the first encounter 04

10 0 0
                                    

  
💖💖💖💖💖💖💖💖
*AL'UMMATA*
_(akan kasata!)_
💖💖💖💖💖💖💖💖

*FATIN MAMA*

  *PAGE* 0️⃣4️⃣

     Tafiya suke sannu a hankali kamar masu tsoron taka kasar , sir JT ne a gaba yayinda sir lious mattew shida olgey suke take mishi baya kansu bisa kasa lokaci_lokaci suna dan taba hira tsakanin su wacca baifi a kirge su ba

  Sun yi tafiya mai nisa sosai wanda har saida ya zamto basu gano ginin gidan kwata_kwata saidai benensa shima ba sosai ba alamar sunyi nisa da gidan ba kadan duk da haka suna cikin wannan lambun na sir jt wanda yanzu za'a kira shi da daji

   Wata dabara ce ta faduwa sir lious mattew da dansa olgey tashi daya Ganin sunyi nesa da gidan

   Kallon dan nasa sir lious mattew yayi wanda shima ke kallonsa da alamar koda shi bai yi masa magana ba shi yana shirin yi masa , yayinda duk abinda suke sir JT yana ankare da su duk da yana gaba  dasu kadan ba lalle suyi tunanin yana ankare da abinda suke ba

  Cikin wata irin karamar murya wacca iya tsakanin su ne kawai zasu iya ji sir lious mattew yacewa dan sa
  "Ya dana !,
tabbas gautam yana tare damu"

    Dariya mahaifin nasa yayi ta farin ciki yana kara siranta murya tare da fadin
  "Godiya ga gautam!,
wannan itace damar mu ya dana"

Wani irin kazamin murmushi sir JT ya saki na gefen baki jin abinda sir lious mattew ya fada yana fadin a zuciyarsa
  "Da alamar ka kusa ka canja abun bauta indai abinda zaka yi yanzu shi ne sa'arka da abun naka ya baka!"

   Cikin farin ciki olgey ya amsawa mahaifin nasa da fadin
  "Abinda nike son fada kenan ya mahaifina!,
godiya ga gautam!"

  "Babu dadewa zaku tsinewa abun bautar taku!"
#sir JT ya saki wani mugun murmushi daya fi na farko bayan ya gama ayyana hakan yana mai cigaba da tafiyarsa ba tare da yayi ko waiwaye ba

  
   Yayinda sir lious mattew da dansa olgey basu gushe ba suna maganganu akan abinda suke ganin shine mafita a garesu ba har saida suka tsara yanda zasu yiwa sir JT duka ta yanda zai dawo karkashin umarnin su kamar yanda suke a karkashin nasa umarnin yanzu,
  Karshen tika_tikin tik! , tunanin gaje dukiyarsa suke koma abinda yake mafi sauki gare su shine su kashe shi kawai su kwashi dukiya idan yaso sai su nemi wani dan kasuwar yayi musu aikin da suke bukata

   Wata yar dariya sir JT ya saki  bayan ya gama jin gaba daya tsarin su akansa ,
wani irin sauti ya saki kamar tsaka "tsk_tsk_tsk_tsk!!!" Wanda ya sanya hankalin sir lious mattew da dansa olgey ya dawo gareshi kowannensu cike da alfahari mai tattare da jin kan samun nasara , suna yi masa wani kallo na
  "Meke ga wannan gawa kusa da ramin?"

   Ba tare da sir jT ya damu ba ya cigaba da tafiyarsa yana fadin
  "Idan ka bawa kare abinci yakan yi murna da farin cikin samun kulawar ubangidansa , amma idan ka bawa mage abinci takan ji isa da girman kai sun lullubeta ta dinga tunanin itace ubangidan "

  A wani irin hasale sir lious mattew yace
"Me kake son fada kai wannan botoramin?"

   Dan dakatawa sir jt yayi daga tafiyar da yake da alamar yanda sir lious mattew yayi magana tabbas abun babba ne
"Daga " shugabana" "ubangidana" "ranka ya dade" ya akai nayi saurin sakkowa izuwa wannan suna na "botorami" da wuri haka?"

  Cike da gatsali olgey ya cigaba watsawa sir JT mummunan kallo tamkar idonsa zai fado kasa don bacin rai yana fadin
  "Ya mahaifina ina ga zuwa anjima wannan botoramin zai ce zai koya mana ilimi akan ladabi da biyayya ne!"

  Jijjiga kai sir lious mattew yayi cike da gamsuwa mai tattare da tsabar izgili yana fadin
  "Haka nike tunani , amma baka ganin lokaci ya kure masa?"

Al'ummata (akan kasata)Where stories live. Discover now