(The legendary novelist📝💚💚)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟
💎💐 ..... WATA RAYUWA....💎💐phone number:09035784150
telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0
whatpad :@SAKHNA03
......Dedicated to proficient writer association........
Chp(29)
Labarin masarautar sardaham khairiyyah tafara bawa fahreeyah inda saidavta zayyane mata duk wani abu da ta sani game da masarautar sardaham din.
Saida suka zo wajen da sarki huruddeen ya kori yarima amam daga nahiyarsa said ta tsaya tareda jan ajiyar zuciya tana kallon fahreeyahn,hannun khairiyyah fahreeyah tayi da sauri kafin ta ce cikin zakuwa,
"Menene yafaru khairiyyah?ina yarima amam din,yadawo kuma ,meyasa suka hadashi da mahaifinsa har na tausaya ma sarauniya safeenah,gashi tanada mutumci,samun kamarta a wannan irin matsayin mai girma da halin dattako abune mai wuya,gashi........."
Khairiyyah ceh ta katseta da sauri tana dariya jin yadda take ta zuba kaman itace mai bada labarin,saida fahreeyahn ta taba ta kafin ta gane irin surutun da take,shiru tayi kafin tace,
"Toh kece ai ina tacemiki ki fada min mai yafaru kuma kinyi shiru"
"Gajen hakurinki dai ,dan ni bance miki bazan karisaba,kece kika fara bawa kanki amsa"
"Toh naji cigaba da bani labarin inaso naji mai ya faru wallahi"
"Shikenan,kaman yanda kika tambaya yarima amam yadawo inda abubuwa suka faru har takai ga auransa da gimbiya nasreemah wadda Y'a ce a masarautar da kikazo"
"Ahah ni bana so ki bani a takaice,ki bani shi cikyekykye kaman yanzu akeyi a gabana"
"Shikenan"
**********************
Lokacin da sarauniya safeenah taga cewa dagaske ne danta amam yabar cikin nahiyar sardaham kaman yanda ya ambata sai hankalinta yatashi matuka yazamana koh fitowa batayi sosai bare tasan mai ake shukawa a cikin gidan,Koyaushe tana dakinta rike da hoton yarima amam ,in ta ajiye hoton to sallah zatayi koh kuma amintacciyar baiwarta wato sameerah ta tursasa mata cin abinci.
A bangaren su zulaikha kuwa duniya sabuwa ta dawomusu tamkar sallah,ganin duk wani shiri da suka aiwatar yatafi yanda suke so.
Zulaikha ceh a zaune a falo itada Y'a r ta NEELAH wanda tazo ganin gida ko kuma zuwa hada wata masifar,neelah ce ta kallai mahaifiyar tata tace,
"Yanzu ummah tunda komai ya tafi yanda muke so toh mekuma kika shirya abinda za'ayi nan gaba?"
"Eh yanzu abinda nakeso ki bar manneer a wajena na rikeshi"
"Amma ummah manneer kuma mai zaiyi anan muda zamu tafi ,kinsan ma mahaifinsa bazai yarda ba"
"Lallai neelah har yanzu da sauranki,toh in ke baki hango abinda nake nufiba shine,idan na rike manneer a wajena zanyi kokarin ganin na turashi a wajen mai martaba da kuma sauran manyan gari saboda tunda babu yarima amam sai kawai ya hau sarauta,shikuma mijinki na kinsan bawani damuwa da shi zaiyi ba,saboda manneer shine da na bakwai a wajensa amma idan yaji dansa zaiyi sarautar nahiyar sardaham nasan da gudu zai amince da abinda kikace,toh ya kikaji abinda na shuka?"
