CHAPTER 20

128 12 0
                                    

   *JALEELAH*
_The adopted child_
🦹🏻‍♀️🦹🏻‍♀️🦹🏻‍♀️🦹🏻‍♀️🦹🏻‍♀️🦹🏻‍♀️🦹🏻‍♀️

*_ROMANTIC LOVE STORY_*

*_WRITTEN BY AUTAR MAMA_*

*_FICTION STORY_*

*AMINA MUH'D BASO, INA TAYAKI MURNAR KAMMALA LITTAFINKI MEENAL KUSKUREN DA KIKAI A CIKI ALLAH YA YAFE MIKI... KUMA INA FATAN SAK'ON DA KIKE SON ISARWA GA AL'UMMA YA ISA YADDA KIKE SO... KUMA INA FATAN NA BA DAD'EWA BA ZAKI FARAI MANA WANI... ALLAH YA K'ARA BASIRA 'YAR UWA*

*Wannan page d'in sadaukarwa ne ga masoya wannan littafin gaskiya kuna bani nishad'i babu abinda zance saidai Allah ya saka da alkhairy*

*Team Salman sai dai mu dawo  gefe mu zuba na mujiya 😂 tunda Team Jaleel sun mana k'arfak'arfa 😂*

*FOLLOW ME ON INSTAGRAM @INTEE_BABY*

بسم الله الرحمن الرحيم
         _________________      
       ______
🅙︎𝗮𝗿𝘂𝗺𝗮𝗶 🅦︎𝗿𝗶𝘁𝗲𝗿𝘀 🅐︎𝘀𝘀𝗼𝗰𝗶𝗮𝘁𝗲𝗱📚🖊
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa da jama'a bisa harshen hausa_

                 🏔🅙︎🅦︎🅐🏔
*PAGE 39$40*

       Zaune ta ke ta zuba tagumi da hannu bibbiyu tana tunanin yadda rayuwarsu da Jaleel zata kasance... Dan batajin sam zata iya cigaba da rayuwa da shi... Wayarta ta d'auka dake gefenta.... Ta kai kusan minti hud'u tana kallon number da ta rubuta sannan tai dailing gabanta na fad'uwa... Ringing uku aka d'auka... Daga d'ayw b'angaren ta ji ance " Waye ne?". Ciro wayar ta yi daga kunnenta tana kallon number tunanin ko ta yi mistake ne, amma taga dai² ta rubuta. Cikin dauriya ta ce " Ina me wayar?". Daga d'aya b'angaren akace " Ai da me wayar da wayar duk mallakina ne... Dan haka baki da hurumin da zaki min wannan tambayar kinji ko?". Ba tareda Jaleelah ta ce komai ba ta katse wayar zuciyarta na tafasa.

Mufeedah kuwa na ajiye wayr Salman ya shigo... Kallon rashin gaskiya ya ke ma ta. Ba tareda ya ce komai ba ya wuceta tareda d'aukar wayarshi ya barta tsaye a d'akin tana binshi da kallo gaba d'aya ya k'ara ramewa yayi fari sosai. A fili ta yi kwafa ta ce " Indai ina raye wallahi bazaka tab'a auren wata macen ba idan ba ni ba". Daga haka itama ta bar d'akin.

Yau Aunty Lawisa said azahar ta zo gidan, amma yanayin da taga Jaleelan ya tabbatar ma ta da ba lafiya ba... Kuka sosai Jaleelan ke yi duk iya rarrashin da Lawisa ta ma ta Kain shuru ta yi sai da ta gaji dan kanta ta yi shurun. Nasiha sosai Lawisa ta yi ma ta kana za man aure... Taji hankalinta ya kwanta sosai. Cike da tausayi Aunty Lawisa ta ce " Kinga Jaleelah idan ya dawo ki sameshi ki bashi hak'uri idan ma wani laifin kikai masa ku zauna cikin kwanciyar hankali... A hankali soyaiyya zata shiga tsakaninku ba tareda kun sa ni ba, sannan zan tutturo miki wasu sirrika ta whatsapp da yadda ake dafa k'ananan abubuwa kema ki koya sannan indai kika tashi da safe ki dinga gaishe shi koda ace bazai amsa ba karki gaji wataranan zai amsa... Kinji ko? Kinga yanzu yamma yayi kuma yau zamu koma gida, sauran bayanan zqn miki idan mun had'u online, sannan shima Jaleel d'in zan mishi magana kinji ko? Ki daina sa damuwa aranki". Kai kawai Jaleelah ta d'aga alamar ta ji tana share hawayenta.... Sai da Aunty Lawisa ta ba ta had'i sosai na ma ta masu kyau da inganci sannan ta barta ita ta taho gida....
 

