👨🏻🦯 MAKAHO NE👨🏻🦯
*Na*
*_Rashida Usman_*
*_{Rashma}_*بسم الله الرحمن الرحيم
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.comhttps://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
*Free page*
*11&12*
Murmushi ya yi ya ce "sai in ke kika gaya musu ni na biya miki nifa ganin ki nakeyi kamar ƙanwata juyawa ta yi ta koma ciki shi kuma ya shiga ɗakin yana nan zaune sai ga Mudassir ya shigo da kayan sa "ya dai ka zauna kayi shiru?"
Numfashi ya sauke sannan ya ce "yariyar tana cikin damuwa duk yanda aka gaya min ta fi da haka wai a ce baza'a biya mata kuɗin makaranta ba amma an iya bawa wata taje ta kashe a banza ina so gobe kaje ka biya mata kuɗin makaranta."
"Ai indai mutanen mu ne kaɗan ka gani."
A nan suka ci gaba da fira saida sukayi sallar isha'i sannan Mudassir ya tafi haka Zaid ya kwana juyi dan yana jin katifar ta yi ƙasa kuma ta masa tauri da ƙyar ya ga gari ya waye koda zai fita Masallaci babu wanda ya buɗe gida bare yasa ran wani ya fita sallar asuba yana dawowa ya fara karatun ƙur'ani saida rana ta fito sannan ya fito waje Musa ya samu yana goge motar gasawa sukayi sannan ya nufi teburin malam Idi ya zauna suna nan zaune sai ga su Zarah sun fito mota suka shiga har Musa ya tada mota sai ga Jiddah ta fito da gudu ta haki tsaya wa Musa ya yi ta shiga take Zarah ta fara bala'i "Musa ban hanaka idan nashiga mota ka tada ba kar ka tsaya ba."
Cikin ƙasƙanda kai ya ce "Allah baki haƙuri Hajiya ƙarama naga bamu fita ba."
"Bari nadawo sai ka bar gidan nan tunda bana ubanka bane ke kuma shegiya mai idanu kamar na mujiya fita daga motar nan tunda bata uwar ki bace."
Kallon ta Jiddah ke yi idanun ta sun ciko da hawaye ta buɗe murfin motar ta fita duk abinda sukeyi Zaid najin su kuma yana gani buɗe musu get malam Idi ya yi suka fice ta ƙaramar ƙofa ta fita tana share hawaye tashi Zaid ya yi yana dogara sandar sa "Hajiya inzo na taka miki?"
Taji muryar Zaid "ya Zaid ina kwana."
"Lafiya lau ƙanwata kawo jakar na riƙe miki." "A'a yaya ka koma kaga idan ka yi nisa bazaka iya komawa ba."
"Waya gaya miki bazan iya komawa ba ai muna gani da zuciyar mu ba wai sai idanu ba."
"Me yasa idan Zarah ta gaya miki magana baki ramawa?"
"Baki mai yaya banason tashin hankali da a taɓa lafiya ta ne shiyasa nake yin shiru idan ta gaya min magana."
"Ai gani yanzu babu wanda ya isa ya taɓa ki zan saka sandana na make mutum."
Murmushi ta yi haka kawai taji Zaid yana burge ta dan yanada saurin sabo Sun kusa fita layin suka ji horn waigowa sukayi a tare murmushi Jiddah ta yi ta ce "uncle dogo."
Harar ta ya yi ya ce "kinsan Allah duk mr etodo ya san ina ɗauko ki inaga sai an kore ni."
"Uncle dogo kayi tafiyar ka zan tafi a ƙafa kadaina tsayawa ɗaukata tunda ban biya kuɗin bus ba."