🥬🥬🥬🥬

100 8 0
                                    

☘️☘️☘️☘️☘️
*WATA MIYAR*
         ☘️☘️☘️☘️☘️

𝗪𝗿𝗶𝘁𝗶𝗻𝗴
            𝘉𝘺
𝑺𝒂𝒅𝒊𝒚a Musa Rimi
__________________________________
🥬🥬🥬8🥬🥬🥬🥬
Suna tsaka da tattaunawa Aliyun ya shigo cikin falo,a hankali hajiya Fanna ta koma tayi tsit daga masifar da take bin Hajiya Fadila da ita.
    Yarone qarami Aliyun Amma wani irin kwarjini yake Mata tamkar mahaifinsa.
   Cikin sallama ya shigo da muryarsa Mai taushi da bai San hayaniya,a hankali ya riqa bin falon da kallo tamkar Mai neman abu har ya ajiye fuskarshi akan fuskar Hajiya Fadila da take dubanshi cike da bacin Rai da nacinsa ya janyo Mata.
    Kusa da itan yaje ya zauna a hankali ya kama hannunta ya riqe a nashi yace.
    "Yaya Maminah! Akwai damuwa ne?"
     Akwai Aliyu!nice nan na Mata magana akan zaman yarinyar nan da ka dauki duk wata soyayyar duniya ka dora mata ,meye gaminka da ita,banda ma Kai sakarai ne ina dan gida Ina yarinyar yaran gida,daga ita har iyayanta a qarqashinka suke ai,dan haka alaqa ta kusanci tamkar wata taka na yanketa,ga 'yar uwarka nan Nasma idan kewar Zama kakeyi Kai kadai ta isheka duk wata hira da shaquwa kayi da taka ka rabu da wadda bamusan asalinta ba qilama maiyace mu bamu sani ba".
     Hajja ta fada tana dubansa.
   Shi dinma Kallan Hajjan yakeyi tamkar Mai karanta wani abu a fuskarta.
    "Kanajina kuwa ka zauna kana kallona"
    "Ina baby?shine kawai abinda ya furta Yana duban granny din tashi.
    "Tana sama kuma.....
Hajja ta Soma fada Amma ga mamakinta kan ta Kai qarshe ya miqe da wani irin zafin nama yayi sama,Hajja da Fanna suka bude baki cike da madaukakin mamaki suna bin bayanshi da kallo.
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
Tana maqure acan dan koridon hanyar bandaki taci kuka har bacci ya dauketa a kwance a wajan ya shigo dakin,ya tsaya Yana qarewa dakin kallo koina tsab dashi sai itan da bai gani ba.
     A hankali ya taka qafafunshi har cikin dakin Yana dubanta,ya tsaya a hankali Yana duban yadda ta takure a kwance a qasa bacci take amma tana ta faman ajiyar zuciya.
   Tsugunawa yayi a hankali sannan ya sa hannu ya juyo da ita.
   A firgice tamiqe daukacin jikinta na tsima ga zafin zazzabi da jikin nata ya dauka sai bakinta daya haye sosai lebenta har da tsaga sai uban zafi yake Mata.
    "Allah Zan tafi wajan innata yanzu kada ki yankani Zan tafi ba Zan qara ba"
  Ta fada cikin tsuma.
Bude ido yai sosai da sauri Yana dubanta yayin da idanshi a hankali yake rinewa daga fari zuwa ja sabida bacin ran da yakeji Yana bijiro Mai.
     "Nutsu Mana baby uhim!nutsu na gani waye ya bugar min ke?"
  Ya fada Yana caje jikinta.
   A zabure ya miqe Yana kallan bakinta,waye ya bugeki a bakinki?
    Ya tambaya Yana daukarta.
  "Ni Innar mu zanje !ka kaini wajan Innarmu!".
    Maryama ta fada tana hawaye.
   "Nace waya bugeki kina min maganar waike Innarku zakije "you are very stupid Maryama" waye ya bugeki nace.
     Mami data bude qofar ta shigo dakin jikinta a dan sanyaye tace.
