👨🏻🦯 MAKAHO NE👨🏻🦯
*Na*
*_Rashida Usman_*
*_{Rashma}_*بسم الله الرحمن الرحيم
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.comhttps://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
*Free page*
*13&14*
"Yawwa Mama namanta bangaya me ki ba Fahad zeyi birthday kuma kinga gidan su gidan manya mutane ne to bansan me zan basa ba."
Murmushi Mama ta yi ta ce "wai nikam mezai hana kiyi masa magana ya turo ayi maganar auren ku sai a haɗa ayi tare da na waccen shashar."
Kwaɓe fuska Zarah ta yi ta ce "haba Mama ya za'a haɗa auren mu da ita karki manta daraja ta da nata ba ɗaya ba."
Murmushi mama ta yi tace "abinda ya saka nace a haɗa saboda kinga mutane sun taru dan nasan abokan Alhaji har na ƙasashen waje zasu zo da abokaina masu ji da kansu kema ga ƴan makarantar ku to anan zamu ƙasanƙantar da ita idan suka je gidan ki jere sannan sukaje nata kinga ko a nan ansan ke ba sa'ar ta bace kuma zamuyi shagali kinga kuma shi wance MAKAHO yana neman abinda zasu ci ina zeyi wani shagali."
Dariya Zarah ta yi tana wani fari da idanu "Mama har kunsa naji ina son bikin nan yazo kusa dan dai nidai ba ƙaramin shagali za'a sha ba."
Haka suka ci gaba da tattaunawa akan bikin batare da sun tabbatar da za'ayi bikin ba Fahad ɗan wani me kuɗi ne dake cikin garin Abuja dan ko motar da yake hawa ba ƙarama bace kuma yana sake ma Zarah kuɗi bana wasa ba shiyasa duk ta ruɗe batada masoyi sai Fahad wannan kenan.
Zaune take tana wasa da magen ta da take ɓoyewa a tsohon kitchen ɗin su dan idan aka ganta to ba makawa kashe ta zasuyi shiyasa take ɓoye ta wasa takeyi da ita tana bata labari kamar tana fira da mutum "ƴar fara kinsan wani abu?"
Ɗagata ta yi ta ɗora akan cibiyoyin ta ta ce "su yaya Umar sunce sun kusa dawowa kuma sunce idan ya dawo zasu siya min kayan sawa nadaina saka tsofaffi kaya."
Dariya ta yi cike da jindaɗi har gefen kumatun ta suna lotsawa kifin ta ta ɗauka ta fara bata take magen ta fara ci ta jima a gurin sannan ta maida ta gurin da take ɓoye ta sannan ta nufi hanyar cikin gida koda ta shiga Zarah na zaune da ƙawayen ta ruwa ta ɗauka zata fita Zarah ta ce "ke kije kiyi mana samosa."
Bata ce mata komai ba ta juya ta nufi kitchen fulawa ta ɗiba iya yanda ze ishe ta kallon agogo kitchen ɗin ta yi ta yamma ta yi leƙawa ta yi ta gansu inda suke firij ta buɗe ta ɗauko wanda ta riga ta haɗa soyawa kawai za'ayi maida fulawar ta yi sai ta basa shi a faranti ta bashi ƴan mintuna ya saki sannan ta fara soya wa tana kwashe na uku sai ga Zarah ta shigo da taga ta soya da yawa sai kawai ta ɗauki filet ta zuba musu ta fita tana gamawa ta zuba wani a filet ta rufe sannan ta rufe sauran ta fito ko kallon su bata yi ba ta wuce akan wasu kojeru ta zauna ta ajiye filet ɗin gefe baza idanu takeyi taga ta ina ze ɓullo duk yau bata ganshi ba can ta ganshi ya shigo gidan ya ganta amma sai ya yi hanyar ɗakin sa ita dai wani lokaci sai taji kamar ba MAKAHO bane ganin be ma kalli inda take ba ya saka ta miƙewa ta ɗauki filet ta nufi gurin sa yana ganin ta taso ya rage tafiya cikin sauri ta same shi ta ce "Ya Zaid ina kaje duk yau bangan ka ba?"