Tasha aiki sosai sai idanshi daya boys a cikin glasses.
     Suna zaune a dakin baba Liman na zaure Maryaman dasuka shigo gidan da Ladidin baba,har yanzu shaddarta ke jikinta gari sosai Suka zaga da Ladidin baba.
   Ina Kika shiga ke kuwa Maryama aka nemeki aka rasa tun safe kamar wadda tayi layar Bata,Aliyun da kanshi ke jingine da bango ya rufeshi ruf cike da damuwa bayakojin me baba Liman din ke fada ya juyo an fada daga faffadan zauren nasu.
    A hankali yaji siririyar sanyayyar murta Mai Dadi tace .
    Gidan dakan ruwan Zuma mukaje da Ladidin Baba baba uwa,daga Nan kuma mukaje gidajan qawayanta.
   Uwa !baba Liman ya kira baba uwan daga dakinshi na zaure (qanwar su malam bubace)ta amsa tare da Kama hannun Maryama ta shiga da ita dakin,ta San dai abinda baban zaice kenan.
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
Wata irin ajiyar zuciya ya sauke da kowa sai da ya juya ya dubi Aliyun sosai wani irin tausayinshi ya rufe baba Ali da Baba Liman,shi kuwa idanuwanshi fes ya zube a fuskar Maryaman da aka shigo da ita Yana dubanta baiko qiftawa tamkar wadda ke Naman wani a jikinta.
     "Finally our bride is arrive".
    Nabil ya fada da murmushi a fuskarshi,yayin da su Salman kaf suke kallan Maryama da birgewa yayin da suke mamakin quruciyarta.
     Wani irin murmushi ta saki daya kusa kashe Aliyun a zaune lokacin da idanta ya sauka a kan nabil din.
    "Yaya nabil!ta fada da muryarta Mai Dadi.
   Amaryarmu! Shima ya kirata da sunan da yake kiranta tun da, kusa da baba Liman ta zauna yayin da ta sunkuyar da kanta tana Wasa da hannayanta.
    To baki gaishesu ba su yayan naki ba Maryama sai murmushi kawai kikeyi ko bakiga Haidar bane gashinan ya biyoki?
   Baba Ali ya fada Yana dubanta sabida yadda Aliyun ya tsareta da kallo Yana sauke wani irin wahalallan numfashi.
   Da sauri ta dago kanta tana binsu da kallo daya bayan daya har ta dire kallanta akan fuskar Aliyun lokaci daya gabanta yai wata irin faduwa fara'arta ta qaru da rarrafe ta matso gaban Aliyun ta kasa magana sai dai dariyar da har siraran haqoranta suke futowa baki daya kawai ta kuma kawo hannu ta rufe fuskar sabida dariya da suke ta faman Yi Mata abokan Aliyu.
   A hankali xuciyarshi ke sanyi sabida yadda yaga babyn tashi taji dadin ganinshi sai ya kasa daurewa duk da kunyar da yakeji tasu baba Liman ya Sanya hannayanshi ya janye hannayanta daga fuskarta da ta rufe tana dariya kawai ya kasa magana shima sai dai mammatsa hannayan nata da yake a hankali.
   Baba Liman ne ya Fara miqewa sai baba Ali da sauran abokan nashi duka Suka fita Suka bar Mai dakin sun sani bai iya cewa komai a gabansu a yadda yai tarin abin fadawa babyn tashi.
     Suna Gama fita kuwa ya janyota baki daya ya shigar da ita cikin jikinshi ya matseta ya hade bakinsu waje guda jikinshi na wata irin rawa.
    Da qyar Maryaman ta amshe bakinta Amma ta kasa sauka daga jikinshi sabida yadda yake dada riqeta ga hannayansa daya sarqe a cikin hannayanta ya kasa bude baki har lokacin yai Mata magana,zuyarshi kawai yakeson ta nutsu Kuma  numfashinsa ya dawo dai dai itan ma bugunta ya dawo dai dai.
A hankali siririyar muryarta ta Shiga kunnansa .
    "Shine tunda ka tafi baka taba nemana ba Yaya nifa fushi nake Yi dakai.ta fada tana zunbura baki gaba.
     Cikin wuyanta ya shigar da kanshi Yana shinshinata a hankali yace .
  "Shiyasa Kika gudu Kika boyemin kanki Kika kusan kasheni ko?".
     "Da sauri ta dauko hannayanta ta kamo kanshi tana zare ido tare da kallan jikinshi,fuskarshi ya karbe daga hannunta ya sake maidawa gefa  Wuyanta Yana sake shigar da ita jikinshi.
    'baka da lafiya Yaya Bakaji jikinka akwai zafiba Bari na amso maka magani a hannun Innarmu.
    Ta fada tana yunqurin tashi sake maidata yayi ya maqaleta a jikinshi a hankali muryarsa tana rawa can qasa yace "no pls!stay calm"ya fada Yana sauke ajiyar zuciya.
   A hankali wayarshi ke qara da qyar ya Ciro ya Danna ya Sanya a kunnanshi ba tare daya bude ido ya duba Mai wayarba,bai kuma yi magana ba sai numfashin da yake ta faman saukewa.
    "Kai Malam kada ka cinye musu yarinya fa baba Liman da Baba Ali suna san shigowa so ka kintsa kanka.
    Da qyar ya Zame wayar daga kunnanshi yai ma Maryaman wata irin matsa da sai da tayi qara sannan ya sauketa a kusa dashi ya harde hannayansu waje guda ya rufe da babbar rigarshi yadda Babu Mai ganin yadda ya maqale hannun nata alqawari ne yama.zuciyarshi bai sake barinta balle tai Mai nisan data gwada Mai a yau.
     Nasiha sosai baba Liman ya musu Wanda sai a Nan Maryaman taji an daura aurenta da Aliyun yayin da ya futo da jakar silallan gwal din sadakin nata Yana nuna mata,jikinta kaf ya Fara rawa da wani irin tsoron da Bata San na meye ba,shi ko Aliyun kanshi na qasa a hakan ya kama hannunta da yaji Yana mutsu mutsu fita daga nashi ya riqe gyam.
    "Zakuje ku wuce kada dare yayi muku a hanya ko".
   Baba Ali ya fada Yana duban Aliyun da duk kukan Maryaman ya dagulamai lissafin.

wata miyarWhere stories live. Discover now