Page 8

77 6 0
                                    

*AL'AMARI! Book 1*

*©️Halima H.z*

*P-08*

Few Days later.
Yanda take tafiya zai nuna maka tabbacin a matuƙar gajiye take, tafiya kawai take tana faman yamutsa fuskarta, tana kuma kare hasken ranar daya dallare mata fuska da hannunta.

Jakar dake rataye da ita ma kamar zata faɗi, baki ɗaya Idon Hamma Saddam da hankalinsa sun tattara zuwa gareta, Ji yake inama babu idon mutane da babu abinda zai hana shi fita ya ɗaukota saboda ya sauƙaƙa mata tafiyar.

Sai a sanda ta ƙaraso bakin motar tashi sannan ya lumshe idonsa kaɗan ya kuma buɗesu.
Hannunsa yasa ya buɗe mata murfin side ɗin da take tahowa, sannan ya juya suka shiga gaisawa da ƙawayenta da suka zo tare don gaishe shi.

"to ya karatun naku ana dai yi sosai ko?".
"Hammah Saddam muna karatu sosai kam, yanzu haka ko da aka kafe mana test munyi ƙoƙari, Tasleem ma da bata jima da dawowa ba itace first class".

Cikin nuna jin daɗi yace, "Good haka ake ake so, kuci gaba da dagewa a fito da 9credit kunji".

"promised you Hammah ba zamu baku kunya ba".
"to yayi kyau, duk wadda tayi ƙoƙari zan mata kyauta.
Ku buɗe ku shigo sai mu sauke ku a hanya".

Bayan motar suka buɗe suka shiga suna masa godiya.
Yana tuƙin a hankali kuma ya kan juyo ya kalli Tasleem wadda ta kauda kanta gefe tana ta kallon waje sai faman harhaɗe rai take yi, kuma tunda ta shigo bata yi masa magana ba bacin sallamar da tayi.

Tunaninsa ya tafi akan mai ke damunta, sanin ba shi da masaniyar amsarsa sai ya share har sanda suka sauke ƙawayenta kowacce a gidansu, duk wadda aka sauke zata ce da Tasleem sai gobe amma babu wadda take amsawa baccin ma rufe idonta da tayi kamar mai bacci.

Taɓa jikinta yay yaji sanyi ƙalau babu wani alama na rashin lafiya dake damunta, Tausayinta kamar kullum ya kama shi domin ya san hakan ba zai rasa nasaba da damuwar dake damunta ba, duk da cewar ta masa alƙawarin zata bar saka damuwa ko saboda lafiyarta da kuma Abbu'nta.

"Tasleem".
Ya kira sunanta cikin murya mai ƙarfi.

Buɗe ido tayi ta dubesa kaɗan, shi kuma ya sake ce da ita,
"mai ke damunki? Jikin naki ne? Ko An yi miki wani abun a makaranta ne?".
Ya faɗa cikin nuna kulawa ga ƙanwar tasa.

Ƙura masa ido tayi na ɗan lokaci sai kuma ta fashe da kuka tare da kifa kanta saman cinyarta.
Wuri ya nema yayi parking, ɗago da fuskarta yayi yana dubanta, handkerchf ya sanya yana goge mata hawayen sannan cikin ƙara nuna kulawa yake ta tambayarta abinda ya sata kuka, bata iya ce mishi komai ba har sai da ya ɗan ɓata rai tukunna ta buɗa baki tace da shi,

"Hammah Saddam ba su ba ne".
"suwa kenan?".
"ƴan school ɗinmu mana. Kowa sai nace masa baka da kyau amma sai suyi ta cewa aini makauniya ce amma kam kai kana da kyau tamkar kai kayi kanka, haka idan nace musu kai ba ɗan gayu bane sai suce ai ba haka ba ne kai ɗin mai burgewa ne, kai namiji ne mai class, ka iya gayu, mai ƙamshi da jan hankali, idan mutum ma na kallonka kamar kar ya ɗauke idonsa akanka, yanda kake abin so da burgewa haka komai naka ma".

Numfashi ya sauke gami da ɗan sosa girarsa yana mai ware idanuwansa yana dubanta, a hankali ya furta, "to miye abin damuwa a ciki?".

Sai a lokacin ta samu damar buɗe idonta, wanda ta rufe su tun lokacin data fara masa bayanin a cikin tsiwa-tsiwa.
Rau-rau tayi da idanuwan nata ta fuskance shi sannan tace,

"to ai bana son hakan, bana so kowa ya ganka da dukkan waɗannan abubuwan, bana so kowacce mace taji tana sonka ko kuma wani abu naka, ni nafi so ma mace taji ta tsane ka bata ma son ko ganinka.
Ni kaɗai da rabin raina nake so mu dinga ganinka da wannan, rabin raina kawai nake so ta soka fiye da yanda nake sonka, kuma kaima ita kawai nake so ka dinga kalla da dukkan soyayyarka".

Ɗan rausayar da kai tayi sannan ta cigaba da cewa, "Hammah Saddam ka tuna abinda Ammi tace kamin ta rasu?".
Tayi maganar tana ƙoƙarin maida hawayenta.

"Ammi tace kai namu ne kuma muma naka ne kai da Hamma Lamiɗo.
Hammah Saddam na roƙeka ka daina bari kowacce mace tana kallonka da jin burgewa, karka kuma barin kowacce mace ta kuma cewa ina sonka Saddam. Na rantse maka sam bana jin daɗin hakan, ina taya Rabin raina kishinka".

"shikenan abinda kike so?".

Ɗaga masa kai tayi alamar ehh tare da kuma cewa,
"kuma ko ƴan biki ma da suka fara taruwa ka daina bari suna ganinka, waɗannan ƴan matan masu baki kamar zumɓoto kawai sun zo ne saboda kai, ni nasan ba biki ba ne ya kawosu, saboda duk lokacin da nazo wucewa sai naji suna magana a kanka.
To Na rantse maka idan na ƙara jin wata yarinya tace ƙala a kanka, to saina kulle ka a ɗaki ba zan buɗe ka ba har sai an gama biki an watse, ɗaurin aure kawai zan barka kaje, shi ma kana dawowa zan kuma kulle ka".

*SHARE.*

AL'AMARI! Completed.Where stories live. Discover now