Noor ta na daki ta na ta kuka saboda irin wulakancin da baba yama Bello bazata iya kara hada ido dashi ba saboda kunya💔💔💔😭😭😭, Tun tana kira yana dauka har yabar kiranta inda ya fada mata gaskiya shi aure yakeso yayi Allah ya hada kowa da rabonsa.
Result ya fito Noor da Fatima an samu Microbiology a ABU zaria suna zaune suna hirar makaranta sai hirar kuma gaba daya ya koma kan bikin Fatima wanda ya rage saura sati uku suna ta shawarar abubuwan dazasuyi kasancewar bawasu kawaye ne dasu dayawa ba. Wasa wasa cikin ikon Allah anyi biki an gama lafiya inda aka wuce da Amaryar faruk Zaria fatan mu dai Allah ya ba Amarya zaman lafiya da yara nagariAn fara late registration a makarantar su Noor inda take sanar da mama akan idan ba'a biya mata ba zatayi asaran Admission dinta saboda an kusa rufe biyan kudin makaranta, mama taje ta sanar da mijinta ya hau masifa akan cewa shi za'a wulakanta ko tausayin shi bataji kudin makarantar ma bazata iya biya ba sai an same shi toh ta zauna next year sai ta rubuta jamb lokacin ya samu kudin da zai biya mata a yanzu kam baidashi yana ta zazzaga bala'ee ranar farko da mama ta daga ido ta maida mashi magana akan cewa ita burinta diyarta tayi karatu gidan mijinta amman tunda shi ya dage akan cewa diyarshi sai tayi jami'a gashi gata ita biyar dinta baziyi ciwo ba nan mama ta birkice mashi tana ta masifa kunsan an ce mai hakuri bai iya fada ba, Noor na ganin kalan tashin hankalin da gidansu ke ciki ta hau kuka haka ta karasa ranar cikin tunanin halin da zata shiga idan ba'a biya mata kudin makaranta ba mama sai da ta yi kwana biyu bata sauko ba inda lokaci daya tausayin yarta ya mamaye mata zuciya ta bata kudin komai dazata yi amfani dashi.
Noor an fara makaranta tana zaune cikin main campus dake samaru komai na tafiya yanda ya kamata inda dakin da aka bata gabadaya yan level 1 ne kuma yan department of science dukansu suna subsiding da courses din juna. Guda daya ce take lectures a kongo. Noor kawayenta 3 a makaranta gaba dayansu babu wacce take zama a hostel fatima,Asiya & khadija suka hada click daya Fatima wacce kowa yasani kawarta ce tun a gida tana da ilimi sosai sai Asiya wacce itama ba laifi sai kuma unserious one din khadijah wacce aka fi kira da Dizz ita bata damu da makaranta ba ga tarin samari iri iri tun Noor na ma Dizz fada har itama ta fara sha'awar yanayin rayuwar Dizz azo lectures lokaci baiyi ba a fa fita watarana ma a ki zuwa, Fatima abun yazo yana damuta a kullum cikin ba Noor shawara take inda Noor ke ganin takurar datake mata yafara yawa. A haka akazo akayi exams Noor ta samu 2.10 Fatima ta samu 3.56 Asiya kuma 2.90 khadija 1.40 khadijah tana matakin probation tunda ka'idar makaranta itace 1.50 koda Fatima taga result din Noor abun kwatakwata baiyi mata dadi ba. Amman ganin Noor ta fita harkarta sai dai in sun hadu a lectures a zauna wuri daya daga baya ma ita da dizz suka fara tsame jikin su suna yawo su kadai inda suka hadu da wayayyun yan bariki masu zaman kansu a OFF K idan Dizz tafito a hakazasu hadu gidan kawayen su (a hankali Dizz ta fara gwadawa Noor rike manyan kudi tunda a cewar Dizz iyayen Noor basu wani bata kudi tunda baya wuce 10k a wata ) duk da dai ita Noor batasan ta wace hanya ake samo kudin ba sai dai a bata saboda a gaskiya Dizz batada rowa.