   "Kanajina ko! Ka bar batun komai ka hada Mata kayanta ka kai ta can wajan Innarsu inyaso daga baya ta dawo"
    Aliyun ya dubeta a mamakance da wata irin zuciya da take dibansa yace.
    "Sabida me zata koma wajan Innarta Mami bayan da can ba'a wajan Innar tata take ba?
     Kai me yasa ba ka Jin magana ne sai abinda ka qullawa zuciyarka?dole sai na fada maka ga dalili sannan Zan saka abu kayi shi?ka rainani ko Haidar?"
    Baice komai ba sai hadiyar zuciya da yakeyi kamar Wanda yai gudun fanfalaqi,Mamin na tsaye a nan yazo ya wuce ta gabanta ya fita daga dakin.
    Baki dayansu da suke zaune a falan babu Wanda ya kula ko ya kalla sai ma shi da Suka ci gaba da kallonshi Yana sabe da Maryaman a kafadarshi wadda yakejin tiririn zafin da jikinta yakeyi har cikin xuciyarshi.
  🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
     Alh. Bamanga dake tare da baqin shi a gidan baqi wasu baqin turawa da sukazo Masa yanaso ya sallamesu da wuri sabida ya tashi ya wuce gida sabida dare sectary dinshi ya Shiga har cikin falon dan isar da saqon zuwan Aliyun,tunda ya Baro office Suka dauko baqin daga airport yake nan gidan.
    Ko kan ya Isa ga Alh.Bamangan Aliyun ya shigo sabe da Maryaman a kafadarshi.
    Alh.Bamanga ya bishi da kallo cike da faduwar gaba.
    Yana zuwa ya shimfide Maryaman da zazzabin jikinta ya dada Hawa sabida kukan da taci gaba dayi bayan Wanda tayi da fari idanta fal qwalla yace.
     " Dadi! Dadi ka dubi cin mutumcin da akayi min;ka dubi abinda akayimin Dadi aka bugar min ita sannan kuma akace na fitar da ita daga gidan na maidata wajan Innarta.
   Alh.Bamanga da qirjinshi ke bugawa ya duqa da sauri ya dauko Maryaman ya rungumeta a jikinshi sai fama rawar jiki yake tamkar yankan naman jikin Maryaman akayi.
    "Waya tabata hakan har ya haifar Mata da zazzabi haka Aliyu"
Aliyun ya watsa hannaye yace .
    "Ta Ina zan sani Dadi!naje masallaci na dawo na taddata haka sai Mami kuma tace na dauketa na maidata wajan Innarta,Amma anyi threatening dinta ne kaman za'a kasheta idan bata koma wajan Innarta ba.
   Alh.Bamanga da ranshi ya baci sosai ya bude ido ya dubi Maryama da take sauke wani irin Nishi na wahala tausayinta sosai yakeji a cikin zuciyarsa.
   Sallama yayi ma baqinshi shike dauke da ita har asibitinshi,Dr daiyib ya dubata inda ya tabbatar Mai da firgita ta akayi sannan ya hada Mata magunguna akayi Mata allura Suka taho kuma har lokacin shike dauke da ita ko a motar nan jikinshi ya zaunar da ita.
    Babu kowa a falon lokacin da Suka dawo sai ac dake ta faman kuka kawai da qamshi dake tashi a cikin falon.
    Tana sabe a kafadarshi har cikin dakinta;ga mamakinshi Nasma ke kwance sosai àkan gadon Maryaman yayin da aka futo da kayanta baki daya akayi dakin dinsu daga ciki dakin,hatta da takalmanta da school bag duka an ajesu a waje daya.
    Turus ya tsaya Yana duban Nasman dake barcinta cikin kwanciyar hankali babu abinda take damunta.
   A hankali Mami da taji motsin yayi yawa tun daga hawansu saman zuwa bude dakin Nasman ta bude dakinta ta turo qofar dakin.
    Wata irin faduwar gabanta yayi tayi turus kawai tana duban Alh.Bamangan dake sabe da  Maryaman har a lokacin.
    "Wacece wannan? Ya tambayeta yana nuna Nasman.
