👨🏻🦯 MAKAHO NE👨🏻🦯
*Na*
*_Rashida Usman_*
*_{Rashma}_*
بسم الله الرحمن الرحيم________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.comhttps://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
*Free page*
*5&6*
Murmushi Mama ta yi itama tana cewa "eh nice."
Kallon mai aikin ta yi tana cewa tana cewa "ki kai ƙanwata ɓangaren da kuka gyara ɗazu sannan ki kai yarona ɓangaren matasan gidan."
Kai ta gyaɗa mata tana mai sauke kanta sannan ta yi gaba suka bita a baya yana kusa da wancen ɓangaren shima ya tsaru sosai saidai baikaira wancen haɗuwa ba falon take kallo tana sauke ajiyar zuciya ɗakuna biyu ne baida bene wannan saɓanin wance a kwai ɗakuna sama jakar ta mai aikin ta karɓa ta kai mata ɗaki sannan ta fito ta koma wancen ɓangaren ta ɗauko mata abinci da ruwa sannan ta fita numfashi ta sauke tana ƙara kallon falon abinci ta buɗe shinkafa da miya ne yaji naman kaji da salat a gefe cin abinci tayi saida ta ƙoshi sannan ta shiga ɗakin da mai aikin ta saka mata kayan ta ɗan ƙaramin gado ta gani sai wardrobe a gefe wanka ta shiga ta yi sannan ta ɗauro alwallah ta gabatar da sallar magariba sai bayan sallar isha'i mai aikin ɗazu tazo kiran ta mayafin ta, ta yafa sannan ta biyo bayan ta har babban falon su na ƙasa sannan ta nuna mata sama ta ce "ki je suna falon sama Bama hawa idan ba shara zamuyi ba."
Daga haka ta juya ta fita cike da sanyi jiki ta haura sama a nan ta sami *Abdallah* da wasu samari uku sai ƴan mata biyu cike da girmamawa suka gaida ta da fara'a ta amsa musu sannan ta gaida Alhaji Bashir shima da fara'a ya amsa sannan ya kalli Abdallah ya ce "munriga mungama magana da Alhaji Dauda makaranta zaka koma."
Ɗago kai ya yi ya kalli Alhaji Bashir ya ce "Abba nidai gaskiya kasuwanci nake so nayi."
Murmushi Alhaji Bashir ya yi sannan ya ce "kar ka damu idan ka dawo makaranta sai ka riƙa zuwa kasuwa."
Godiya ya yi masa sosai shida mama sannan suka masu sallama suka fita bin mamar tasa ya yi ɓangaren sa suka ci gaba da fira sun jima suna fira sannan ya mata saida safe ya koma ɓangaren su washe gari koda ta tashi duk mutan gidan sun watse har Hajiyar gidan aiki take zuwa abin ya bata mamaki mai gida ya fita matar gidan ma ta fita tana zaune ta mamaki sai ga wata budurwa ta shigo kallon ta tayi rusunawa budurwar ta yi tana gaida ita sannan ta ce "Hajiya nazo na gyara wannan ɓangaren ne."
Murmushi ta yi sannan ta ce "ƴata ya sunan ki?"
"Sunana lubuna." "To Lubuna kije zan gyara da kaina."
Kanta ta sauke a ƙasa sannan ta ce "kimin rai aunty Ramlat ta sani zata kore i."
Da mamaki ta kalle ta dan dai ita tasan ba sunan Hajiyar gidan kenan ba a yanda kawu Dauda ya gaya mata sunan matar Farida katse tunanin ta yi ta hanyar ce mata "wacece ita Ramlat ɗin?"
Babbar ƴar gidan ce kowa tsoron ta yakeyi a gidan har ƙanen ta Hajiya ce kawai take mata faɗa dan ko yayunta basa taka mata burki."
Jinjina kai ta yi sannan ta ce "jekiyi aikin ki."