A Garin Kano fa? Shuru shuru har daya na dare babu sama'ila ba zancen shi gata ba 'da ba kowa agidan daga ita sai ita a haka ta kwana tana jin ba dadi da shakku Indai ba wani abu bane ya sameshi ba har safe da kyar ta waye gari ga yunwa da ta addabe ta haka ta leka taje kofar gida ta kira almajiri ta aikeshi ya siyo mata wainar fulawa ta zauna taci abunta ta sha ruwa
Ya shigo gida wuraren goma da minti arba'in ya samu goggo tana gyangyadi yana zama gab da ita sai tayi firgigit tace ya akayi ka dade haka ai na dauka ka koma Chan kano din yayi murmushi yace cikin Daren nan tace aww toh zaka ci abinci taliya ce da mai da yaji yayi saurin cewa manja tace eh tana murmushi din tasan abincin da yake sone yace akawo mun da fura irin ta dazu zata mike sai yace goggo Ina yarinyarki dinnan ne? Ya kawo mun manah ke ki huta tayi shuru Chan tace ai ta kwanta gobe akwai makaranta sai hassai ta leko tace goggo gani nan ai banyi baccin ba karatu nakeyi sai goggo tace toh maza kawo mishi taliya yace sai a lokacin hassai ta ganshi ashe dai kyakkyawa ne ta wuce ta gabanshi shikuma yake gayawa goggo ai ya hadu da murtala ne na gidan baabah lame sai goggo tace aww shiyasa ka dade? Yace wlhy ya rakani ne na amso magani sai goggo tayi saurin cewa baka ji dadi bane? Yace mata a'ah da sauki ai yanzu kunu nakeso zan sha magani sai goggo tace ai kuwa sai an dama dai dai lokacin da hassai ta ajiye kwanon abincin tace bari zan dama kunun goggo ai ke baza kiyi baccin ba inji goggo hassai tace ai karatu nakeyi saboda jarabawa ya wuce ya shiga kitchen din ta hura wuta nan take ya daura ruwan tazo ta wuce dakin ta dauko ruwan sanyi ta kawo ya dago kai yace mata kinga ki Hado fura irin ta dazu ki kawo ahankali suka hada ido sai ya kawar da kanshi yaci gaba da cin abinci amma aranshi yana ta tunano yadda idonta yake da yadda take kallonshi goggo ta katseshi tana tambayar shi wai meke damunka sai ya dago kai yace ai na samu sauki yanzu tunda ga magani sai tace toh yace goggo gobe Ina son ayi mun abincin sadaka Idan zaki iya da safe ko kuma idan yarinyar nan ya dawo sai goggo tace ai makaranta zata je kuma jarabawa takeyi sai yace toh shikenan sai ta kawo kunun a kofi tace mey za'a girka ya dago kanshi suka hada ido akaro na biyu yayi jim yace ba makaranta kike zuwa ba tace ai karfe goma zan gama jarabawa sai Inzo gida in girka sai biyu in koma inyi last paper for the day hassai ta fada tana murmushi sai yace toh shikenan shinkafa ne da wake sai naman ragon da za'a soya a ciyar da mutum ashirin da naman rago akan kowane kwanon abinci daya ta amsa da toh ya kuma cewa mey dame ake bukata gobe zan siyo in kawo goggo sai kallon hassai take don mamaki ya kusan kasheta bayan tasan hassai akwai ta da son jiki amma yanzu ita ce take kokarin karbar aikin wahala Hassai ta katse wa goggo tunani alokacin da take fadin shinkafa, wake mangyada, yaji, maggi sai gishiri da su kayan miya saboda tafasa naman da Kuma enough oil for frying the meat goggo ta kuma cewa ashe dai ta iya turancin da ban taba jin tana wannan turancin ba ashe dai ba hasarar kudina nakeyi ba. Yace ba damuwa za'a kawo komai gobe in sha Allah yace goggo akwai fridge dinki kuwa tace ai fridge ya lalace kankara nake siyo wa insa akula ai sama'ila yace toh shikenan ya dauki waya yayi kira nan take mansur ya dauka suka gaisa yace kana kano ne? Yace eh wlhy cewan mansur yace DanAllah Ina son asiyo mun freezer babba da fridge mai gida biyu kaje shago sai ka bani shuaibu muyi magana ya baka kudi sai a aikomun anan gwarzo zan karba a babbar kasuwar gwarzo gobe in Sha Allah suka gama magana sukayi sai da safe sai alokacin yake cema goggo dazu yayi magana da masu Gini anan fagge gobe zasu zo su auna su fara gyara saboda aure zaiyi nan take farin ciki ya mamaye goggo tace madallah yace baza ki tambayeni a ina na samo mata ba tace ai ko a Ina ne bazan damu ba saboda Ina maka addu'a kullum yayi murmushi yace wlhy Baabah lame ce tace ya bani mata wata marainiya yana murmushi goggo tace madallah wannan abu yayi mun dadi Hassai na daga ciki tana karatu nan take taji komai ya tsaya mata tace wlhy ko mata hamsin zakayi ni sai na aureka don bazan yadda ba
Kamar da wasa masu gini suka zo suka awna koina yace su koma daya bangaren da ba kowa don za'a fara aiki washe gari abu na kudi washe gari aka fara aikin gadan gadan a hakan ya koma wurin m khalifa yace mishi ya koma bakin kasuwancin shi amma kada ya yadda ya nuna mata ya shirya da mahaifiyarshi ko kuma zancen auren shi ko kuma ya warke ya daure ya karbi shawarwarinsa yayi shirin komawa kano bayan yaje wurin baabah lame akan maganar matar data ce ta bashi ashe 'yar kanwarta ce wadda ke aure a Gombe da mijin kanwarta ya rasu sai ta dauko ta riko yanzu shekararta daya da wata biyu anan gwarzo baabah lame tace ya jirata a soro zata fito ahankali take tafiya har tayi sallama shikuma ya amsa ya dago kai yaga wata kyakkyawa mai dogon hanci gata fara tas tasaka hijabi amma yanayin jikinta duk ya bayyana ya kamshi turare ta sunkuyar da kanta kamar wasa yaji kafarsa baza ta daukeshi ba saboda kyanta da shaukin sonta da yaji ya debe shi nan take cikin natsuwa ya zauna akan ginin kasan dake gefen dakin soro suka gaisa yayi mata bayanin kanshi da kuma maganar aure Idan ta yarda dashi da sauransu shi zai aiki magabatanshi suje Gombe suga iyayenta suka kudin aure da sadaki a basu lokacin daurin aure ya hada da cewan baya bukatar tazo da komai shi zai saka kayan daki kuma zaiyi mata kaya tace mishi ta amince saboda tun data daura idonta akan shi taji ya kwanta mata
Sun gama daidaitawa yace zai koma kano ayi kokarin Sanar da magabatanta sannan yabar ma goggo sako baffa yayan mahaifin sama'ila su shirya suje su kai kudin aure da saka rana
YOU ARE READING
Kyautar Allah(Allah's Gift)
Romance#TrueLifeStory #Halfcaste #love #lovestory #Hausa #hausanovel #yemani #nigerian #marriage #princess #Royalty #yemaniprincess