   "Nasma ce! diyar Yaya Fanna,dazu Suka iso hadda Hajja suna part din baqi baka iso da wuriba shiyasa baka samemu a falo dasu zaune ba".
    Ta fada da Dan kwarin qwiwar da bai Kai ya kawo ba.
     Ita me take anan da bata tafi part din baqin ba ta zauna a dakin wata?ko ita Mai dakin ba zatayi amfani dashi ba wata zata zauna Mata?. 
    Ya kuma tambayarta Yana tsatstsareta da ido.
    Ka Bari Dadi Zan maka bayani!Kai Dan ubanka me nace maka uhim Kai har abada ni yanzu ba Zan ce ga abinda nakeso kayi ba kayi minshi sai raina ya baci?.
   " Fadilah!" Dadi ya kirata da bacin ran da bata tsammanin zai Shiga ba a muryashi.
    Mami ta maida dubanta kanshi zuciyarta na wani irin lugude.
  " Wannan yarinyar ta koma wajan uwarta Zan kwantar da Maryama".
     A firgice tace "haba dadi! Nasma fa 'yatace ta tashin qiyama,kuma kaima Nasma Koda bana aurenka 'yar kace amma harka fifita wata bare da baka sani ba akanta?
     Wallahi na sake cewa ki fitar da yarinyar Nan daga cikin dakin nan ran kowa a gidan nan baqo da dan cikin gidan sai ya baci wallahi.
     Ranta a bace ta dubi Aliyu tamkar shike da maganar ba mahaifinsa ba,ka kyauta nagode da abinda kamin sannan ta wuce ta tada Nasma dake magagin bacci ta riqe hannunta ta wuce dakinta da ita.
    "Kira Mariya! Dadi ya bashi umarni da sauri Aliyun ya juya ya wuce zuwa part din masu aiki ya taso Mama Mariyan ya wuto da ita.
    "Barka da dare Alhaji"ta fada da risinawa.
   Bai ko bi takan gaisuwar taba ya nuna Maryaman.
    " Ki zauna kici gaba da kwana da ita Kamar yadda Kika Saba Bata da lafiya,ki lura da ita kamar yadda Zaki lura da 'yar cikinki,kada ki bari wani ko wata ya cutar da ita a gidan nan kada ki manta itan amanace a hannunki,kada Kuma wani ya Miki wata barazana ko ta meye a gidan,aikina kikeyi,Ni na saki Kuma Ni nake biyaniki.
   Mama Mariya jiki a sanyaye ta qarasa bakin gadan tana duban Maryama da dan tausayi a fuskarta.
   Har daki ya raka Aliyun shima Kamar wani qaramin yaro har sai da ya tabbatar ya Yi alwala da shaf'i da wutiri tukunna ya kwanta sannan ya rufo Masa dakin zuwa dakin Mami,Bata a cikin dakin har toilet Dan haka Kai tsaye ya wuce zuwa part dinsa,tana zaune ta zuba uban tagumi à cikin qayataccen falan nasa
      "Waya bugi yarinyar nan a bakinta har ya Kai ya fasa Mata baki?"
   Ya tambaya ko Zama baiyi ba Yana tsaye akan Hajiya Fadilan.
    Itanma ranta a bace yake game da abinda yakeyi,dan haka cikin Zafi tace.
     "Koma waya daketa ni  bashine abinda yake gabana ba,matsayina a wajanka nakeson ji da har tafi 'yar 'yar uwarka ta jini kake fifita qaunarta akan kowa,meye hadin mu da ita?ko kuma Kai kaiwa uwarta cikinta da riqonta ya Zama dole ban sani ba,ya Kamata idan da abinda kake boyewa ka futo fili ka fada ka daina fakewa da wani qaunarta da Aliyu,Ni na Fara saka shakku àkan irin kulawar da kake bata da har tafi sauran jama'a a wajanka,mutum nawa ne masu yara a cikin maaikatanka kasan kalar yaransune ko kuwa sai dai ita dan itan wata uwace.
   "Cike da nutsuwa ya tako qafarshi har gabanta,a hankali ya tsaya a dai dai kanta yace.
     "Matsayinta kikeson sani a wajena ko?"