Watarana dizz da Noor sun je gidan kawayensu inda suka tidda gidan a cike ga mata da maza zaune ana ta shan shisha wasu kuma suna shan sigari daki ya cika da hayaki Noor ta fita rai a bace daga dakin tunda bata taba ganin irin wannan a gidan ba a nan dizz ta taba wani mai suna mukhtar a kan yaje ya sameta a waje. Hello miss pretty cewar mukhtar, H... dagowan datayi ne yasa muryarta sarkewa ta kasa fadin abun da tayi niyya saboda haduwar Mukhtar ta kafeshi da idanu sai da ya kara maimaitawa sannan ta rude ta daidaita kanta ta ansa shi tana murmushi, can i sit? Yes of course. Tace mishi sannan ya zauna ya mika mata hannu Hi my name is Mukhtar abunda Noor bata tabayi ba wato zama kusa da wani balle har akai ga shaking hands amman sai ta tsinci kanta da mayar mashi da gaisuwarsu ta hanyar mika mishi hannu. Tundaga wannan rana kullum sai mukhtar yazo gaban hostel dinsu Noor soyayya me karfi Noor tafarayi wa Mukhtar (Nikam nace batasan halim campus guys bane suna da shiga rai💔) satin Mukhtar 2 da fara zuwa wajen Noor ranar wata asabar da daddare Noor tan zaune tana tunanin rayuwar da ta jefa kanta yanzu yaushe rabon da ta je lecturers? Sai kiran mukhtar ya shigo wayan ta tayi mamaki saboda 8 ya wuce harda Rabi ana neman 9 ta fita ta ganshi yazo shikadai batare da wani abokinshi ba kasancewar su biyu suke zuwa saboda abokin yana da budurwa hostel dinsu daya, suka gaisa cikin mamaki ta tambayeshi Abokinshi Khaleepha inda ya sanar da ita baijin dadi, sai gani tayi mukhtar ya bude mota wai su zauna ciki suyi hira da kaman bazata shiga ba sai ta tsinci kanta da rashin gardama shikuma ya zagaya ya ja mota can gaba da hostel a dan wani daji yayi parking a dan tsorace tace wai Mukhtar ina ne nan sai jitayi ya rike mata hannu yana cewa baby you know i love you right a dan rude tace wai meke faruwa baby ?ya kara rike mata hannu yana murzawa a hankali yana kallonta sai tsintar kanta tayi tana cewa yes bata an kara ba sai jin bakin shi tayi cikin nata nan ta tattaro dukkan wani karfi nata ta tureshi tana hawaye, wai baby mene haka ya fada rai a bace lokacin idonshi yayi ja, tace baby abunda mukeyi bai kamata bai dace ba saboda sanin kanka ne Allah da Manzonsa tsirada Aminci su tabbata a gareshi sun hana kebewar mace da na miji a wuri daya... kafin ta karasa magana yace taje tunda haka takeso yaje ya taba wasu taje shi zaije ya nemi wasu kuma daga yau karta kara kiranshi a waya satin su biyu bai tabayi mata haka ba taje kawai tunda tanason ya mutu cikinshi yayi ta ciwo ( toh my watt readers what do you think will happen to Noor , is she going to allow him or the opposite thank you so much for the time spent in reading I promise you this is going to be amazing a heart touching story this story happened some years back May Allah swt bless you All)
YOU ARE READING
TAWA KADDARAR
RomantikA true life story💔💔💔 Gargadi ga iyaye wanda suke dagewa akan yaransu sai sunyi boko bayan su yaran Aure ne a gaban su. KARATU BAYA HANA AURE, AURE BAYA HANA KARATU. Da yaranku su fada halaka gwara su raya sunnahn manzo (SAW) Amin!!! HUKUNCIN A...