ABDUL JALAL 108

1.2K 27 2
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹

*ABDUL JALAL*

_Story, writing and edited _

By
AISHA HUMAIRA
( _Daddy's girl_)

*PERFECT WRITER'S*
*ASSOCIATION*🌞

(𝕎𝔼 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 𝔹𝕌𝕋 𝕎𝔼'ℝ𝔼 𝔸𝕃𝕎𝔸𝕐𝕊, 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 𝕆𝕌ℝ 𝔹𝔼𝕊𝕋 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ 𝕆𝕌ℝ ℝ𝔼𝔸𝔻𝔼ℝ𝕊💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A*✍️

PART 2
_PAGE 5️⃣4️⃣107

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com
Watpad @Ayshercool7724


_MY FIRST NOVEL _

Gaba daya jikinta yayi sanyi ta tsaya tana kallonsa, juyawa tayi ta koma daki ta barshi a parlourn, se bayan ta tafi yaji gaba daya jikinsa yayi sanyi, yake tambayar kansa meyasa yayi mata shouting? Laifin me tayi masa? Gaba daya se yaji ransa ya baci. Ya tashi ya bi bayanta, amma ya tarar ta rufe kofarta sannan ta kashe futile, haka ya hakura ya koma dakinsa.

Washegari bayan tayi salla, ta shiga kitchen ta hada breakfast, kafin ya tashi har ta kammala abunda zatayi tai ficewar ta.

Naja ce ta shigo gidan ko sallama babu sekace korarriya, Yaya mairo ta kalleta tace "ke meye haka ko sallama babu"?
Dan guntun tsaki Naja tayi tace "wallahi matsiyaciyar yarinyar nan ta cuceni, da yanzu ina Abuja ina hutawa, Amma gashi ba Auren, kuma duk samarin nawa sun gudu ga talauci ya isheni"

Yaya mairo tace "kema ke kika cuci kanki, shaye2 Naja, na miki fada har bansan adadi ba, ga wannan abun kunya da kikayi, ba dan Allah ya rufa asiri ya zube ba da shikenan, kinjamin masifa"

"Amma da ya aureni aida zan dena, wannan bakar shegiyar ta zalunceni ita da Allah makira, kuma itama tayi Aure sun barni a titi"

Yaya mairo tace "Aure kuma, wata aura?"

Naja tace "Agurin daurin Auren aka bawa wannan dan shaye2 sadakarta, Jalal suke ce masa ko Jamilu oho dai"

Sa'ada da tun dazu ke kwance na danna waya ba tace uffan ba se yanzu, ta kalli Naja tace "Ke bana son shirme, da gaske Jalal ta aura"

Cikin tsiwa Naja tace "Bansani ba tunda baki yadda ba meye na son se kin tabattar aikin banza kawai, na tsani inyi magana a karyatani"

"Sorry ba karyataki nayi ba, amma waya gaya miki?"

Cikin kosawa Naja tace "Zancen duniya yana buya ne? A anguwarsu naji, har gidan seda aka kwatanta min, shi aka Aura mata, Ai Allah ya kara, Allah yasa yayi mata dukan da seya kashe ta"

Yaya mairo tace "Ameen dai Naja, Ai Allah ne yasaka miki ya hadata da dai dai ita, yayi ta cin kaniyarta"

Kallonsu kawai Sa'ada take da sun san me Jalila ke nufi a rayuwar Jalal da basuyi wannan maganar ba.

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now