6

224 16 2
                                    

A tsaye suka iske shi cikin falon sai zarya yake yana tunani, jijiyoyin kanshi sun fito rado rado. Ko baka taba ganinshi ba kana ganinshi kasan tabbas ranshi a bala'in bace yake. Batul waje ta samu ta rabe ta zauna gabanta yana dukan uku uku dan tasan yau kam, dole rubutun kaddararta ya chanza salo. Wani sabon babi za'a fara rubutawa wanda ko ba'a fada ba dole yai mata wani kalar matsanancin ciwo.

Saida Khalil ya shigo ya zauna can nesa sosai da ita kafin Abba ya juyo yana kallonshi. "Ibrahim ashe baka da hankali? Ashe kai sakarai ne wawa wanda baisan ciwon kanshi ba? Wani kalar iskanci ne wannan? Dama kai dakiki ne wanda baisan hukuncin addini ba? Ina kallonka a matsayin me hankali me tunani har na yarda na baka amanar yarinya baiwar Allah, marainiyar Allah amma saboda kai munafuki ne kuma azzalumi shine ka yarda akaci amanata da kuma amanar Allah dakai?!" Da wani kalar karsashi yake magana, ga wani kululun bacin rai nan a muryarshi wanda in akace zaiyi kuka babu gardama a hakan.

Farkon fara kasuwancin Abba tun yana samartaka tsakanin Kano da Katsina ya farashi, dan haka duk wani samfari na zagi babu wanda Abba bai iyaba sai dai girma ne yasa ya daina wasu abubuwan dan kuwa ya dade a garuruwan nan kafin Allah ya bunkasa masa kasuwanci ya bude sashe a Abuja daga nan sai Lagos sai ma ya koma har kasashen waje yanzu ba adadi.

"Abba, zagina fa kakeyi..." Abunda Khalil ya furta kenan. Dan shidai yasan Abba bai taba mashi kallon banza ba balle har takai su ga zagi sai yau gashi Abba har marinshi yayi kan waccan kwailar yarinyar.

"Na zageka Khalil! Yanzu dan ubanka abunda kayi ba duka ya kamata a maka ba? Wallahi tallahi kaci sa'ar shekaru na sunja yanzu, baccin haka bugun bala'i zan maka yau saidai na kaika asibiti daga baya. Baka da hankali ne? Dama kai shashasha ne ban sani ba? Sakarai a haka kamar me wayau kamar kana da addini ashe kai tantagaryar jahili ne ban sani ba?!" Ihu ihu haka Abba yake masifa, inda yake shiga bata nan yake fita ba.

"Abba me nayi? Kayi hakuri in na bata maka rai amma ni ban..."

"Au bakasan abunda kayi ba? Bama kasan abunda kayi ba kace Khalil? Tashi kaje," Abunda Abba ya furta kenan kafin ya nemi waje ya zauna. Khalil ya bude baki zaiyi magana ya daga hannu ya dakatar dashi. "Tashi ka fitar min daga falo, minti daya bance ka kara a nan wajen ba, kanaji na?" Da kyar muryar Abba take fita yana kokarin danne bacin ran dayazo mashi.

Khalil sumu sumu ya tashi ya nufi kofa kafin muryar Abba ta tsayar dashi. "Idan ka shiga ciki ka fada ma uwarka an fasa aurenka." Abunda Abba ya furta kenan ko kallon inda yake ma bayayi. Da wani bala'in hanzari Khalil ya juyo yana kallonshi gabanshi yana dukan uku uku kamar zuciyarshi zata fito waje.

"Abba..."

"Zaka wuce ka bani waje ko sai na babballaka?!" Ya daka mashi tsawa wanda Khalil baisan lokacin daya fita daga falon ba dan yasan ran Abba yayi bala'in baci.

Saida Abba yaga fitar Khalil kafin ya juyo ya kalli Batul dake kallonshi mamaki ita kanta ya gama cikata dan kuwa bata taba tunanin Abba ya iya masifa irin haka ba. "Zo ki zauna nan kusa dani Fatima, kinji?" Muryarshi a hankali yayi magana kamar bashi bane wanda ya gama tada jijiyoyin wuya yanzu ba.

Ba musu Batul ta koma kusa da kujerar da yake zaune ta zaune kanta a kasa. Zuwa yanzu tayi nasarar tsaida hawayenta amma tsoro, fargaba da kuma bakin ciki sune ababen da sukafi komai samun mazauni a zuciyarta.

"Kiyi hakuri Fatima, bansan da wane kalar baki zan baki hakuri ba. Ki sani, wallahi ban yarda na aurawa Khalil ke ba dan na kawo ki nan a wulakanta ki Fatima. Ban yi haka ba kuma dan kizo a kaskantar dake a ci maki zarafi ba. Allah yaga zuciyarta, tunda naji bayanin Liman Allah ya sanya tausayinki a zuciyata. Kiyi hakuri da abunda ya faru yau, da wanda suka faru a baya dukda ban san dasu ba. Nasan banida hurumin rokar masu gafara daga wajenki amma dan girman Allah ki yafe masu. Sun zalince ki Fatima, ki yi hakuri kinji?"

K'abila...Where stories live. Discover now