Fitowarta keda wuya aka jefo mata takalmi sai agoshinta abunka da mai farar fata don ma wahala ta dusar da hasken ai da ba haka ba sai jini tayi saurin saka hannunta ta rufe goshinta sai jini nan take jinin ya bata gaban rigarta tayi waje da gudu tana kuka
Daidai lokacin fitowar Alhaji lawal sai ya matso dab da ita yana fadin tanko kawo ruwa abuta maza tanko ya fito aguje ba tare da sanin abunda maigidan nashi zaiyi da ruwa ba tunda ba lokacin sallah bane
Nan take ya hango maigidan nashi yana ba Ranaa Amaryar Sama'ila hakuri jini yana ta zuba daga goshinta
Tanko yazo ya kamata suka zuba mata ruwa afuskanta ta goge jinin ya duka yana bata hakuri suna cikin hakane sama'ila ya fito yana ta bala'i yana tana Ina ne? Sai alhaji lawal yace haba sama'ila kuji tsoron Allah yarinyar nan ku daina azabtar da ita kai da azeema ya za'ayi an baka amana daga kasa zuwa kasa kazo kana cin amana, Wato shi amana wani abu ne wanda wallahi duk wanda ya ci shi sai ya wahala arayuwa, shuru sama'ila yayi yana sauraren alhaji lawal yana kada kanshi kamar wa'azin yana shigarshi saboda a zahirin gaskiya inda ba alhaji lawal bane mai kudin layinsu ko ince unguwarsu da bazai saurareshi ba, nan take yace tanko ya raka Ranaa wurin mai dakinshi wato mariya zata bata kariyar farko wato first aidSama'ila Buba Gwarzo haifaffen Dan garin gwarzo ne dake cikin garin kano, Nigeria. Shine 'da daya tilo ga gwoggwo Larai da marigayi mallam buba Karatun sakandiri ne ya kawo shi garin kano wanda ya tsaya a aji biyu ma'ana js2 daga nan yabi masu saida gwanjo a kasuwar wambai kamar wasa ya daina boko islamiyyar ma duk ya yar sai dai addu'an gwoggwo larai
Ana haka kasuwar gwajo ta budewa sama'ila yana shekara ashirin da hudu a duniya yazo ya siye gidan makocinsu da ya Rasu ya hade da gidansu mai daki biyu da tsakar gida sai ban daki daya da wurin girki ya buge ginin yayi ciki da falo kashe uku ban daki biyu da wurin girki babba wanda akayi masa mabudar fitar da hayaki sannan ya samu gwoggwo da maganar auren azeema yar mutan zaria
Ankai kudin auren aka saka shekara da rabi bikin
Lokaci baya jiran kowa akayi biki alokacin yana shekara 26 ita kuma azeema tana sha shida aka kawo wa gwoggo amana, gwoggo larai kam ta rike amana sosai amma makircin azeema shine ya fara kawowa zaman lafiyan gidan mallam buba matsala saboda zata saka sama'ila adaki kamar 'danta tace mishi gwoggo tayi kaza gwogga tayi wannan tun baya dauka har ya fara
Akwana a tashi kwanaki sun ja!
Salamu alaykum larai na nan kuwa, daga soro ake sallama gwoggo ta amsa daga cikin daki inna tabawa tsohuwar dake karshen layi ta shigo da 'yar jikallenta hassai
A'ah tabawa ke ce da sanyin safiyar nan, eh wlhy ke dai ganinan nazo bankwana, bankwana fa? Mutuwa zakiyi? Inna tabawa tace kaura zamuyi zuwa kano Chan Adakawa umar('Dan tabawa) ya siye manah gida toh kinsan yayi amarya kuma na samu daki achan shine zamu kano muga yadda Allah zaiyi
Ikon Allah! Tabawa yanzu mey rabawa zatayi halinta, damah mutuwa ko rayuwa sune ke hadawa ko su raba tabawa ta amsa da e wlhy tana kokarin zaunawa akan shinfidar da gwoggo tayi musu tana fadin ke jikallen inna zo ki zauna manah damah ke za'a bar mun muyi zaman mu anan
Inna tabawa tace toh ai kuwa gata nan sai ta zauna tunda Chan umar 'ya 'yansa sun kai biyar fa ke kuma baki da jika ko daya Ina ga azuri'ar ma ba'a taba bari ba sai ta kwashe da dariya sai larai tace Allah bai kawo ba, ai ke kika sani, inda nice da tuni an kwashe kayan wancan dakin an kawo amarya don mu samu kukan jarirai da kuma kudin laraba na 'ya'ya
Kaji tsohuwa tazo zata kawo muna kinibibi acikin gida yo kece ke bada haihuwar muyar azeema daga sama. Lah larai kinji yar mutan zazzau ko? Rashin mutunci duk ya kare gaba daya akan su cewa tabawa ai duk rashin mutunci akanku ya kare munafukai dai akarkashi wuta suke azeema ta kuma gayamata da masifa tana kada kugunta kamar mai yi da sa'ar ya, lallai larai kedai kin zama abun tausayi 'da daya dilo amma baiyi sa'ar matar aure ba gashi kuma ba Batan wata shekara kusan biyar abu kamar baki sai ki mike ki taimaki 'danki kada ya mutu mosai tabawa ta miki tana kakkabe jikinta ta kuma cewa Indai da gaske kina son hassai tazo ta zauna dake toh zan turo ta da kayanta gobe kada kema ki mutu mosai ba 'Dan kuma ba jika, ke kika kashe mata 'Dan azeema ta kuma tambayar tabawa a harzuke a'ah cewar tabawa kedai ce kika shanye mata 'da jinin mayyu tabawa tayi waje tana fadin Ina neman tsari daga gareka rabbana
Azeema ta juyo kan gwoggo da tayi tagumi cike da rashin kunya tana fadin wato gwoggo haka kike gayama kawayen ki ban taba batan wata ba ko toh shikenan ta suri gyalenta akan kofar dakinta ta fita fuuuuDaga Soro ta jiyo kukan Azeema tana gayawa sama'ila karya da gaskiya haka ya fado tsakar gida yana huci ya shuru kafa yana hargowa damah shi sama'ila dan rigima ne gashi kuma yaga gata iya gata
Gwoggo ya za'ayi ki dinga aibata azeema cikin jama'a kowa naji kina cewa cikin gidanki ba'a taba batan wata ba ai ba laifinta bane nine banyi mata ciki ba kina kiba ko? Nidai ki kyalemin mata ta kawai azeema ya amsa tana mu koma kano Chan unguwar dasu tabawa zasu koma muje muci dadi mu barta nan kawai
Haka za'ayi ma Cewar Sama'ila yayi daki yana fadin zanje kano din in duba masauki din ya dauki buta yayi ban dakinsu shida matar sa
YOU ARE READING
Kyautar Allah(Allah's Gift)
Romance#TrueLifeStory #Halfcaste #love #lovestory #Hausa #hausanovel #yemani #nigerian #marriage #princess #Royalty #yemaniprincess