JARABTA PAGE 14

52 3 0
                                    

🌹🍃🌹🍃🌹
🍃.•°''°•.¸.•°''°•.🍃
🌹                    🌹👈
*🍃JARABTA😭🌹*
🍃'•.¸            ¸.•' 🍃
     🌹° •.¸¸.•° 🌹
           🍃  🍃 ,
  🍒🌹🍒🌹🍒🌹

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
_{Gidan karamci, rubutu don cigaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.}_
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
https://www.facebook.com/106494781436168/

         🇼​ɾίttεη
             BҰ:​
ᕼᗩᒍᒍᏆᎩᗩ ᗰᗩᖇᎩᗩᗰ
─────────────

*M͟a͟r͟u͟b͟u͟c͟i͟y͟a͟r͟:*
➪FYADE 2020
➪KOMAI NISAN JIFA
➪ABBANA NE
➪ILLAR LUWADI
➪UZMA
➪'YAN BARIKI
AND NOW
*JARABTA*
TRUE LIFE STORY
⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯
*Dedιcaтed тo:*
⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯
➪HAMDALA
⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯
*Masu yimin maganar yaushe zan ci gaba da ƴar lesbian insha Allah nesa tazo kusa kude kuyi shirin shan karatu da waɗanda suka biya kuna rainah next month zan dawo aci gaba da gashi🥰🥰🥰🥰*

