Chp(26)bazaki koma ba....

71 13 0
                                    

(The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟
     
💎💐  ..... WATA RAYUWA....💎💐

phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03

  ......Dedicated to proficient writer association........

Chp(26)
Ganin razanar bazata yimata ba sai ta matsa sosai domin jin mai zasu ce wanda tasan bazai wuce akanta ba,
"Yana so a sanar dake ne cewa a bada ajiyarsa daya baki idan harkin gama kiwonta yanda ya kamata"
Jikin fahreeyah ne yafara karkarwa da taji mai yace dan tasan ita yake nufi za'a mayar saidai hankalinta yadan kwanta da taji abinda INNAN tace saidai tasan hakan bazai hana ta komawa wajen da ko a mafarki bata fatan tunashi bare kuma komawa wajen,
"Ina so kaje kace masa bata gama warkewa ba har yanzu kuma karna kara ganin kafarka anan wajen"
Bayan ya tafine fahreeyah tafito daga dakin tana sunkuyar da kai har ta isa wajen da inna take zaune,
"Inna um........"
"Kiyi Shiru karkice komai saboda bazaki koma wajen ba,wannan magana tace,in kuma sun dage toh su kaimu nidake"
"Amma inna inkikace haka zasu iya kaimu nidake duk tare"
"Kin taba ganin inda d'a yakai uwarsa wajen horo batare da ta aikata komai ba"
Zare ido fahreeyah tayi tana kallon innan da alamar neman karin bayanin abinda taji innan tace,
"Ehh nasan zakiyi Mamakin hakan,shugaban kurkukun da su ka kaiki dana ne na cikina sannan shikadai na haifa,saidai bani ce na shaku dashi ba,ya girma ne a wajen yar uwata da aka haifemu tare KAINATA,itace ta rike shi  tareda yar ta KHALISA,nikuma ni ce na raini yarima saheel ,sarkin wannan masarautar bashida tausayi wannan dalilinne yasa suke shiri da dana wato KAMARU,sboda shima haka hlinsa yake tun yana yaro,wanda nikuma banason hakan saidai babu yanda zanyi,musamman dana ji ya damka masa ragamar horon wannan masarautar sai abin yafimin ciwo,ga kuma rashin yar uwata da kuma yarima saheel ,shiyasa nabar cikin masarautar na zauna anan wajen,na dade magana bata hadamu da shi saboda muguntar da sarki yake sakashi yana aikatawa,abinda yasa bana masa magana a wani,saboda hana horar da mai laifi ne,saidai ynzu bazanyi shiru saboda sun so cutar da wanda bashida laifi,dan haka koni koshi ne yanzu"
Shiru fahreeyah tayi tana sauraron abinda innan take mata,wanda a take gabanta yafara bugawa da taji innan ta ambaci saheel,saboda lokacin da take bata labarin taboye ainihin sunayen yan labarin,saboda tsaro,
"Ton amma inna menene alakarki da sarkin garin?"
"Mahaifinmu shine babban dogarin dayake kulada duk wani lamari na gidan sarautar nan,sannan nikuma da yar uwata mu muke kulada duk wani shige da fice,wato a takaice shugabannin bayi mata,wanda muka karbi aikin tun lokacin da mahaifiyar mu ta mutu"
Gyada kai kawai fahreeyah tayi saboda bata da abin cewa yanzu kuma.
***********************

