*HAYATUL ƘADRI!*
(LABARIN DA YA FARU A GASKE)
*HASSANA ƊAN LARABAWA* ✍️
EXQUISITE WRITER'S FORUM (EWF)
🅿️ 51-52
Ya dire kayan hannunsa kawai yana ƙarasowa da sauri ya riƙe ni ganin na tashi a hanzarce, ina ta kallon shi zuciyata na bugawa cike da ɗokin sanin abin da ya dawo da shi kwana biyu da tafiyar shi, amma fara'ar da na ga ni a tare da shi sai ta zaftare katso ma fi tsoka na fargabar da na samu kaina.
Ya ja ni kan kujera ya zauna ya ɗora ni kan cinyoyin shi yana duba na.
"Mami! Sai kika ganni katsaham ko?" Ya ambata hannun shi kan cikina yana shafawa.
Na gyaɗa kai na ce.
"Eh fa, lafiya dai ko? Me ya dawo da kai?"
Ya ɗora kan shi kan ƙirjina ya ƙanƙame ni yana sakin ajiyar zuciya, a haka ya yi magana.
"Abin da muka jima muna roƙon ALLAH a kai ne yau ya tabbata, Mami ki taya ni murna yau na samu aikin yi."
Na saka hannu na ɗago kan shi da ke tsakiyar ƙirjina, na ƙura masa idanu cike da mamaki na ce.
"Aiki fa ka ce! Wani irin aiki ka samu? Kuma a ina?"
Ya riƙe tafukan hannuna da ke rungume da fuskarsa ya sumbata, sannan ya ce.
"Kin san me? Yanzun ba lokacin bayani ba ne, ɗan taimaka mini da ruwa na sha kin ji."
Na zame jikina da hanzari zan miƙe, ya taimaka mini cike da tausayawa yana mini sannu, na yi murmushi na amsa sannan na wuce ktcheen na ɗebo ruwan na kawo masa.
Bayan ya sha ruwan sai ya miƙe yana dubana ya ce.
"Bari na je na dawo."
Ni ma na miƙe ina kallon tsakiyar idanuwansa na ce.
"Ina za ka je? Yanzu fa ka dawo ko hutawa ba ka yi ba."
Ya shafa kumatuna yana murmushi ya ce.
"Kar ki damu Mamina, ɗan anjima kaɗan zan dawo ba wani jimawa zan yi ba."
Kafin na furta komai ma ya sumbaci goshina ya fice da sauri, na ƙura wa bayansa idanu har ya ɓacewa ganina.
Na koma na zauna ina ta saƙe-saƙe da nazari, amma ban canko komai ba, sai na tattara komai na ajiye da nufin jiransa ya dawo domin ya warware mini ƙullin.*******
Sai yamma liƙis bayan na kammala girki na sha wanka da kwalliyata sannan ya dawo, na tare shi da murnata domin farincikin da na hanga a fuskar shi ya fi gaban kwatance.
ID card kawai ya zaro a aljihunsa ya damƙa mini bakinsa kamar gonar auduga, na mayar da kallona kan ID card ɗin ina kallo, kafin na gama karanta abin da ke jiki ya sauƙaƙa mini hanyar gano abin da ke jiki.
"Mami aiki na samu a wani kamfanin takalma, yanzu daga can nake sun tantanceni, wannan shi ne ID card ɗin da suka ba ni na shaidar sun ɗauke ni aiki...
Kafin ma ya kai aya na miƙe a firgice na daka wani uban tsalle na murna wanda ban taɓa yin irin shi ba, idanuwana a runtse nake tsalle da furta kalmar "Alhamdulillahi ya ALLAH!"
A rikice na ji ya kama ni ya riƙe kafaɗuna, na tsaya cak na buɗe idanu ina kallon shi sai haki nake yi saboda tsallen da na sha, ina ƙyalƙyala dariya, shi kam fuskar shi a tamke ya riƙa hararata har da sakin tsaki.
"Mtsww! Wai Mami ba ki da hankali ne? Hala dai kin manta da cikin jikin ki shi ya sa kike wannan tsallen ko? Gabaɗaya kin tayar mini da hankali wallahi."
Na afka ƙirjin shi cikin tsananin murna da farinciki na riƙo wuyan shi na ce.
"Murna ce ta ishe ni, na rasa inda zan saka raina, Wayyo ALLAH daɗi."
Ya sa hannu ya rungumeni yana sunsunar wuyana yana sauke numfashi, muryar shi ta yi ƙasa sosai yake faɗin.
"To kuma saboda murna kawai sai ki wahalar mini da kanki da baby Mami?"
Na sake shi na durƙusa na ƙara ɗaukar ID card ɗin ina dubawa, fara'a ta kasa ɗaukewa a fuskata, ji na yi kawai ya janyo ni ya waiwayo da ni gabansa, ya saka yatsunshi ya ɗago haɓata tare da faɗin.
"Ke kalleni nan."
Na zuba masa ido muna kallon juna, ya ɗaga gira tare da ce wa.
"Ni za ki rainawa hankali ko?"
Na ɗan zaro idanu ina kaɗa su alamar tambaya don ban gane nufin shi ba, ya hura mini iskar bakin shi wadda ta sa na lumshe idanu ina sakin ajiyar zuciya.
"Hmmm! Ni za ki yi wa pretending ko? Ki nuna mini ba ki san komai ba?"
Cikin mamaki na riƙo hannunsa na ce.
"Ban gane ba, Me na sani?"
Ya ja ni kan kujera yana faɗin.
"Zo zauna 'yammata."
Muka zauna, ya fara wasa da zif ɗin gaban riga ta, sannan ya ce.
"Kina son faɗa mini ba ki san cewar a gidanku a ka sama mini wannan aikin ba? Ba ki san cewar Mama ce ta samo mini ba?"
ESTÁS LEYENDO
HAYATUL ƘADRI!
Ficción GeneralRayuwa kowa da irin tasa, labari kowa da irin nasa, haka nan ƙaddara da jarrabawa sukan sauya rayuwar mutum daga asalin yadda take. Tafiya ce miƙaƙƙiya cikin rayuwa ta zahiri mai laƙabin HAYATUL ƘADRI.