BISMILLAHIRRAH MANIRRAHIM

*🇵​αɡε ➪☾24☽*




Innata na watsamin ruwan na farfaɗo na fara kiran
"Baffa Baffa maƙoshi na Baffa ka bani ruwa na sha maƙoshi na zai tsinke cikin sauri ya amshi ruwan a hannun innata ya bani nasha amma san banji abin ya faɗa min ba na runƙa ƙaƙarin amai amma shiru can nace
"Baffa ina jin mutuwa zanyi"
Baffa da inna har suna haɗa baki wajen cewa
"Insha Allah ba za ki mutu ba koma menene Allah zai yi mana maganin sa, suka shiga dani cikin ɗaki Baffa ya ajiye ni ya fita zaure ya yi rubutun  addu'o'i ya kawo min na sha sannan na ji wani abu ya faɗa min cikin cikina na sauke wata ajiyar zuciya na ce
"Baffa ya faɗa min"
Baffa ya ce
" Alhamdulillah "
Innata ma ta ce
Mun godewa Allah "maɗaukakin sarki"
To tundaga wannan ranar muka fara shiga masifa iri-iri na runƙa kumbura ina girma cikina sai ƙara ƙato yake kaina ma  kullum sai ƙara girma yake har ta kai ta kawo idan na fita mutane kowa guduna yake yara kuwa idan sun ganni har suma suke wallahi wallahi a cikin wannan bayanin babu ƙarya   mutanen unguwa suka yi gangami akan lallai sai dai Baffa na ya bar bari na ina fita nida kaina sai fitar ta fita raina ko ina bana zuwa ko san kallon halittata bana son yi gaba ɗaya sai na zama abin kyama daga dangi har bare, innata ta yi neman magani har ta gaji haka Baffana kullum safiyar Allah sai ya yi min rubutu nasha amma abun babu sauƙi har takai takawo idan na fita mutane na jifa ta ganin haka yasa Baffa ya ce mu haɗa kayanmu mubar garin muka dawo nan Masama da zama a nan ɗin ma ban tsira ba ga rashin jituwa da aka sa tsakanin nida mahaifiyata da bamu zama inuwa ɗaya sai dai duk da haka idan lalurata ta tashi bata zaune ba ta tsaye ta yi nan ta yi can ita kam ba ga malamai kawai ta tsaya ba har bokaye take bi, duk inda ta ji ance magani ba ta zaune ba ta tsaye haka rayuwata ta ci gaba da tafiyar mana bana zuwa ko ina sai gida ga faskareren kai fuskata gaba ɗaya halitarta ta canza na zama kamar ba jinsin mutane ba sai nace na fi kama da Aljanu, hakanan idan aljanuna suka tashi a ranar babu kwanciyar hankali daga ni harsu Baffa a haka rayuwa ta ci gaba da shuɗe mana sai wata rana Innata ta ji ance anyi wani baƙon boka mai ba da magani ba ta ko tsaya gayawa Baffa ba don tasan ba zai yadda ba ta kama hanya ta je wurin bokan ta yi masa bayani sai bokan ya ce idan na yi fitsari a tara ayi min wanka da shi inna ta dawo a tsorace ta ce
"Suhaima yau naje neman taimako amma bawon Allah ya ce idan kin yi fitsari in tara in yi miki wanka dashi"
Na dago a razane na kalle ta ta sake cewa
"Kodai bakya son lafiyar ki ne?  Ki bari mu gwada ko Allah zai sa mu dace"
Sai kawai muka jiyo sautin Baffa yana cewa
"To ba a gidana ba wannan shirkar ba za ayi ta dani ba Inna ta ce
"Haba malam dan Allah ance fa wannan shi kaɗai ne maganin waraka amma ka ce a'a"
Baffa ya ce
"Wallahi tallah babu wani maganin waraka wanda bai zo a al'ƙur ani ba duk wani yawon bokaye da ki ke ba shi ba ne mafita mafita ita ce mu dogara ga Allah shine zai isar mana "
Inna ta ce
"Ko Allah dakansa ya ce ka tashi na taimake ka ba ka na daga kwance magani zai zo ya same ka ba "
Ya ce
" nidai na faɗa miki ban yadda ayiwa ƴata wanka da wani ruwan fitsari ba idan ma anyi ba da yawu na ba"
    ya bankaɗe ƙofar gidan ya fita inna ko ta rafka uban tagumi wajen watana ɗaya ina zaune a haka a gida bana fita ko ina saboda ƙaton kaina wallahi girman kaina ya kai girman fanteka nasan mai karatu za ka yi tunanin wannan littafin na JARABTA  labarin ƙarya ne to babu abinda yake ƙagagge wata ranar juma'a bayan Baffa ya fita masallaci inna ta leƙo daki ta ce dani
"Suhaima idan kin gadama ki fito muje banɗakin ki yi fitsarin na yi miki wanka dashi kafin baffanki ya dawo, in kuma ya dawo kika gaya masa ni dake ne"
A lokacin banda wayo na miƙe na bita muka wuce banɗaki na yi fitsari a fo ta ɗauka ta kwaramin tundaga kainah har ƙasan ƙafata tun anan naji kamar anzare min ƙaya a jikina na fara atishawa babu ƙaƙautawa kunsan ance tsafi gaskiyar meshi cikin ikon Allah na fara dawowa dai-dai ko sati banyi ba na koma yadda nake a lokacin Baffa ya ƙara samomin makaranta a nan garin Masama naci gaba da boko da arabic




     MAIDUGURI

Ummu kullum cikin zuba ido take  ta ga ya ta Allah zata kasance dasu yau ta kama ranar asabar bayan Baba ya dawo gida Mama ta same shi da maganar Suhail ta yi mai bayanin komai ya ce babu damuwa zai je ya samu malam gwani duk yadda suka yi zai sanar dasu

Washe gari bai yi ƙasa a gwiwa ba ya je ya samu malam gwani ya yi mai bayanin komai, Malam gwani ya ce a taho da yaron ya ganshi kafin yasan abin yi


Haɗin ƙarin girman Nono

Gwanda
Ki haɗa a barba
Mangwaro
Ki fere su ki yayyanka su ƙanana ki shanya su subushe sai ki zuba ruwan ɗumi a kofi ki ɗibi su gwandar bussasu ki zuba a ruwan ɗumin ki runƙa sha a haka za ki yi mamaki suna ƙara girman Nono




HAJ MARYAM

Labarine akan wata baiwar Allah da aljanu suka addabi rayuwartaWhere stories live. Discover now