JARABTA PAGE 20

76 5 0
                                    

🌹🍃🌹🍃🌹
🍃.•°''°•.¸.•°''°•.🍃
🌹                    🌹👈
*🍃JARABTA😭🌹*
🍃'•.¸            ¸.•' 🍃
     🌹° •.¸¸.•° 🌹
           🍃  🍃 ,
  🍒🌹🍒🌹🍒🌹

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
_{Gidan karamci, rubutu don cigaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.}_
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
https://www.facebook.com/106494781436168/

         🇼​ɾίttεη
             BҰ:​
      SAKATARIYA
─────────────

*M͟a͟r͟u͟b͟u͟c͟i͟y͟a͟r͟:*
➪FYADE 2020
➪KOMAI NISAN JIFA
➪'YAN BARIKI
AND NOW
*JARABTA*
TRUE LIFE STORY
⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯
*Dedιcaтed тo:*
⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯
➪HAMDALA
⎯⎯⎯⎯⎯⎯⎯

BISMILLAHIRRAH MANIRRAHIM

*🇵​αɡε ➪☾20☽*
End. End   End

Suhaima ta ɗago ta kalli Inna Fati ta ce
"Nagode da tunatarwa inna Fati kuma ina roƙon Allah ya bani lafiya dama marasa lafiya baki ɗaya " ta amsa da
"Ameen "

Haka rayuwa ta ci gaba da shuɗewa kwanaki suna tafiya inna Fati kullum cikin bawa Suhaima magani take babu dare babu rana har natsawon sati biyu, sai ga Suhaima ta yi kyau ta gyagije ta murje jiki ya yi kyau duk girman Nonon nan sun tsotse duk da babu kan Nono amma Nonon ya yi kyau ba kamar da ba, a ranar da ta cika sati biyu a ranar Innarta da Bello da baffa suka zo ɗaukarta sunyi matuƙar farin cikin ganinta ta samu lafiya duk abinda suka ba inna Fati ba ta amsa ba face kuɗin magani sauran ƴan jinyar nata ma wasu har sun koma gida suma daga nan suka tattara suka koma gida murna a wajensu har ba'a misaltawa, Ammi kuwa mahaifiyar Bello ta yi mamakin ganin Suhaima ta warke sai dai har yanzun ƙiyayyarta na nan a cikin zuciyarta kunsan duk wanda ya riga ya ce bai son ka to zai yi wuya  ya soka sai wani ikon Allah haka dai zaman yake Shukrah ma ganin soyayya ta dawo sabuwa tsakanin Bello da Suhaima sai ta fara neman zaman lafiya

     *********      **********

A ɓangaren Ummi kuwa Suhail kullum lafiya ƙaruwa take yau ta kama ranar lahadi mama ta leƙa ɗakin ta ce
"Ummi tunda yanzun Allah ya bawa yaron nan lafiya gashi har ya fara zama to ku shirya ku koma gida"
Ummi ta ce
"To Mama"
Tundaga ranar suka fara bankwana da jama'a sun samu shatara ta arziki, ranar Alhamis kuwa suka dawo gida, nan da nan gida ya ɗauka masu farin ciki na yi masu baƙin ciki na yi Allah ya bawa Suhail lafiya su gwaggo ta kasa ɓoye farin cikinta dangi na nesa da na kusa sai zuwa suke taya su farin ciki

a ranar dai Ummi da kyar ta samu ta runtsa washe gari da asuba da ta farka ta yi sallah ta idar ta ɗauko litafin azkar ɗin safiya ta fara yi kamar haka tana ƙara neman tsari a gurin Allah

*Bismillahirarrah manirrahim*
*Allahu la ilaaha illaahu huwal hayyul ƙayyum laa ta'akhuzuhu sinatun walaa naumun lahu maa fis samaawati wamaa fil ardhi man zallazii yashfa'u indahu illa bi iznilah ya 'alama ma baina aidihim wama khalfahum  walaa yuhiiduuna bi shai'in min ilmihi illa bi ma shaa'a wasi'a kursiyyuhus samawati wal ardhi, walaa ya'uduhu hifzuhuma wahuwal aliiyul aziimu"*
*Ƙulhuwallaahu ahad*
*ƙul a'uzu bi rabbil falaƙi*
*Ƙul a'uzu bi rabbin naasi,,,,,*

*Asbahana wa asbahal mulku lil-laahi wal handu lil laahi laa ilaaha illallahu wahdahu laa shariika lahu lahul mulku walahul hamdu wahuwa alaa kulli shai'in ƙadiir, rabbi as'aluka khaira maa fii haazal yaumu wa kyaira ma adahu wa'auzubika min sharri maa fii haazal yaumi wa sharri maa ba' adahu  rabbi a uzubika minal kasali wa su 'il kibari rabbi a uzu bika min azabin fin naari wa azabin fil kabari*

Bayan ta kamma ta miƙe ta cigaba da ayyukanta mutane na shigowa har ila lau ba ita ta samu hutu ba har yamma bayan ta idar da sallah nan ma batayi ƙasa a gwiwa ba wajen azkar ɗin yammaci ta ce kamar haka
*Amsaina wa amsaal mulku lil-laahi,,,,, rabbi as aluka khaira maa fii hazihil lailati wa khaira maa ba'adahaa wa'a uzu bika min sharri maa fii haazihil lailati wa sharri ma ba'adahaa,,,,,,,*"