    Tayi shiru kawai tana kau da Kai zuciyarta cike da fargaba.
     "Nace matsayinta kikeson sani a wajena ko Ni nayi cikinta muka boye da Malam Buba sabida Yana daga cikin maza daiyus da basa kishin matansu ko?sabida talauci yai Masa yawa Bari ya bani matarsa na dana sai na wadatashi Ni kuma daga cikin tarin ni'imar da Allah yai min ko"ko ba hakan kike nufi ba?".
    Nan ma taqi magana ta juyar da kanta waje daya kawai taqi yadda ta kalli cikin fuskarshi.
    "Murmushi takaici yayi sannan yace "idanuwanki sun rufe kin kasa ganin abinda ya kamata da Wanda bai Kamata ba Fadila,banyi tsammanin kema din kina da halaye irin na 'yan gidanku ba da Baku San komai ba sai San zuciyarku.
   Da sauri ta juyo tana dubanshi ranta Yana sake baci.
    Zama yayi a Gefan kujarar da take ya sake  dubanta sannan yaci gaba da magana.
     "Eh halaye irin na masu son zuciya da kwadayin abin duniya ko ba halayen ku kenan ba,ke a tunanin ki kin dauka ban San maqasudin aurena dake bane?kin dauka dani da mahaifina bamusan abinda kuke yiwa qulafici bane?kin dauka duk wani Abu da kikeyi na shirke shirke tun kan muzo duniya bani da labarinsane? Kin dauka bansan an shigo dake rayuwata bane dan ki dauka musu abin duniya ta hanyar abinda zamu Haifa ki kaiwa kwadayayyan kakanki da babanki,kin dauka na aureki ne sabida ni din aikin da kukayi ya samu Shiga a kaina da mahaifina?
    Hajiya Fadila da daukacin jikinta ke rawa sabida abinda Alh,Bamangan ke fada ta rasa abinda zatace sai faman Bari da jikinta keyi tamkar tana filing daga.
    Qafa daya ya Dora àkan daya sannan yaci gaba.
    "Duk wani Abu da kikeyi a tafin hannuna kukeyinshi Fadila, bilhasalima Ni na yadda na aurekine Dan na koya muku darasi dasa kwadayi da shishshigi a rayuwar a abinda yake ba nakuba,wani Abu da baku sani ba, wallahi ke Kika haifi Aliyu amma baki Isa
Control din xuciyarshi da baqar aqidarku ba.
    Aliyu nawane,jinina ne kuma yake gudu  a jikinshi,kuma Aliyu jikan Maina ne yadda cutarwa ta gagari zuri'ar ku a tsakaninku da Maina to ta gagara ga zuri'ar Bamanga ma daku,na aureki ne dan na maida wasan da kukeyi ya qare a kanku.
    Zan gani Aliyu dankine shikenan Miki a nan duniyar baki daya,duk kuma ta hanyar da Zaki biyo baki Isa juyashi da muguwar aqidarku ba,Zan gani Zaki bawa 'yan uwanki dama ne su cutar dashi sabida kina kwadayin samo musu abin duniya ko kuwa Zaki tsaya dakin daka ne ki Kare rayuwar danki.
     Wannan yarinyar kuma Allah ne ya bama Aliyu nima kuma na bashi,Ina rainonta ne ta yadda zakiji dadin Zama da ita domin itan matarshice, idan baki sani bama a baya Yana da kyau a yau ki sani,Maryama matar Aliyu ce,Dan haka ruwan kine ki dauketa tamkar abar da Kika haifa ki Sami mutunci da kwanciyar hankali kuma ki Sami zuciyar danki,ko ki wulakanta rayuwarta ki cutar da ita ki rasa rayuwar naki dan baki dayanta.
     Kuma inason kiyima duk wani Dan uwanki gargadi, wallahi Wanda duk ya cutar da ita Kota wacce hanya nima ta ita zanbi na ramamata Koda kuwa kece Kika kuma cutar da ita,kuma ki saka a ranki zamanta a gidan nan shine yake riqe da naki,barinta gidan kema hakan yake nufi akanki,ya ragewa gareki ki duba ki zabi abinda yafi Miki a cikin Zama da tafiya,har gobe haihuwar kyakyawan Mata ake a duniya,irin wadda duk nakeso ita Zan samu.
