👨🏻🦯MAKAHO NE👨🏻🦯
*Na*
*RASHIDA USMAN*
*{RASHMA}*بسم الله الرحمن الرحيم
*Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Ƙai.*
*Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki.*
*Ya Allah ka bani ikon rubuta abinda zai amfar da al'ummar Annabi ka kare ni rubuta abinda zai cutar da su dani gabaki ɗaya.*
*Dedicated to:*
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION wannan shafin naku ne ina alfahari da ku Allah ya ƙara haɗa kawunamu baki ɗaya ina muku fatan alkhairi.*
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.comhttps://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
Free Page1&2
Kallon tulin kwanukan wanke_wanke dake gaban ta ta yi tanajin wani iri a cikin ranta tunani da ya zame mata jiki ta fara batayi nisa a cikin tunanin ba ta ji muryar mama na faɗin "dan ubanki bazakiyi ki gama ba ga shara da mofing ga yiwa yara wanka wallahi kika sa yarana suka makara sai na halaka ki a cikin gidan nan shegiya munafuka."
Daga haka ta juya ta fice ita kuma cikin kuka ta ci gaba da wanke_wanken cikin lokaci ƙalilan ta ƙara sa wanke_wanke cikin babban falon ta shiga daga nan ta haura sama ɗakin yaran ta shiga kwance ta same su suna ta sharara bacci har babbar wacce kusan sa'anin da ita amma duk ta makara sai taci ubanta gashi ko tashin ta tazo yi da faɗa take tashi wata rana ma harda duka duk da sa'ani ne amma dan dole take ce mata aunty Zarah numfashi ta sauke ta fara tashin ta "aunty *Zarah* ki tashi shida da rabi har ta yi."
"Wallahi *Jiddah* idan na tashi saina zubar maki da haƙora."
Baya ta matsa ta nufi gadon *Walid* da *Walida* bata ma tsaya tashin su ba sungumar ɗaya kawai ta yi sai ban ɗaki kaya take cire masa amma yana langaɓewa saida yaji saukar ruwa a jikin sa sannan ya buɗe idanu tana gama masa ta ɗauko *Walida* itama yanda ta yiwa *Walid* haka ta yi mata bata sake bi ta kan *Zarah* ba ta ci gaba da shirya su saida ta gama saka musu kaya tukunna ta kaisu suka karya sannan ta kaisu ɗakin mama shara ta fara tanayi tana kallon a gogo saboda kar ta makara sai bakwai da minti hamsin sannan ta gama (7:50) da sauri ta shige ɗakin ta dake ƙasa ta yi wanka ta zura kayan makarantar wanda ya kasance kalar na zara ne gajeren siket sai farar riga da ɗan guntun hijabi a bakin get ta haɗu da Musa driver ya dawo daga kai su Zarah girgiza kai ya yi dan yarinyar ba ƙaramin tausayi take basa ba "kiyi sauri na saukeki karki makara."
Da gudu ta ƙara sa ta buɗe gaban motar ta shiga tafiyar minti goma ta kaisu makarantar su mai suna Dependable international School get man ɗin su ta gaida da fara'a ya amsa mata sannan ta shiga tana shiga ana gama asambili sama ta haura dan hawa na uku ajin su yake dan SS1 take ajin su ɗaya da *Zarah* hakan ya saka take shan tsangwama a gurin ta hakan ya saka principal raba masu aji ya maida *Jiddah* SS1 rose hakan ya saka ta sami sauƙi a makaranta aunty ɗinsu ta gaida sannan ta saka jakarta da lunchbox ɗin ta a cikin loka sannan ta cire litattafan ta ƙarfe uku aka tashe su waje ta fito tana kallon wajen makarantar motar su ta hango tana zuwa hakan ya saka ta saurin saukowa ƙasa ta sami Musa suna jiran *Zarah* dan tun ƙarfe ɗaya aka zo aka ɗauki su *Walida* saida ta gama ɓata masu lokaci sannan ta fito tana yanga hijabin ta a hannu ta buɗe bayan mota ta shiga ta hakimce jefi_jefi suke fira ita da Musa wani dogon tsuki *Zarah* ta ja "ni kun dameni da baƙi surutu ku."