Chapter 22

114 10 2
                                    


🦹🏻‍♀️🦹🏻‍♀️🦹🏻‍♀️🦹🏻‍♀️🦹🏻‍♀️🦹🏻‍♀️🦹🏻‍♀️
    *JALEELAH*
_The adopted child_
🦹🏻‍♀️🦹🏻‍♀️🦹🏻‍♀️🦹🏻‍♀️🦹🏻‍♀️🦹🏻‍♀️🦹🏻‍♀️

*_ROMANTIC LOVE STORY_*

*_WRITTEN BY AUTAR MAMA_*

*_FICTION STORY_*

*Wannan shafin naku ne team Salman duk da dai an mana k'arfa² amma Salman yace yana gaidaku he really appreciate ur luv 😜*

بسم الله الرحمن الرحيم
         _________________      
       ______
🅙︎𝗮𝗿𝘂𝗺𝗮𝗶 🅦︎𝗿𝗶𝘁𝗲𝗿𝘀 🅐︎𝘀𝘀𝗼𝗰𝗶𝗮𝘁𝗲𝗱📚🖊
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa da jama'a bisa harshen hausa_

                 🏔🅙︎🅦︎🅐🏔
*PAGE 43$44*

     Washe gari Jaleelah na idar da sallar asuba ta had'a kayanta tsaf cikin k'aramar akwati... Bisar da ta ta k'asar Dubai ta d'auko wadda bata samu zuwa ba acan baya... Ta had'a komai. Hijab har k'asa ta sa ka,  sai dai hannun ta a waje wanda ya k'one... Cikin sand'a ta fita daga parlon gidan. Zata bud'e gatw me gadi ya fito da sauri yana tambayar " Hajiya lafiya?". Wani d'an iskan kallo ta watsa masa cikin b'acin rai ta ce " Dallah ni bud'e min k'ofa sakarai kawai". Kanshi a k'asa ya ce " Hajiya wallahi indai na barki kika fita Alhaji korata zeyi kuma da aikinnan na dogara ga matana da yara na sunkai ahirin a gida... Ki taimaka min Hajiya". Ganin yana son b'ata ma ta lokaci yasa ta tureshi ta bud'e k'ofar ta yi ficewarta. Iskar asuba me sanyi ce ta ke kad'awa sai had'a hak'ora ta ke. Tafiya ta yi me nisa har saida ta fita daga layin sannan ta samu napep... Har airport ya kaita... 7am dama jirginsu zai tashi... Ta gama komai kawai jira ta ke afara kiran suna. Wayarta ta ciro a jaka tareda yiwa Hajiya Mama sak'o daga bisani kuma ta sa ta a Airplane mode.

B'angaren Jaleel kuwa k'arfe 9 da 'yan mintina ya shigo d'akin hannunshi rik'e da tulin kayanshi. Ganin bata kan gado, hakan yasa yayi zaton tana toilet ajiye kayan yayi yana sauke nishi da k'arfi ya ce idan kin gama ki fito ga kayana nan... Inaso kafin na dawo da daddare na tarar da su a wardrobe d'ina a wanke a goge". Daga haka ya fice abunshi. Ko ta kanta be k'ara bi ba ya bar gidan. Me gadi kuwa ganin Jaleel be yi masa magana ba yasa hankalinshi kwantawa.

A hotel Jaleelah ta sauka... Layin garin ta sa a wayarta tare da kiran mataimakiyar awajen aiki akan ta kula ma ta da komai da bata jin zata dawo bakin aiki nan kusa. Wani dad'i take ji, ko banza zata huta idan Jaleel ya gaji da jiranta ai ya saketa dan bazata iya rayuwa da mara tausayi irin Jaleel ba. Salman be ya fad'o ma ta arai. Har ta yi niyyar kiranshi kawai ta fasa ta yi kwanciyarta.

