BABI NA 1

77 6 5
                                    

💓💓 *_RAYUWAR INDO AISHA_* 💓💓

*_CIGABAN LITTAFIN INDO AISHA_*

*_LITTAFIN_*
*_NAFISAT ALIYU FUNTUA_*
((Ummuhfadima))

*_Bissimillahirrahanirrahim ina miƙa dubun godiyata ga Allah ubangijin talikai da yabani damar cigaba da wannan littafin na INDO AISHA bayan dogon lokaci, ina roƙon Allah da yabani ikon rubuta abindazai amfani al'umma baki ɗaya ya Allah ina roƙon gafarar ka akan abinda zan rubuta na kuskure acikin wannan lbr Allah kayafe mana kura kurammu alfarmar annabi muhammadu s,a,w._*

~~Wannan littafin gaba ɗayanshi sadaukarwa ne agareku 5star's Aminai na ƙwarai haziƙan marubuta Mummyn Meenal Marubuciyar *AISHA HUMAIRA* da Ummuh Hameedat Marubuciyar *ZAMAN TAKEWAR AURE* da Mommyn Ilham Marubuciyar *GIDAN MIJINA* da Maman Haidar Marubuciyar *ILLAR ƘASATA* Ummuhfadima nayi muku son so fisabilillahi.~~

PEGE 1~2

My hapness! My hapness!! my hapness!!! Haidar ne keta ƙwallawa Indo kira wanda dawowar shi kenan daga gurin aiki, tsayawa yayi yana jiran ganin ta inda zata fito amma yaji tsit, gabanshine ya faɗi tuna yadda yabar Indo da safe kafin fitar shi office da sauri yayi hanyar ɗakinta kwance ya isketa lilliɓe da bargo tana ta faman rawar sanyi ai da sauri yayi wata sufa zuwa gareta.

Tallafota yayi zuwa jikinshi yana cewa "Humairana lafiya? Meya sameki? Ina keyi miki ciwo?" Gaba ɗaya ya ruɗe bema jira amsarta ba yacicciɓeta gaba ɗayanta yayo falo da ita, jiki na rawa yako ɗakinta ya ɗakko mata hijab ɗinta da yake dama sanye take da dogon riga marar nauyi, a bai baima yasaka mata hijabin sannan yakuma ɗaukarta kamar wata baby yayo waje da ita wanda kota kan Emeka driver bebiba dakanshi yaja motar bayan sakata a seat ɗin baya jan motar yayi da mugun gudu yayi asibiti da ita jikinshi yana rawa tun kafin yakai asibitin yakira babban likitan yake gayamishi yana tafe.

Cikin mintinan da basufi biyar ba ya isa asibitin da ita yana zuwa ya iske nos nos awaje da gadon ɗaukar marar lafiya, amma kota kansu bai bi ba yakuma ɗaukar ajikinshi yayi ciki da ita aguje ko motar be tsaya kullewa ba saide cikin ma aikatan wurin wani yakulle mishi motar bayan yacire key ɗin daga jiki.

Yadda yake aruɗe yana kiran likitan afusace kamar yana filin daga sai yasa hankalin mutane yayo kansu nanfa ƴan ƙananun maganganu yafara tashi irin de ƴan gulmarmu ta mata, likitanne yatare su da sauri ya gwada mishi ɗakin da zai shigar da ita kan gadon ɗakin yakwantar da ita da ƙyar likitocin suka samu yafito waje, saida suka lallaɓa shi sannan saboda dama asibitin tasu ce kowa yasan shi kuma yasan matsayinshi koma wa'inda basu sanshi ganin shi dakaki ajikinshi sunsan babbane sbd kunsan dawowar shi daga aiki kenan ko ɗaki be shiga bare yacire unifom ɗin.

Likitocine suka rufu akan Indo kasan cewar ta ga labaita sosai, sunjima akanta sosai saida sukaga komi yakoma normal harma tayi bacci sannan suka fito, yana ganin doctor Joshua yafito yayo kanshi yana tambayar shi ya matar shi take, murmushi yasakar mishi sannan yace "relax my friend komi yayi normal yanzu ma tana barci ne biyoni office kafin sakamako yafito".

Shide Haidar binshi kawai yayi amma fa saida ya leƙa ya ga farincikin zuciyarshi Indo, kwance ya isketa tana bacci fuskarta yashafa yace "Allah sarki my hapness ubangiji Allah yabaki lafiya" ni Ummuhfadima na amsa mishi da ameen.

RAYUWAR INDO AISHA CIGABAN LITTAFIN INDO AISHAWhere stories live. Discover now