A jihar katsina karamar hukumar Bakori a nan na hango wasu yan mata su biyu sunfito ko wacce dauke take da fara'a da murmushin jin dadi na zana jarabawar karshe na NECO a wani secondary school da ake kira da "FGGC Bakori"
Yan matan dana hango su biyu daya fara daya baka suna ta zabga sauri bakar fadi take Noor kiyi sauri mu koma gida kafin sauran su fito suce sai sunyi mana signout dan wannan uniform din auta zan bawa gaskiya bazanyi asara ba Wanda naji an kira da Noor tace Fatee kenan sai kace baki san halin babana ba kinfi kowa sanin halinshi gashi nan yake koyarwa kuma kada ki manta nayi wa auta alkawarin uniform dinnan har suka fito basu ci karo da kowacce yar ss3 ba suna fitowa kuwa suka yi sa'a ga mai adaidaita sahu suka tsaya ciniki , malam funtua zaka kaimu layin yan wanki da guga mu biyu mai adaidaita yace 200 Noor tace 150 mu biyu yace shiga muje amman da changi hannunku Fatee tace eh akwai suna ta waige waige suka shiga (kasancewar futua da bakori babu nisa) suna isa fatee ta bada kudin suka sauka gida mai bakin gate naga an sauke su duka biyun suka shiga ciki gida ne irin compound house dinnan mai dauke da flat guda biyu kacal da dakuna uku uku. Sai naga su biyun sun shige farkon flat din. Sai yanzu na kare ma wacce naji ana kira da Noor kallo farace sol ita bata cikin jerin wa'inda za'a kira da munana ba tana da kyau iya misali she is chubby and kind of short ma'ana wato tana dan da kiba kadan kuma batada tsawo duk da baza'a kirata da gajera ba. Fatima kuma baka ce ita ma kyaunta daidai gwargwado tana da tsawo kuma siriruwa ce saidai duk da haka Noor ta fita kyau. Suka shiga da sallama Noor na kiran mama da karfi tana fadin Kitaya mu murna mun kammala jarabawar mama ta fito daga daki dauke da murmushin jin dadi Allah ya bada sa'a 'yayana suka Amsa da Amin inda Fatima ta gaida mama tana tambayar ko an kawo makullin gidansu nan inda ta ansa tayi gaba tana ma Noor sallama dakaga mama kasan cewa ita ce mahaifiyar Noor din saboda kamar su ta bace saidai mama saboda shekaru sunja Noor din tafi mama haske sosai.Wacece Noor?
Noor wacce ake kira da Aisha Abubakar su uku iyayenta suka haifa Sufyan & Bilal duk yayyenta ne ita kadai mace. babanta malamin makaranta ne a FGGC bakori Malam Abubakar Bindawa inda yake koyarda mathematics mahaifiyar Noor Hajiya Zainab Audu Likita (gynecologist) ce a General hospital dake funtua. Baban Noor Allah ya dora mishi masifa wanda ko yaranshi da matarshi gudun zama inuwa daya sukeyi dashi idan yana parlor kuwa duk suna daki idan yana daki suna parlor. Duk wani musulmi yasan cewa Allah ne gatan bawanshi amman mahaifiyar noor itace cin su shan su da suturar su bawai mahaifinsu baya samun albashi bane. Yan mata yake kashewa idan an biyashi domin daidai da biro sai zainab matarshi ta siyo mishi da sunan bashi zai biya idan anyi albashi amman da anyi sai ya hau fada yana zaginta yana fadin bata tausaya mishi kullum cikin kiran babu, iyayen duka su biyu sun dage akan bawa yayan su tarbiyya na gari. A dalilin wannan dawainiyar da maman Noor keyi ya haddasa mata hawan jini ga masifan miji kullum idan yana gida ba zaman lafiya takamarshi shi yasata bokon saboda auren wuri da musuluntar da tayi iyayen ta suka juya mata baya shiyasa yake wulakancin da yakeso amman daidai da rana daya bata taba maida mishi magana ba. Noor yarinya ce mai addini da kamala baka taba ganin ta fita hakanan idan ba babban dalili ba islamiya ko aikenta akayi sai kuma ziyara idan ta kama.
Cigaban labari.... bayan wata uku WAEC ya fito inda Noor taci 8 courses a cikin 9 inda ta fadi Hausa Fatima kuwa ta lashe duka papers dinta duk suna ta gode ma Allah a lokaci daya yanayi fuskan Noor ya canja idan ta tuno yau saurayinta Bello zai gabatar da kanshi a matsayin manemin ta duk da tasan abune mai wahala baban Ta ya amince saboda shi mutum ne wanda yakeson 'yayan shi suyi Boko duk da kuwa bashi zai biya kudin makarantar ba tayi zurfi cikin tunani ta tsince muryar Fatima na fadin nasan me kike tunani ki kwantar da hankalin ki InshaAllahu baba zai Amince tunda kinga mungama secondary school fatima na mikewa tana fadin kinga time dinmu ya kare a cafe dinnan muje ayi mana printing mu tafi gida tunda Kinga azahar din da Bello yace zaizo ta kusa suka tashi suka tafi gida. Bayan sallar azahar daidai Bello ya iso bakin gate din gidansu Noor ya buga wayan mama kasancewar da wayan mama Noor ke amfani bugu uku Noor ta dauka tayi sallama ya amsa ya sanar da ita cewa ya iso nan take zuciyar Noor ta hau bugun dari dari ta sanar da mama domin ta fadawa baba kasan cewar yau weekend baba na gida. Mama duk da tasan abune mai wuya da murnarta taje ta sanar da mijinta abunda yake faruwa saboda zasu sauke nauyin da Allah ya dora musu itama tadan huta nan take fuskan shi ya canja kala ya hau masifi yana fadin a gaya ma bakon tun wuri ya bar mashi gidanshi kuma alokacin Noor ta shigo dashi cikin falo kallon da yayi ma Noor ne yasa tayi saurin shigewa ciki, Baba ina wuni cewan Bello shida abokinshi suka duka har kasa hannu Baba ya daga musu bana bukatar gaisuwan ku inda baba yace mishi kada ya kara zuwa wurin yarshi karatu zatayi a karshi yayi musu koran kare yana ta huci ya zazzaga balaeen daya saba
YOU ARE READING
TAWA KADDARAR
RomanceA true life story💔💔💔 Gargadi ga iyaye wanda suke dagewa akan yaransu sai sunyi boko bayan su yaran Aure ne a gaban su. KARATU BAYA HANA AURE, AURE BAYA HANA KARATU. Da yaranku su fada halaka gwara su raya sunnahn manzo (SAW) Amin!!! HUKUNCIN A...