Chp(37)ita ba baiwa bace

84 10 0
                                    

The legendary novelist📝💚💚)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟
     
💎💐  ..... WATA RAYUWA....💎💐

phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03

  ......Dedicated to proficient writer association........

Chp(36)

Cikin nutsuwa yake sarrafa jikinta kaman mai kokarin tab'a tangaran yana kokarin kar ya fashe.
A wajen fahreeyah kuwa duk da cewar tasha wahala amma bata nuna masa ba,sai murmushi da take masa a duk lokacin da suka hada ido,dan yanzu ba karamin tausayinsa takejiba.
Bayan yagama saka mata kayane suna zaune,wanda sannan asuba ta kusa yi,
"Yah amam"
"Ma'am menene?"
"Ina tsoro sosai saboda gani nakeyi kaman bazan haifi wannan cikinba,ciki na gaske ba haka yake ba,koda kunga alamun zan mutu kuyi kokarin fitarda abinda yake cikina kaida inna kainata,dan har yanzu yana motsi ina jinsa,karka cemin bazakayi hakan ba,dan ni kaina sheda ce kanason abinda ke cikina,ina tsoron na kasa jurewa "
Hawayen dayake fitowa daga idonsa ya share kafin yasaka dan yatsansa a baikinta yahana ta cigaba da abinda take fada,
"Yah isa haka,banason nasake ji kinyi wata maganar kuma,yakamata kidan kwanta ki huta kafin ayi sallah"
Daga haka ya shima ya kwanta tareda zawota kirjinsa.
A yanzu fahreeyah ta shafe wata kusan biyu a sashen yarima amam,shikansa in ka ganshi yana cikin tashin hankali shida su khairiyyah ballanta kuma ita uwar gayyah wato fahreeyah,kullum in ta kwanta da fargabar mai zata tashi tagani gobe takeyi,tun tana tunanin haihuwa har ta daina saka wannan tunanin a ranta har ta daina,kawai ta mika lamarinta ne ga mai duka.
A wajen nasreemah kuwa a kasarsu bahmeer,zamanne ya isheta,ga kuma mai martaba daya sakata a gaba,duk da tasan tanason yarima amam saidai zuciyarta takasa barinta komawa gidansa,saboda a yanda sarauniya zulaikha ta fada mats,haka zata kare rayuwarta babu haihuwa.
Gidannasu a cike yake saboda gimbiya nameemah ta zo ganin gida bayan auren da tayi,kowa farinciki yake da zuwanta wanda ba komai bane saina dole,a gefenta kuwa kirisah ce tasha kayan bayi amma masu tana wani daga kai,saboda yanzu ta shiga ta fita ta raba gimbiya nameemah da duka bayinta,yanzu babu wanda nameemah ta yarda dashi kaman kirisah.
Bayan sun gama hutawane da gaida mai martaba saikuma tayi hanyar sashen yar uwar tata dataji labarin ta dawo gida,samunta tayi akan kujera tana kallon waje ita kadai,
"Yar Uwa"
Juyawa tayi da sauri ta rungume nameemah cikin farin cikin ganinta.
Labarin abinda yafaru ta kwashe tabawa kanwar tata duk abinda yafaru.
"Toh amma inaga ba haka za'ayiba,yakamata ki koma inkuma aka samu magani fah,idan bakyanan wata zai aura ta haihu inkika yarda aurenki ya mutu,dan haka ki shirya kicewa mai martaba zaki koma,kinga ma yanzu can masarautar zamuje saboda mai gidana yanason kaiwa ziyara can,kinga saimu tafi tare musan abinyi acan din"
"Hakane kam kin kawo shawara amma yaushe zaku tafi?"
"Jibi zamu wuce inshaallah"
"Shikenan kafin sannan munyi magana da mai martaba din".
Hakan kuwa akayi bayan nasreemah tayiwa mai martaba maganar komawarta bai hanata ba,saima fada dayayi mata akan,karkuma tazo tana cewa zata sake dawowa kuwa,tana maida shi karamin mutum a idon duniya.
Shirya kayanta tayi suka nufi masarautar sardaham din itada kanwarta da mijinta dakuma baiwar ta wato kirisah.