Bayan la'asar Jaleelah ta yi searching d'in yadda ake yin faten dankalin turawa.... Duk ingredients d'in ta had'a da yake tana da komai a fridge... Kifi ne da alayyahu ba ta samu ba... Haka ta yi tana yi tana duba yadda suke yi. Girki sai khamshi ya ke ta sauke abinta ta d'iba ragowar ta kai dining... Zama ta yi a parlo tare da plate d'inta na abinci da kuma lemon kwali. Cokali d'aya ta kai baki... Ko taunawa batai ba ta nufi hanyar toilet da ke cikin parlon ta furzar dashi tana yamutsa fusaka, ruwa tasa tana d'auraye bakinta... A fili ta ce " Chab... Idan wannan mugun ya dawo yaci abincinnan nasan yau kashe ni zaiyi". Abinci salam sai d'an karan yaji. Gyara wajen ta yi ta nufi sama  danyi wanka tazo ta kwashe abincinta kafin Jaleel ya dawo. Wanka ta yi ta tayi shirinta kamar yadda tasaba cikin k'ananan kaya... Sai khamshi ta ke yau kham harda kwaliyya duk da daurewa kawai ta ke tayi amfani da sharawara Aunty Lawisa.  Tana fitowa sukaci karo... Wani dum ta ji gabanta ya fad'i... Kallonta ya ke daga sama har k'asa yana jin wani yanayi a jikinshi. "Sa..sannu da zuwa". Ta fad'a da kyar. Wani irin kallo ya ke ma ta daga bisani ya d'aga gira d'aya ya ce " Oh... Kice yau da wani sabon salon kika zo?". Kanta a k'asa ba ta ce komai ba. Matsowa ya k'arayi, itama tamatsa jikin bango tana rarraba idanu. Gefen fuskarta ya shafo yana k'arewa kwaliyyarta kallo, cikin yanga kamar mace ya ce " Duk wannan fa na menene? Naga har girki akai ko?". A hankali ta d'ago idanunta ta zuba mishi har sun kawo ruwa... Cikin rawar muryar ta ce " Dan Allah Jaleel ka yi hak'uri idan ma na maka wani abun...ni banason irin wannan rayuwar". Kallonta yayi na 'yan sakwanni daga bisani ya fashe da dariyar rainin hankali yana kallonta. Sosai ta k'ufula hakan yasata juyawa zata shiga d'akinta... Da sauri ya fincikota suna kallon juna, rai a had'e ya ce " Jaleelah baki ga komai ba ai... Kawai na barki kici amarcine tukunna". Daga haka ya tureta har tana fad'uwa k'asa ya shiga d'akinshi... Kuka ta saki me k'arfi tare da dafe k'ugunta inda ta bugu... Sai da ta ji kiran magariba sannan ta tashi ta koma d'akinta.

••••••••••••••••••••••••••••••••••••
Yau Juma'a yai da² da sati biyu da auren su Jaleel... Kuma yayi dai² da saura sati uku bikin Salman da Mufeedah.

Jaleelah ce durk'ushe kusa da k'afar Jaleel da ke cikin ruwa tana gyara masa sai uban gumi ta ke, dan ita bata ga abin gyarawa anan ba amma tafi awa a k'afa d'aya ya k'icewa abarshi. Kamar zatai kuka ta ce " Jaleel Dan Allah kayi hak'uri wallahi na gaji... Bayana ma duk ciwo ya ke min". "Oh dagaske? Ai bansani ba". Ya fad'a cike da rainin hankali yana maida kanshi ga TV.  Be tausaya ma ta ko kad'an ba sai da ta gama tas. tagaji sosai hakan yasa ta zama ta huta a band'aki...

*Kuyi hkr da wannan banda charji amma zuwa anjima insha Allah zakuga wani update din*

Autar Mama ce

JALEELAH (THE ADOPTED CHILD)✓Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt