1

553 37 8
                                    

Tsugunne take daga can gefen bango ta makure ta yadda idan ba mutum ya biyo ta wajen ba kuma yana lura babu wanda zai lura akwai mutum a wajen. Dukda kasancewar yau Juma'ah, kuma masallacin cike yake makil da Al'umma, inda take ba waje bane da mutane suka fiye bi ba. Waje ne da yake sadaka da inda liman yake shiga masallaci to ko sahu ba'ayi ta wurin.

Ba kuka take ba, dan kuwa tayi me isarta har ta gaji. Idanunta sunyi jajir sun koma kamar danyen nama. Jikinta gaba daya babu karfi dan kuwa rabon da cikinta yaga abinci kusan kwana uku kenan. Saidai in ta samu ruwa ko ragowa taci. Amma abinci me sunan abinci? Ba dai ita ba saidai wata.

Tasan tunda liman yace ta jirashi a wajen to tabbas zai dawo, dan mutum ne shi me cikar kamala idan tun farko yasan bazai taimaka mata ba ta tabbatar bazai mata karya yace zaiyi ba. Jinginar da kanta tayi jikin bango tanajin yanda zafin rana yake ratsa jikinta, gashi sai zufa takeyi jikinta ya jike sharkaf da ruwan zufa.

Batasan bacci yana neman kamata ba sai lokacin da taji alamar wasu sun tsaya saman kanta. Firgigi tayi ta tashi dan ita a tunaninta su Baba Kamalu ne suka gano inda ta ruga sukazo daukarta. Zuciyarta na dukan uku uku haka ta bude ido. Ganin cewar Malam Zakariya ne tare da wata mata sanye da hijabin yan agaji na mata yasa ta saki wata kalar ajiyar zuciyar da batasan tana bukata ba.

Mikewa tayi tsaye tanaji gwiwowinta suna ansawa saboda yanda ta dade a tsugunne. Dago da nauyayyun idanunta tayi. Dan sunkuyawa tayi ta gaidasu baki daya.

"Ina yini, Malam," ta gaida shi kafin ta juya ta gaida matar itama. "Ina yini?" Dukda cewar a Kano aka haifeta kuma a nan ta taso, hakan be hana cewar da tayi Hausa a gane cewar ita din ba cikakkiyar bahausa bace.

"Lafiya lau," Malam ya amsa yana nuni da ita, "Yama kikace sunanki, yarinya?" Ya tambaya.

"Sunana Fatima amma anfi kirana da Batul ko Islam." Ta fada tana me sadda kanta kasa. Domin kuwa kaf dangin mahaifinta duk wanda zai kirata da Islam sai ya tabbatar ya tuna mata da asalinta da yadda a ganinsu wannan sunan sam be dace da ita ba.

"Masha Allah, Batul. Yanzu Hajia Hauwa zata wuce dake bangaren mata. Karki damu insha Allahu abunda muka tattauna zanyi kokari akai. Inma hakan be samu ba zamusam yanda zamuyi koda hukuma ne sai mu saka idan ma abun yafi karfinmu..." Shiru tayi ta sadda kanta kasa tana sauraren Malam Zakariya. Ita kadai tasan tsananin da take ciki da kuma cikakkiyar sanayyar cewar idan har abunda suka tattauna be faru ba to tabbas rayuwarta tazo kan gaba wajen karewa.

"Karki damu kinji? Malam yaman bayanin komai. Muje masallacin," Fadar Hajia Hauwa wanda hakan yasan Batul kallonta tana gyada kai.

So take ta kara rokan Malam Zakariya akan ya taimaka mata. Dan wallahi ita kadai tasan halin dangin mahaifinta amma sai taji nauyin yin hakan. Tunda ya tabbatar mata da zaiyi kokari tasan zaiyi din. Kuma ta mika ma Allah dukkan lamuranta tasan zai kawo mata mafita.

Sumsum tabi bayan Hajia Hauwa har suka shiga wani bangare na masallacin mata inda suke ajiye ajiyen kaya. Juyowa tayi ta kalli Batul tana murmushi kadan. Miko mata da wata zumbuleliyar hijabi tayi. "Karbi nan ki saka Fatima. Kinci abinci kuwa?"

Girgiza mata kai tayi. Wata kila Hajia Hauwa ta lura da yanayin da take ciki. Fita tayi ta shigo sai gata dauke da takeaway biyu sai robar ruwa data lemu, da alama wanda ake bayarwa sadaka ne a duk ranar Juma'ah a masallacin. Koda Hajia Hauwa ta miko mata karba tayi hannu bibbiyu tana godiya. Duka ta cinye su tas tasha ruwa da lemun ta dago tana kara yi mata godiya.

Jin an gama huduba za'a tada sallah yasa Hajia Hauwa tace mata taje tayi alwallah su shiga suyi sallah. Hakan kuwa akayi. Koda akai sujjada kuka Batul ta fashe dashi tana kara yima Allah magiya akan kar yabari su Baba Kamalu suyi galaba a kanta. Allah ya kawo mata mafita cikin gaggawa.

K'abila...Where stories live. Discover now