    🥬tirqashi🥬
Har Alh Bamanga ya kammala al'amuran sa na yau da kullum.Hajiya Fadila na zaune a falansa banda hawayen nadama babu abinda takeyi,a duniya ta yadda da komai a kalleta dashi amma Banda rashin yadda da daukarta a maha'inciya,a iya zamansu da Bamanga Bata San cewa bai taba Yi Mata kallan so ba,      Bata San cewa yana kallanta ne a matsayin wadda aka qullo baki da ita dan a cutar da rayuwarshi data zuri'ar su ba,batasan cewa Yana zaune da itane a irin abinnan da bahaushe ke cewa idan kasan maqiyinka jashi kusa da Kai yadda duniya zatasan cewa duk wani abu daya faru da Kai to shine ba.
     Yanzu itan wacce riba ta samu a zaman nata dashi,Aliyu natane,kuma jini ba qarya bane Amma har abada Aliyu bai taba hada qaunarta a matsayinta na uwa da ubanshi ba,Aliyu tun kan ya Soma hankali zai ta qunbiya qunbiya da Abu a cikinsa har sai ya Sami ubanshi shi kadai zai iya budewa cikin shi.
   Candi!kenan magunguna da aka riqa Bata tun Kafin haihuwar Aliyun ya shigo duniya daga mahaifin Bamangan da Bamangan kanshi wani shirine da ake yinsu Dan su tanqware duk wani nufi nasu da quduri na dadewa da mutane da yawa Suka saka burinsu akai.
    Meyasa tun tashin yaran ma Bata lura da yadda Bamanga ya janyeshi daga jikinta ba a matsayinta na uwa sai shi ya Bari yayi mishi irin shaquwar da zakayima uwa da uba.
   Kai Kaicon su da samun gurbatattun iyaye da Basu iya Dora su akan tafarkin gaskiya da dora diginsu na gidan aure akan mataki na gari ba.
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
Safiyar washer gari sukuku Hajiya Fadila ta tashi jiki a nauyaye tayi wanka ta shirya sannan ta sauko daga sama,Hajja na zaune da Hajiya Fanna sai Aliyu da suka zaunar da alama fada Hajjan ke mishi Dan dukkansu daga ita har Hajiya Fanna sai faman numfarfashi sukeyi.
     Sai da ta kusan qarasowa ta lura da Maryama dake kwance àkan qafar Aliyun har yanzu bakinta da sauran kunburi,rai a bace ta kautar da kanta daga dubansu sannan ta Sami kujera ta zauna,duk Suka bita da kallo suna mamakin  kunburin da fuskarta tayi tamkar an Dana fanke abinka da farar mace.
    "Dauketa ka bar nan kuje can kuyi jinyar a falonka ko dakinta".
   Ta fada ba tare da ta yadda ta dubi wajan da Aliyun yake ba.
    "Wai kina nufin yarinyar Nan ba zata koma gidan ubanta ba anan din zata ci gaba da Zama Fadila?ke din wacce irin lusarar macece da Bata iya tsara rayuwar gidanta ba"Hajja Fanna ta fada tana bin bayan Aliyu daya Sabi Maryaman a kafadarshi in a bridal way da kallo.
    Hajiya Fadila Bata kalleta ba kuma Bata daga Kai ta kalli wajan. Da su Aliyun suke ba har Suka haura saman.
   "Qila yau baki da lafiya ko Naga idanki da fuskarki duk a kunbure
   Karan farko da Hajja tayi magana tun bayan zaman Hajiya Fadilan a wajan.
   Idan fal qwalla ta dago kanta,komai da Suka tattauna da Bamanga sai da ta juye musu Hajja na salati Hajiya Fanna na salati,har zuciyarta taji dadin yadda bai taba kallan Fadilan da kima ko wata darajaba baqin cikinta guda tsohon burinsu da take San ya tabbatu àkan Nasma kuma ake Neman a maida kan wata kucaka can da bata Kai kima ko darajar Nasman a kanta ba shine babban tashin hankali ta.