Kwanansu daya suka isa nahiyar da daddare,inda suka kafa tanti suka kwana da safe kuma suka shiga ainihin cikin masarautar,wucewa sukayi sashen nasreemah akan idan suka huta sai suje ta gaisa da surukannata.
"Toh muje sashennaki nima na huta nasan shikam wajen mai martaba zai wuce"
Nameemah ceh tafada itama tareda da bin nasreemahn.
Abinne yabasu mamaki ganin yanda aka sanja tsarin falon hatta kujerun ansanjasu ba nada bane,
"Nasreemah yanaga kujerun kaman na mai ciki"
"Mai ciki kuma?"
"Eh mana kujerun masu cikine irin wanda cikinsu ya tsufa,toh mai hakan yake nufi?"
"Oho no bansaniba dan ba haka..........."
"Dakata bakiji kamar magana ba acan dakin?"
Kirisah ceh datake bayansu tayi saurin cewa,
"Eh nima naji maganar mata kaman suna hira"
"Amma kuma can dakin amam ne fah"
Nasreemah tafada da Mamaki,basuyi kasa a gwiwa ba kawai suka nufi hanyar dakinnasa.
A Zaune suke itada khaleesah da khairiyyah a dakinta,suna ta zance akasan dakin itakuma tana jingine da filo a akan gadon,duk hirar dasuke jinsu kawai take,dan ita yanzu magana ma wahala take bata dakuma cin abinci,shiyasa idan taga ana cin abinci ko hira sai tayi ta sha'awar hakan,koda bazata iyaba tana so taga anayi a kusa da ita.
Su khairiyyah basu ankaraba sai ganin kawai mutane sukayi akansu,da mamaki khaleesah suke kallon su inda suma din Mamakin ganin su khairiyyah sukayi a lokacin ,gashi sun dagargaje akan daddumar yarima amam din,suna cin abinci na alfarma,ko lokacin da take gidansa bata samun irin wannan damar a dakinsa.
Duk abinda suke ba wanda yakula da da fahreeyah da take kwance akan gadon,saidai itama tayi Mamakin ganin su nasreemah a lokacin.
Kirisah ceh ta kulada fahreeyah dake kwance akan gadon,aikuwa cikin daga murya takira sunan ta,hankalinsu ne ya koma kanta dukansu.
Sunkuyar dakai fahreeyah tayi dan batasan mai zata ce ba,
"Kutt mai wannan matar take itakuma anan wajen ?"
Nasreemah ceh ta tambayi nameemah jin abinda tafada,
"Wacece itadin"
"Itah ce Wacce gimbiya nameemah takama itada mijinta"
Kirisah tayi sauran bada amsa cike da Mamakin ganin fahreeyahn,
"Toh shine nima ta biyo nawa mijin,toh baki isa ba,mijina yafi karfinki kina kaskantacciyar baiwa kina bin mijin wanda suka fi karfinki"
"Ba baiwa bace,sannan zancen miji dakike fada kuma ,tun kafin yazama mijinki yazama nata,ke saida kikasan matsayina tukunna kika aureni ita kuma ta aureni batareda tasan koda ainihin sunana ba,kin kasa jure lalurata na tsawon shekara itakuma ta jure na tsawon shekara biyu,kuma nayi imanin ko zata rasa ranta toh bazata taba gazawa ba,duniya ta tazama duhu tun sanda narata har zuwa samunta,wanda zamanki a rayuwata kika kasa cireni a ciki,ita din matatace wacce nake alfahari da ita ko ina zanje kuwa.
Ke kuma da kike cewa kin kamata da mijinki to kisani cewa mijinki da duk wani na miji ba'a haifeshiba wanda zai iya jan hankalin fahreeyah har tajen gareshi saini kadai kuma ki fadawa kowa haka,saidai kije ki tambayi mijinnaki koshine yayi kokarin shiga gonar da ba tasa ba,kuma daya shiga gonar toh bazai taba amfanuwa ba a duniya ,saboda hukuncin da zan zartar a Kansa "
Kowa juyawa yayi ya kalli yarima amam harda yarima saheel da suka shigo tare, wanda idonsa yayi ja saboda jin zafin abinda du nameemah suka fada akan hasken rayuwar tasa.

SADY-SAKHNAceh❤❤❤
#comment
#vote
#share
#like

Wata RayuwaWhere stories live. Discover now