Page 11

103 5 0
                                    

*AL'AMARI! Book 1*

*©️Halima H.z*

*P-11*

"ummm.... yanzu dai ku tashi mu fita kan hidiman bikinnan, sarai kun san tsohuwar gidannan ta fara sanya mana ido, nema take ta fara zarginmu, musamman ni da nake zuwa yanzu akai-akai, kullum naje wurinta maganar ta ɗaya na fita a harkar ku halinku ba mai kyau ba ne, ita duk cikin sirikanta da kune ba tayi dace ba, bata san cewar duk kanwar ja bace".

Suka sheƙe da dariya suna tafawa, Inna Zara dake maganar taci gaba da cewa,

"Allah kuwa, ita fa gani take kallon uwa nake mata, bata san tun ina yarinya ni ba mai ƙaunar ta bace, kawai dai tana cin darajar sauran ƴan'uwana da suke girmama ta. Amma da ita da waɗannan ƴaƴan nata ji nake tamkar na sheƙe ƴan banza a lokaci ɗaya, musamman idan naga yanda Allah ke daɗa ɗaukaka su".

Mami ta ɗan ɓata rai tace, "saboda rashin mutunci harda mijin nawa kike haɗawa".

"maida wuƙar mutuniyar, ai ina sara ina duban bakin gatari ne, tayan zan haɗa da Aminullah bayan ina tare da uwar gidansa".

Duk maganganunsu a kunnen Anty wadda ke ƙoƙarin shigowa, taji suna wannan zance hakan yasa ta tsaya.

Tabbas idan fahimtarta tayi dai-dai to fa bayan kulawa har da so a take-taken Saddam akan Tasleem domin tana lure da shi tun kamin yaje yay wannan dawowar, ga yanzu ma data ke ganin alaƙar hakan na ƙara girma.

to amma kuma gashi waɗannan annamiman matan na wata gagarumar magana mai cike da surƙulle da suka ƙulla a cikin makircinsu, lallai tana zargin Tasleem itace suka musanya a haihuwar Mama data yi wadda aka ce an shigo asibitin anyi satar jarirai cikin dare, kuma ranar ne itama marigayiya Ramlatu ta haihu, sannan wani abu daya faru a wannan dare ya matuƙar ɗaure mata kai, itace a wajen Ramlatu kuma jaririnta namiji ne ita kuma Aisha ta haifi mace, tayi matuƙar mamakin daga baya da taga jaririn Ramlatu ya koma mace na Aisha kuma babu.

_innalillahi wa'innah ilaihi raji'un, ya zama min dole na yiwa tufkar hanci tun kan a kai ga aikata kwaɓa, domin babu aure tsakanin Saddam da Tasleem, su kuma waɗannan azzaluman mutanen ba ruwansu da aikata saɓon Allah muddin buƙatarsu zata biya. Amma shin ta ina zan fara? Duk inda naje da wanna zance za'ai min kallon mahaukaciya ne. Ya Rabb ka kawon mafita._

Zancen zucin da Anty keyi kenan, tana jin motsin fitowansu tai saurin barin wajen.

Jikinta duk ya ɗau kyarma sai kace wadda aka kama da laifi, domin yanzu a tsorace take da al'amuransu kam, rannan taji suna batun kashe Abbu, yau kuma ga wata badaƙalar ta daban.

Cikin ɗaki ta tarar da Manar na shiryawa, kasancewar lunching za'ai ba dinner ba, Yaya Babba yace a soke wannan taron daren, idan ba zasu yi da rana tsaka ba ido na ganin ido to fa sai dai su haƙura.

"ke daɗi na dake kin fiya nawar jaraba, tun fa ɗazu dana fita na barki nan kina faman Kwalɓace-kwalɓace a fuska amma har yanzu kin gagara gamawa".

Tai murmushi tana faɗin, "Anty ai na kusa gamawa, ɗauri kawai ya ragen, kuma sai na jira Tasleem tazo tayi min".

"to dai ki hanzarta kar a tafi a barki".
Anty ta nufi wadrobe tana zuba kayan Manar data gama gogewa a ɗazun.
Tana mai ci gaba da ce mata,

"don Allah idan kunje wurin party'n nan ki kula da kanki, mace ta kama kanta shine mutuncinta, kina tare da ƴan'uwanki amma bance ki biyewa shirmensu ba kin sansu da maza, ba ruwanki da shashanci, ba ruwanki da cakuɗewa wuri ɗaya da maza, ban hana ki rawa ba amma ayi wadda ta dace, wadda bata saɓa addinin musulunci ba, ki kama mutuncinki, Kin san dai yanda rayuwar yanzu take, ka kafa ka tsare ka kula ma ya aka ƙare bare kuma kayi sake, shi namiji idan ya cuce ki ya gama da rayuwarki, a banza ya tafi ya barki da zubar hawaye. Idan kika tsare mutuncin kanki sai shima Allah ya tsareki, kullum abinda nake sake faɗa miki kenan. Ban isa na raba ki da ƴan'uwanki ba amma ni dai ki taimake ni karki bani kunya a rayuwa, ki sani idan ni bana ganinki a duk abinda ki kai to Allah yana kallonki, kuma akwai ranar tsayuwa, ranar tonan silili, ranar da duk abinda mutum ya aikata zai gani kuma kowa ma ya gani.... Allah ya tsare min ke yay miki albarka da sauran ƴaƴan musulmi ma gaba ɗaya".

AL'AMARI! Completed.Where stories live. Discover now