A wajen su kirisah kuwa,tun lokacin da taga tarkon da ta dana yaci sai murna da farin ciki ya isheta,wanda sareeenah kuma ta kwana tana kuka tareda tausayin halin da fahreeyahn zata shiga a wannan azababben wajen.
Bayan kwana uku da abinda yafaru ne gimbiya nameemah ta aiko wasika akan tana Neman kirisah,murna tafarayi,ganin ta cika burin ta kuma ga kira daga wajen gimbiya,tun kafin tasan mai zai faru tafara dagawa yan wajen kai,ita a dole ta wuce matsayinsu.
Tun dan sako bai karisah komawa ba saiga kirisah a falon farko na turakar gimbiya Nameemah tana jiran fitowarta,
Nameemah tana shigowa ta tashi tana yimata gaisuwa tareda washe hakora,wani kallon kasa tayi mata kaman bazata amsa ba saikuma tace,
"Naga abinda kikayimin nafadamin abinda yake faruwa ,dan haka zan sakaki a cikin bayina,idan naga kokarinki zan iya tafiya dake gidan aurena dan dagani zaki iya amfani,yanzu saikijie ki karbi kayan bayina a gun jakadiya,saboda banason wannan kazamin kayannaku,tafatan kin jini?"
"Eh ran ki yadade nagode za'ayi yanda kikace"
Da haka sannu a hankali kirisah tahada gimbiya nameemah da amintattun bayinta,har saida yazamo cewa ita ce farkon wanda nameemah take nema kafin kowa a hidimrta.
Bikine yamatso ya kankama inda su kirisah ake ta shiga da fita ana shirin auran uwar dakinta,ana cikin hakanne kumaru yasamu gimbiya nameemah yafada mata abinda mahaifiyarsa tace akan fahreeyah,da farko bata  amince da kin komawar fahreeyah makargama ba saidaga bayane tace
"Shikenan tunda ta dage kuma kace abinda ta taba umartarka dayi Kenan tun shekara ashirin baya,amma fah kasani dolene kuma nabata horon"
"Eh karki damu dama nasaka ta a cikin Wanda za'a bayar a matsayin kyauta ga tukwuicin aurenki"
"Mehhh kana nufin taje garin danake kuma acikin bayi masu daraja ,ba zai yiyuba,kasaka ta a cikin bayin da zasu kai kaya ga masarautun da suka zo"
"Shikenan an ga ma rank I yadade"
**********************
Fahreeyah ce zaune itada inna sungama cin abinci suna dan taba hira,wani dogarine yazo bakin dakin innan tareda tsugunnawa ya mika wa innan wata wasika a nade,
"Sakone daga gimbiya nameemah"
Karba tayi shikuma yajuya yabar wajen,saida yayi dan nisa tukun kafin ta bude Wasikar,
*daga gimbiya nameemah*
Barkan ki inna kainana,tunda kin hana danki hukunta mai laifi to inaso nasanar dake cewa bazata zauna a masarautar nan ba,inkuma kika ja da wannan hukuncin nawa toh zan nuna karfin ikona.

             NAMEEMAH***
Shiru inna kainana tayi tareda maida wasikar ta rufe,
"KO kwantar da hankalinki babu inda zakije,"
"Ahah inna,kinmin abubuwa da dama bazan taba mantawa da alkhairin ki ba nagode sosai"
Shiru inna tayi kaman zatace wani abu saikuma tayi shiru tareda ajiye wasikar da take hannunta,wata karamar takarda ce tafado daga cikin wacce ta karanta din,wacce aka rubuta inda fahreeyah zata tafi,
*Masarautar sardaham,cikin bayin gimbiya nasreemah matar yarima shamam(amam)*
Kallon kallo inna suke itada da fahreeyah bayan jin abinda yafaru,suke ajiyar zuciya inna tayi kafin taja fahreeyah daki,
Bayan sun zauna inna tariko duk hannu fahreeyahn acikin nata,
"Inaso KO saurareni da kyau,dama nayi niyyar daukanki mubar wajennan saboda wani dalili amma tunda hakan ta kasance inaso zan hada miki wani magani,idan har kun isa ki tabbatar kinsha,sannan wasikar dazan baki zan fada miki wacce zaki nema ,wato yar uwata tana can a masarautar sardaham,kitabba tar kinneme ta kin bata kafin wani abu yasameki,itama zan aika mata sako da tsuntsun danake aika gunta zata nemeki idan kikaje,ina fatan kin fahimci abinda nace"
"Ehh na fa him ta"
DA safe kuwa saiga dogarawa sunzo tafiya da ita,inda ta kankame inna Kainana tana kuka,kwantar mata da hankali tayi kafin ta ciro maganin ta bata ta juya cikin bukkarta da sauri,itama fahreeyahn juyawa tayi tafara tafiya,aranta tana tunananin zaman wata tara dasukayi da inna kainana n,wanda yabada shekara guda kenan tayi a masarautar,tabbas tasamu abubuwa da yawa a wajen na dadi da na wahala har ma dana bakin ciki,yanzu kuma zata ga ya rayuwa zata sake zefata a wani karon.
Kaman yanda suka fada kuwa,washagari da wuri kowane bawa yabi sahun inda aka kaishi,inda fahreeyah ta shiga cikin bayin dazasu tafi masarautar sardaham,inda zasu raka gimbiya nasreemah gidan da ta ke aure,bayan antafi da gimbiya nameemah dakinta bayan daurin aure.
Kaya kowa aka dora masa inda fahreeyah itada wata matace kawai matan da zasu tafi masarautar sardaham din,tun daga tafiya nauyi yafara isarsu,sai nishi suke,
Addu'a fahreeyah tayi a zuciyar ta tareda cewa allah gamu gareka!!!!!!!tofah,karku dai gaji kici gaba da bin labarin,inshaallah zaku sameni mai saka ku farinciki.😍

SADY-SAKHNAceh❤❤❤

Wata RayuwaWhere stories live. Discover now