🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 🌹
_ABDUL JALAL (2020)_
_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)
PART 2
_PAGE 2️⃣9️⃣82Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com
_MY FIRST NOVEL _Banza tai masa ta dauke kanta, yakuma kallonta yace
"Gayamin mana"
A fusace tace
"bazan fada ba, meye hadinka da damuwa ta?""Nasan kinajin haushina saboda kuskuren da'aka samu, amma...
" kace kuskure? Ba wannan ne karo na farko daka mareni ba, kace na fiye maka shishshigi, nakuma yi Alkawarin na dena yimaka kaikuma meye naka nayi min shishshigi, dalla matsa kabani guri in wuce" tai maganar tana ƙoƙarin miƙewa
"zan baki guri ki wuce, amma meyasa kika damu dani haka?, kike bani wannan kariyar bansaniba, dukda irin halayena? Kinyi kokarin kareni a lokuta daban2 bansaniba meyasa? Gashi kinsan abubuwa dayawa dani ban saniba, at least kin haska wani bangare a Rayuwata da yakasance me tsananin duhu, nesanta Jeje dani hakika haskene me yawa a rayuwata, bansan ya akayi na yadda da Jeje nafara wannan muguwar rayuwar ba, kawai na tsinci kaina a wani yanayi dani ka dai nasan menakeji, amma meyasa kika temakeni, kike kokarin ganin kin canza akalar Rayuwata?"
yai tambayar yana kara tsareta da ido, itama kallonsa takeyi dan bata san mezatace masa ba, wani uban tsaki taja ta wuce ta gefensa ta fice daga dakin.
A hankali ya koma ya zauna yana tunanin abubuwa da dama, abubuwa dayawa ya dinga tunawa, Jalila tayi Rawar gani a Rayuwarsa, yanzu ya gane abubuwa dayawa da a da sam besan dasu ba.
Itakam guri tasamu tai zamanta taki komawa cikin gidan tanata zancen zuci, karar motar Jawwad ne ya dawo da ita hayyacinta, shida Abba ne ya dakko shi a Airport, da fara'a Jalila ta tashi ta nufi inda suke, Abba yace
"Jalila bakida lafiya ne? Naga kin rame haka" murmushi tayi
"Haba Abba duk wannan kibardanayi kayana sunmin kadan fa"
"Anya kuwa in yadda? Idonki kaman kinyi kuka fa""Abba nikam meze sani kuka yau zanganka? Bacci nayi kawai, kawo jakan in rike maka" tasa hannu ta karbi jakarsa, Jawwad yana ganin dakiyar Jalila daka ganta kasan tana cikin damuwa, amma ta maze tanata kokarin boye damuwar.
Ba karamin murna sukayi ba dawowar Abban nasu, Jalila tasan koba komai zata samu saukin wani Abun,
bayan sallar magariba suka gabatar masa da Abinci yaci, nan suka sake aka shiga hira da Abba, Maama tanata dan dari2 kar Jalila tagaya masa wani abu, dan ta lura tun dazu Abba yake tambayar Jalila koda matsala amma tace ita ba komai. Sekusan goma na dare suka watse suka tafi dakunansu.Ilham tagaji da azabtarwar da Jalal yake mata, yakamata sunemi wata mafitar, tsawon shekarun datayi a gidansu Jalal bataga alamar zasu cinma burinsu ba, Jalal mugun baudadden mutum ne, ga tsabar jaraba da masifa, gashi da rashin yadda, kwanan nan ta lura kaman yakara tsanarta batasan metayi masa ba, ta lura yanzu har uwassa ma yakara fita harkarta, ko cikin gidan baya shigowa, mikewa tayi ta tafi palourn mummy, ta tura kofa bako sallama ta shiga ta samu guri ta zauna
Mummy ta kalleta tace
"Ke lafiya kika shigomin bako sallama meye haka?"
"Mummy yaushe zaki cikamin alkawari na ne?"
"Wanne kenan?"
"Mummy har yanzu banga alamar Yaya Jalal ze yadda ya Aureni ba, lokaci fa kuremin yake ni macece yakamata zuwa yanzu kiyi wani abu akai, ina sonshi, banajin zan iya Auren wani bashiba, kitemaka Mummy dan Allah kiyi wani abu" Ajiyar zuciya Mummy tayi
"Ilham yakikeso inyine? Yaron naan kullum wutar kiyayyata ruruwa take a ransa, kiduba rashin lafiya nayi amma da naje kansa ga yadda ya rikice gana sambatu infita baya son ganina, ya zanyi Ilham? Kaina ya kulle al'amarin Jalal sunfara bani tsoro"

YOU ARE READING
Default Title - ABDUL JALAL (2020)
AcakLabarin wani matashi daya riga ya gurbata rayuwarsa da shaye2 da raina iyayensa, tareda wata matashiyar yarinya 'yar baiwa wadda bata magana biyu, kowa ya shiga gonarta setayi maganinsa wadda ta dage tsayin daka wajen ganin ta sauya akalar Rayuwar A...