    Zuruf ta miqe tsaye!bazan iya zamaba Hajja,Bauci Zan koma yanzun nan.
    Ido taf qwalla Fadilan ta dago kanta ta dubi Fannan.
    Me zakije kiyi a Fannah,bakiji abinda yace ba?duk wani shirinmu a tafin hannunsa yake".
   Fannan ta tabe baki tace,
   "Barazanace kawai ba wani abuba,sabida yaga ke din kin Zama sakara kuma kin nuna kina tsoronsa,in baccin haka ya Isa ya zauna a gaban idanki Yana fadar irin wadannan maganganun ke kuma dake qudahumace kikayi shiru kina Masa kuka idan ma bugar cikinki yake shikenan kin tabbatar Mai da hakan,Banda rashin sanin ciwan Kai uwar data kawoki duniya ce tazo gidan tun jiya amma har yanzu bai zo ya gaidata ba ya kuma sa qafarshi ya bar gidan.
   Ba dama ayi Miki magana ki hau kawo qabli da ba'adi,to ya wuce,idan kin tsorata ke ba Zaki iya komai ba mu zamuyi Hajja tashi mu wuce.
     To Hajja bata miqe ba sai ma Zama data gyara ta Fara tsarawa Fadilan yadda zata bullowa lamarin;ciki kuwa harda bayar da shawarar ta Sanya a fice da Haidar dinma daga qasar baki data.
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
Kwanaki Tara kenan da Kai bahaguwar ziyarar tasu Hajja Kano,tun hajiya Fadila na zuba idan ganin wani abu ya faru har ta saki jikinta,musamman da Bata Sami Kira ko daya daga mahaifinta ba àkan lamarin.
   Rayuwarsu ta koma normal a gidan tamkar babu abinda ya faru kuma a tsakaninne admission din Aliyun ya futo Wanda daga Fadilan har Aliyun basu San dashi ba,zai wuce ingila cikin kwanaki biyu dan yin digiri dinsa a fannin likitanci.
    Fadila tafi kowa murna da hakan yayin da Aliyun ke cikin tashin hankalulin tafiyar da zaiyi ya bar maryama.
   Cikin kwantar Mai da zuciya da Dadi keyi akayi duk wani Shirin tafiyar tashi,har Maiduguri yaje dashi da Dadi kuma sun dade suna tattaunawa da kakanshi da Dadi dashi kan su dawo din.
    Ranar da zai wuce kuka ya kwana Yi Yana jaddawa Mami riqon amanar Maryama a wajanta har sai da itan ma Mamin taji a zuciyarta lura da Maryama ya Zama tamkar wani wajibine akanta.
    Tun daga airport da suka musu rakiya yake riqe da Maryaman da taci kukan daya haifar Mata da zazzabi,can gidansu dake udb road suka wuce duk Dan tabawa zuciyar Maryama sanyi,Amma  yadda damuwa ta sanyata  wani zazzabi dole ta taitayeta sukabar Dijan dake da tsohon ciki suka wuce asibiti.
    Allura tasha da magani Suka dawo gida,Nan falo ta kwantar da ita yayin da itan ma wani irin bacci ya dauketa a falon,bayan la'asar sosai ta samu ta farka  daga nannauyan baccin da ya dauke,dafe da kanta dake Dan ciwo ta juyo ta taba jikin Maryaman Dan Jin ya zazzabin nata.
   A zabure ta miqe tare da birkito Maryama jikinta na tsananta rawa har ji take tamkar zata yanke jiki ta Fadi qasa,baki da jikinta sai karkarwa suke halittar Maryaman data juye lokaci guda zuwa wata kalar kawai take kalla yayin da qwaqwalwarta ta tsaya da aiki cak buwayi gagara misali
Tirqashi.

https://chat.whatsapp.com/GIpbmHXbDTeEusycmTQnS7

https://chat.whatsapp.com/BFKGOJXfQxHEi5rjoaYwsr

wata miyarWhere stories live. Discover now