*NIGERIA*

  Aliyu ne zaune kusa da Salman da ke kwance kan gado hannunsu sark'e da na juna... Aliyu kamar ya tsinkawa Salman mari ya ce " Ai sai ka je ka kashe mijin na ta, toh ka kashe mana idan ba haka ba tayaya zaka iya aurenta? Kuma billah Salman idan ka kuskura ka wulak'anta min k'anwata akan Jaleelah zasu b'ata". Daga haka ya zare hannunshi cikin na Salman. Cikin dauriyar ciwan da Salman ya ke ji ya tashi zaune ya ce " Aliyu, bazan wulak'anta Mufeedah ba! Amma kasani bazan tab'a sonta ba ko da da second d'aya ne! Meerah itace macen da zuciyata ta aminta da ita". Cikin zafin rai Aliyu ya juyo ya cakumi wuyan Salman idanunshi sun kad'a sosai jihiyoyin kanshi sun tashi cikin b'acin rai ya ce " How dare you Salman? Kai waye? Har ma ka isa?". Tureshi Salman yayi ya tashi da kyar yana kallon Aliyu ya ce " Ni ba kowa ba ne Aliyu face yaron da aka d'akko gidan marayu, kuma ban isa ba akan komai... Matsowa yayi kusa da Aliyu da ke huci yayi wani murmushi yana shafa kanshi yace " Aliyu amma duk da kasancewa ta mara iyaye kuma adopted person amma a haka k'anwarka ta gani tace tana so ko?". Cikin zafin rai Aliyu ya ture shi yana cewa " Dama ai tsintattciyar Mage bata mage Salman! ". Saukar mari kawai Aliyu ya ji a kuncinshi... Yasan dai ba Salman ne ya mareshi ba toh waye.. Muryar Abba ce ta katse masa tunaninshi " Ashe Aliyi baka da hankali? Shi Salmanun kake cewa tsintacciyar mage?". Shuru Aliyu yayi Abba na shirin k'ara masa wani marin Salman yayi saurin rik'e hannunshi...  Murmushi me ciwo Salman yayi yana sauke hannun Abba kauda kanshi yayi gefe yana share 'yar k'aramar kwallar da ta zubo mishi. Sannan ya juyo yana kallon Aliyu da Abba... Cikin lion voice wadda be cika magana da ita ba sai ta kama ya ce " Abba baxanso na zama silar cin amanar d'an uwanka da ka d'auka ba! Abba kuyi hak'uri amma ni ban shigo cikin zuri'arku don na lalata muku zumunci ba! Abba inaso kamin izinin tafiya ko na 'yan kwanaki ne". Kallonshi kawai Abba keyi daga bisani ya ce " Salman babu inda zakaje kaji ko? Bazan maka dole ba tunda baka son Mufeedah, bazan tilasta ka kayi abinda baka so ba saboda ina tunanin na d'akko gidan marayu ya zamana cewa baka da 'yanci... Kaima kamar kowa ne Salman kana da 'yanci dan haka na soke aurenka kaida Mufeedah, Allah ya fito ma ta damiji na gari". Bubbuga kafad'arshi Abba yayi yana murmushi sannan ya kalli Aliyu ya ce "Wuce muje". Sai da Aliyu ya yi wa Salman wani banzan kallo sannan ya bi bayan Abba. Mufeedah da ke mak'ale bayan k'ofa tun fara fad'an su Aliyi ce ta fito da gudu ta iso wajen Salman tareda zubewa k'asa tana rushewa da wani kuka meban tausayi. "Yah Salman Dan Allah karka min haka!". Ta fad'a tana girgiza kanta. Shima durk'usowar yayi yana kamo hannunta kamar zeyi kukashima yace " Mufeedah bana so na tauye miki hakk'inki idan munyi aure banaso nazama me laifi wajen Allah... Mufeedah, Meerah itace macen danake so!". Cikin takaici Mufeedah ta mik'e ta na share hawayenta ta kalli Salman tace "wannan mayyar? Itace? Toh wallahi indai kanka ne Salman sai na tabbatar da ta yi shuru na har abada". Daga haka ta wuce ta barshi tsaye yana nazarin maganarta.
***************

Sai yanzu Hajiya Mama ta ga sak'on Jaleelah... "Me take nufi da ta bar k'asa?". Cikin zafin nama ta d'auko mayafi tare da mukullin mota ta. Text kawai ta turawa Daddy tace ta fita. Koda ta isa gidan me gadi ta fara tambaya matar gidan... Jikin me gadin narawa ya fayyace ma ta duk yadda sukai da Jaleelah hakan ya tabbatar ma ta da cewar ta tafin dagaske. Jikinta ba laka ta shiga mota ta bar layin tana tunanin halin da Jaleelah zata shiga... Tabbas idan ta bari wani mummunan abu ya faru da Jaleelah bazata yafewa kanta ba.  Amma ta yi alkhawari nemo ta sannan babu wanda zata sanarwa inda Jaleelan ta ke. 

Kamar yadda ya saba dawowa kullum haka ya dawo.. Sai da gama shirin baccinshi yaci takeaway d'in daya shigo dashi sannan ya nufi d'akin Jaleelan. Yadda ya tafi ya barshi haka ya dawo ya sameshi, abun ya d'aure masa kai sosai... Cikin b'acin rai ya tura k'ofar band'akin amma ga mamakin shi a bushe band'akin ma ya ke alamar an d'an jima ba'a shiga ba... Cikin wani tunani ya fito ya fara dub'e² "me hakan ke nufi? Ta gudu ko me?". Fad'a afili a yayin da idanunshi suka sauka akan farar takardar da ke ajiye akan mudubi an danne ta da kwalbar turare. A hankali ya isa wajen ya d'auki takardar ya fara karantawa afili kamar haka;
_*Jaleel ina fatan ace wannan sak'on ya isa gareka, ni na yafe ma ka duk abinda ka min amma Dan Allah ina nan alfarma agareka... Ka taimakeni Jaleel ka sawwak'e min auren ka da ke kaina*_

Autar Mama ce.

JALEELAH (THE ADOPTED CHILD)✓Where stories live. Discover now