*Allahumma bika asbahana wa bika amsainaa wa bika nahyaa wabika namuutu wa ilaikan nushuuru*
Ya Allah da ikon ka ne muka wayi gari kuma da ikon ka ne muka shiga maraice, kuma da ikon ka ne muke rayuwa, kuma da ikon ka ne muke mutuwa kuma izuwa gare ka ne matattara take

*Allahumma anta rabbi laa ilaaha illa anta khalaƙtanii wa anaa abduka wa anaa alaa ahdhika wawa'aduka mastaɗa'atu a'uzu bika min sharri maa nasa'atu abuu u laka ni'imatika alayya wa abuu u bi zanbii, fagfirlii fa innahu laa yagfiruz zunuuba illa anta"*

*Allahumma inni ashbahtu ushhdu hamalata arshika wa malaa'ikataka wa jamii'a khalƙika annaka antal laahu laa ilaaha illa anta wahdahu laa shariika laka wa anna Muhammadan abduka wa rasuluka"*

Tayi ta zayyano addu'o'in wanda idan nace zan faɗa muku zan cinye lokaci
Kafin daga bisani ta ɗaga hannu sama ta yi godiya ga Allah ta shafa

Bayan shekara biyu Suhaima ce a kitchen tare da Shukrah suna aiki suna hira Ammi na zaune a ƙofar ɗaki sai ga Gwoggo tsohuwa  ta faɗo da gudu tana kuka tana faɗin Suhaima kiyi haƙuri lallai nasan an haɗa baki dani an cutar dake, tun daga duniya Allah ya fara nunawa Malam tsoho makumarsa yanzun koda na baro gida yana ta aman jini da hanta manya- manya duk halittarsa ta canza yana ta tona asirin abubuwan da ya aikata ashe duk surukan gidan nan da suke mutuwa da ƴaƴa shike cinye su dan Allah Suhaima kiyi haƙuri dani aka haɗa baki aka baki abincin da Malam tsoho ya bayar " dukkaninsu sai suka ƙaraso wurin gwoggo suna kallonta kamar mahaukaciya,  Suhaima ta ce
"Ai ni lalurata Allah ne ya ɗaura min kuma shi ya yaye min ban taɓa damuwa don wani ya cutar dani ba saboda duk wanda ya yi abu domin ya cutar dani na barshi da Allah ta sa kuka ta shige ɗaki, Ammi da take fama da ciwon ƙafa dakyar ta iya miƙewa ta ƙaraso ta ɗaga Gwoggo tsohuwa ta ce
"Yanzun ina Malam ya ke "
Ta ce nabarshi a ɗaki jiki babu daɗi nan suka kama hanyar zuwa wajen malam tun a ƙofar gidan suka fara hango wuta tacinye ɗakin da yake wata irin ihu Ammi ta saka da Gwoggo tsohuwa nan da nan mutane aka cika aka zaro Malam tsoho ya ƙone kurmus masu tausayawa na yi masu kuka na yi Malam tsoho dai ƙarshen maitar sa kenan

Bayan shekara biyu ne na yi tattaki har garin Zamfara ina sauka na hau adai-daita ta sauke ni a ƙofar wani ɗan ƙaramin gida, da murna ta na shiga ina sallama sai ga wani ɗan ƙaramin yaro wanda ba zai wuce shekara biyu da wattanni ba ya taho dagwai-dagwai dashi yana yi mini Oyoyo anty Maryam, na duƙa na ɗauke shi na ɗagashi sama nace Oyoyo ɗana, a dai-dai lokacin ne Ummi ta fito daga ɗaki ta ce
"Hajiya Maryam yau kece a garin namu?  Lale lale"

Na yi murmushi nace
"Wallahi Ummi nayi tattaki ne nazo duba jikin ɗana Suhail  "
Ta ce
"Suhail ai shine riƙe a hannunki"
Na yi sauri na ƙara kallonsa na ce
"Godiya ta tabbata ga sarkin da yake fitar da rayayye a cikin matacce godiya ta babbata ga Allah maɗaukakin sarki lallai komai ya yi farko zai yi ƙarshe"
Ummi itama ta amsa da Alhamdulillah ta rumgume ni nima na juyo na kalli masu karatu nace

"Alhamdulillah"

Daga ƙarshe ina roƙon alfarma akan kuyi amfani da abubuwa masu amfanin dake cikin wannan ɗan taƙaitaccen labarin kuyi  watsi da mara amfani inda kuka ga kuskure kuyi min uzuri domin kunsan ɗan adam tara yake bai cika goma ba ina godiya masoya na kuma ina roro da kuyi min addu'a nima Allah ya biyamin buƙatuna na alheri daku baki ɗaya

Sai mun haɗu a littafina na gaba konace wanda na fara wanda nayiwa laƙani da ƴar lesbian kuyi haƙuri zan canza masa suna saboda masu yimin gyara akan sunan bai dace da littafin ba zai koma

U ARE NOT FAIR TO ME

       SAKATARIYA ✍🏼

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Feb 25, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

Labarine akan wata baiwar Allah da aljanu suka addabi rayuwartaWhere stories live. Discover now