official trailer

26 1 0
                                    

*AL'UMMATA!*
*AL'UMMATA!!*
*AL'UMMATA!!!*
_OFFICIAL TRAILER_

Kirkirarran labari ne daya faru a shekara ta 1900 akan SIR JAMES THOMAS shahararran dan kasuwa da bai mutuwa (immortal) wanda yayi shekara sama da dari 700 ba tare daya mutu ba!,
amma an sanar dashi makamin mutuwarsa shine idan har ya zalunci wasu al'umma basu barshi ba saida suka rama komai kankantar zaluncin daya yayi musu

Shahararran dan kasuwa ne da ba kowa yake yiwa aiki ba sai mashahuran Attajirai da suka yi fice a fadin duniya a karnin arzikinsu , mafi akasari yafi yiwa yanki, kabila, Kasa, ko wata nahiya dake duniya aikin nasa ,
Yana amfani da karfin mulkin kasarsa ta birtaniya wajen gudanar da kasuwancinsa ba tare da kasar tasa ta sani ba

A cikin wannan hali ne wani shahararran dan kasuwa dake daular RUSSIA ya bashi kwangilar samu masa bayi bakaken fata mata da maza guda dubu_dubu kowannensu domin su aiwatar masa da wani sihirtaccen aiki

Bisa Binciken da yayi akan wannan kwangila ya gano cewar babu inda zai samu bakaken fatar da zasu biya masa bukatar abinda ake nema sai a yammacin nahiyar bakaken fata kasar NIGER (nigeria) daga arewancin Niger da koma kudancin Niger

Ya fara sauka a daular NIGER (wacca aka fi sani da cibiyar saida bayi)
Karkashin mulkin sarki KPADIA DIMIEN ya fada masa bukatarsa na son bayi dari biyar maza dari biyar mata bisa kyakkyawar alakar kasuwanci dake tsakanin birtaniya da daular niger ya sanya sarki kpadia dimien biya masa bukata ba tare da wani bincike ba (a lokacin kasar birtaniya tana da karfin iko a yawancin kasashen duniya)

daular SOKOTO itace bangare na biyu da sir james thomas ya sauka domin karbar bayi kamar yanda yayi a daular niger wacca ke karkashin mulkin adalin sarki , SARKI HAMZA SULAIMANU ,
An samu akasin rashin biya masa wannan bukata tasa ,bayan tsananta zurzurfan bincike daga karshe daular sokoto ta gano sir james thomas yayiwa masarautar birtaniya karya ta hanyar amfani da sunanta domin aiwatar da hukunci (wanda yin hakan hukunci ne mafi tsauri ga wanda ya aikata)

Bisa wannan laifi da suka yi masa ya sanya shi daukar fansa ta hanyar amfani da maci amanar wazirin daular sakamakon yi masa alkawari da zai kashe sarki hamza sulaimanu ya dawo masa da mulkinsa hannunsa (wanda yakamata ace shine sarki, sakamakon rashin cancanta aka hanashi)

A shekara ta 1903 A hanyar sarki hamza sulaimanu shida mutanansa ta tafiya hajji kasar SAUDI ARABIA ;sir james thomas yayiwa sarki hamza sulaimanu MAMAYAR BAZATO ,
saidai kash! Anyi kare jini biri jini an kashe kowa a wajen idan ka dauke sir james thomas daya kwanta jinya sai bayan shekara 1100 ya tashi

Bayan shekara 1100 aka sake wasu mutane masu suna , kama, halayya ta duk mutanan da suka mutu a baya a wannan mamayar bazato da sir james thomas ya kawowa sarki hamza sulaimanu sannan suke da buri da manufa irinta mutanan baya


YA KUKE GANIN ABUN ZAI KASANCE?, babu amsa ga wanda bai karanta wannan littafin ba!,
Tuna da sunan
*AL'UMMATA*
15 FREE PAGES ,bayan haka sai kiyi_kayi subscribe 200 pages 2 a sati , ko ka zama daga cikin mutane cikin mutane masu matukar mahimmanci ta hanyar biyan 400 pages 4 kowanne sati, domin kayi subscribe saika tuntubi wannan number 09033702615

Ku biyoni kusha labari taku ce dai
Fatima Abdullahi Ibrahim
(Fatin mama)

Al'ummata (akan kasata)Where stories live. Discover now