Page 27

77 6 0
                                    

*AL'AMARI! Book 1*

©️Halima H.z*

*P-27*
'''On Behalf Of Every Girl Child.'''
      *SAY NO TO RAPE.*

Meerah tunda ta shiga ɗaki ta kifa kai da gwiwa tana ruzgar kuka kamar ranta zai fita, duk saita rasa mai ke yi mata daɗi a duniyar nan.

Tana wannan hali ne Tasleem ta shigo, kana kallonta zaga ga fusata a tare da ita.

Kan Meerah ta tsaya tana faɗin, "why the crying Adda? you thank God abunda kike so ya kasance, you should be happy since you have humiliate our father in front of the people da basa sonmu".

Meerah ta ɗago da idanuwanta jawur ta dubeta, ta kamo hannunta ta zaunar da ita gefe guda, kallon Tasleem take da wata tsantsar ƙauna gami da tausayi, yayin da Tasleem ke mata kallo mai cike da jin haushi.

Ta matse hannun Tasleem cikin nata a cikin damuwa sosai, ta haɗe leɓen ƙasa da sama ta furta, "Tasleem ki fahimce ni...".

Tasleem ta dakatar da maganar ta, "in fahimceki da mene Adda koma nace Meerah? Kina tunanin har akwai wani bayani da za kiyi min na saurareki na gamsu dake, To bari kiji, da kika ganni nan ina jin ɗaci da takaicin ki kasancewar Yaya a wurina".

"rabin raina ni kike kira da sunan Meerah? Ni kike cewa dama ban kasance Yayarki ba".

"to ya sunan naki yake in ba Meerah ba, kinma ci darajar mai daraja ne sunan Ammi kika ci da kinji yanda baki na ya iya rangaɗa asalin sunanki na yanka, ke har kyaji haushi ma don na kiraki da ainihin sunanki, nayi dana sanin kasancewar ki ƴar'uwa. Nan ɗazu cikin hargowa kika gama abaton sunan Mahaifinmu... Mtswwww".

Tana faɗa ta ƙwace hannunta a nata ta miƙe, bama zata iya cigaba da zama a gabanta ba tana kallonta tana ci gaba da mata magana, fita tayi a ɗakin tare da buga mata ƙofa bummm.

Ɗakin Abbu ta wuce, inda taje ta tarar da shi a kwance an ɗaura masa drip, ga uban magungunan hawan jini kusa da shi.
Tana kuka ta ƙarasa gare shi tare da kifa kanta saman ƙirjinsa. Daren ranar haka suka kwana akansa, shi yana musu wasiyya su kuma suna kuka, yayin da Mommy da Tasleem tamkar suyiwa Meerah me.

*HIGH COURT OF JUSTICE, YOLA, ADAMAWA STATE, 11:00am.*

Babbar kotun adalci kenan dake garin adamawa, cike take maƙil da dubban mutane wanda suka zo domin sauraron shari'a.
Ta ko'ina hayaniya ce ke tashi, Kana duban kujerun farko ba kowa bane suke zaune face wairo's family, kowannen su jugum-jugum, damuwar su baya wuce rashin sanin akan mene ake wannan ƙarar ta Abbu.

Isowan Alƙali hayaniya ta ɗauke, wajen yay shiru, ya zauna a saman kujerarsa yana fuskantar kowa, gefen hagu da shi mutum biyu ne wanda ake ƙara ne tsaye cikin kanta, Alhaji Isma'il Wairo da kuma Abdallah Adam Wairo, a yayin da ɗayan gefen damansa wacce ke ƙara ce a tsaye itama, hijab ne sanye jikinta, kanta sunke a ƙasa tana hawaye, Meerah Wairo kenan.

Bayan dai-daituwan komi Alƙali ya buɗe baki yace da wadda take ƙara, "ko zaki iya maimata mana dalilin daya sa kike ƙara?".

"ina ƙarar mutum biyu ne a bisa babban zunubin da suka aikata, wanda bai kamaci ace an barsu suna rayuwa ba. Abdallah shine wanda yay ma ƙanwata fyaɗe ina roƙon wannan kotu mai gaskiya da adalci data zartar da hukunci mai tsaurin gaske akan wannan sheɗanin bawa, tayi masa hukuncin da gobe ko dabba ba zai yi sha'awa ba, tayi masa hukuncin da zai zama izina ga ƴan bayansa".

Sai kuma ta fashe da kuka tana ci gaba da cewa, "Isma'il shine mahaifina, mutumin da akaf duniya na tsana, mutumin da nake so ya walaƙanta a duniya ya tozarta, Allah ya la'ance shi, duniya da jama'ar cikinta su tsine masa suyi Ala wadai da halinsa".

Wannan maganganun nata duk sai da suka daki zuƙatan jama'ar wurin, shirun da tayi tana kuka yasa Alƙali ya katse ta da faɗin, "nan ba wurin kuka bane. Muna sauraronki, ko duk akan mene ya janyo hakan?".

AL'AMARI! Completed.Where stories live. Discover now