"Wayyo ummah jinake kman na cinye ki dan murna ace dana zaiyi sarauta nikam abin yamin dadi"
Zulaikha ceh itama ta rungume yar tata tana murna Sannan tace cikin zolaya,
"Toh Iran kika cinyeni saiki samo wata ummah koh"
"Ahah ke kadai tawa ta kaina,barina je wajen su innah kafin nazo nafara shirin tafiya"
Tafada tana barin falon mahaifiyar tata fuskarta dauke da murmushi.haka kuwa akayi,lokacin da gimbiya neelah ta tashi tafiya sai ta bar manneer a wajen mahaifiyar ta ita kuma ta tafi gidanta.
Funds ga wannan ranar sai yazaman duk wani lokaci idan za'ayi wani zama a fada ko wani taro sai zulaikha takai manneer a nufinta wai ya koyi sha'anin mulki tun yana karami,dayake abin na tsafine kuwa koh da wasa babu wanda ya taba tambayar wani inda yarima amam yake ko kuma meyasa yatafi daga nahiyarsa,sai kawai a zuciyar uwa wanda soyayyar sa ta gagara fita daga zuciyarta kullum tana cikin mika kokon bararta ga wanda baya bacci.
Sanadiyyar ruwan kyauta da take zubawa duk wanda ya nuna kulawarsa ga gudan jikannata sai yazamo cewa kowa ma in kaji zancensa toh yarima manneer koda kuwa baka sonsa a zuciya toh zaka nuna kana yi kodan kar dan ruwan arzikin da ake rabo ya wuceka.
Lokaci yaja tun sarauniya safeenah tana daurewa har yazamto cewa ta daina magana saidai duk abinda zaka fada idone nata kawai ,in ka dameta ma saita bar wajen da kake,wannan halin da ta farayi shiya fara damun sarki huruddeen saboda duk maganar da zaiyi bazata kulashi ba ballantana yasa ran zata bashi amsa.
Watarana ne yazo wajenta yana mata magana amma ko juyowa batayiba,numfasawa yayi can kuma yace,
"Nasan kina jina,amma nasan hakan ba halinki bane ,ba yanda zakiyine saidai inaso nasanar dake na amince yarima amam ya dawo gida ya cigaba da zama cikin yan uwansa"
Wata irin zuyowa tayi tareda share hawayen dayake fuskarta tana murmushi,karisawa yayi inda take tareda tallafo kanta yasaka a kirjinsa,
"Zan miki wannan alfarmar ne saboda yanda naga halin da kike ciki,sannan kedin macece mai biyayya a gareni idan na tauye miki hakki na rabaki da danki guda daya tilo banyi miki adalci ba,dan haka na yarda babana yadawo gida amma bisa sharadi guda daya"
Dago da kanta tayi ta kalleshi da alamar tambaya a idonta,shima gyada mata kai yayi kafin yacigaba da cewa,
"Eh dolene yayi aure kaman yanda nace a baya,sannan tunda bashida wacce yake so yanzu na riga nayi masa mata yana dawowa za'a daura aurensa washagarin sanda yadawo,saiki fadamasa don nasaka dogarawa su kirashi duk inda yake a fadin duniya ,wannan shine sharadina idan yanason farinvikinki nasan bazai gagara aikata abinda na umarceshi ba,in kuma zai min gardama kaman farko toh zan sallama shine nima"
Ya na gama fada yafice daga turakar gimbiya safeenah yayi hanyar nasa sashen.
Duk da sharadin da sarki huruddeen yafada wa sarauniya safeenah hakan bai rage komai ba daga murnanr da take na dawowar dannata
Tohfahh!!! Su yarima amam za'a dawo gida ,Karku gaji kucigaba da bina inshaallah zamu kai ga ci😊😊😊🤩🤩🤩🤩SADY-SAKHNAceh❤❤❤
YOU ARE READING
Wata Rayuwa
AdventureLabari kan karamar budurwa data samu kanta cikin kangin rayuwa,!!!! Faryah karki taba barina ke tawace har abada,hakika nayi dacen samunki, Toh amma yazaiyi daya bude ido yarasata a duniyarsa? Sannan ita yazatayi da WATA RAYUWAR data tsinci kanta? W...