*Kanin mijina*Na
*Ummkulthum Ahmad*
*A.k.A Aunty Divaa*
*10th June ,2021*
(1)
"Haa". Yace Mata Wanda yake nuna alamun ana so mutum ya bude baki a bashi abu a bakin..
Bude wa tayi cike da kunya. zuba Mata zuma yayi a bakin.hadiye wa tayi tana lumshe ido,sake cewa yayi "Haa"
Ta sake bude wa,a wannan karon ya debo ice cream ya zuba Mata a bakin ta,wani dadi,Zaki,gardi da ni'ima na musamman taji Yana nunkaya da ita a kogin soyayya..
A ranta take Ayyana irin yadda Maanch din ta ya iya tafiyar da ita cikin salo salo na soyayya me mantar da bawa imanin sa,a gefe guda Kuma yana sa bawa jin kunya.shi dai Kam ko a kwalar shi..
Kallon shi take yi cike da so da kauna,ga dai shi tana so ta nuna masa irin hakan ita ma,amman inaa tana jin nauyin shi.musamman in ta dubi shekarun shi.
Akalla Maanch yana da shekaru 45 a duniya.duk da yanayin jikin shi be nuna ba.dan sunyi gadon kyaun jiki a gun Gwani na Allah.yayin da ita Kuma take da shekaru 28. Se taga da girman ta amman ta ruga irin wannan abubuwan? Kai gaskiya da kunya, musamman in ta tuna cewa kar yaga zaqewar ta se ta kama kanta a guri guda ..
Cokalin ya Mika mata bayan da ya tabbatar ya bata ta Sha da kyau .
A kunyace ta amsa,kamar yadda ya bata zuma haka ta bashi ,ta Kuma bashi ice cream din shima..
Kallon ta yake,a yayin da take fassara ma'anar kallon,kallo ne wanda ko a Ina take in ya mata shi tasan me kallon yake nufi,tasan mi ma ya kunsa tare Kuma duk Wani shika shikai ko farillai gami da wasullam da ka hado su ya basu babban jam'i..
Haka Kuma duk sanda ze Mata wannan kallon se taji gaban ta ya fadi,dan sabo da a duk sanda aka shiga yanayi irin hakan bala'in muzanta take yi.
Takan Yi kuka ba Dan kadan ba,Amman shiko Maanch ba abun da ya dame sa,shi wai be ma sani ba a yadda ya fada.ita kuwan tasan kawai yana kaara Mata ne..
Ba yadda ta iya dole ta saki jiki ta bi yadda idon shi ya nuna mata aka samu zaman lafiya...
Wannan fa mafarki ne. Wanda ya faru kafin tafiyar Maanch Lagos shine take bitar sa a baccin ta.
Asalin Labarin
Kwance take tana bacci a kan lafiyayyen gadon ta,bacci ne take me cike da mafarkii me gardi da tsayawa a rai akan Maanch din ta mijin ta Kuma Masoyin ta darling hub din ta..
Wayar ta ce ta hau Kara,Karan da ya katse Mata baccin ta,mafarkin ta me dadi,mafarkin da ta fi appreciating din shi akan reality..mafarkin da ko kadan ba jin kunya bare muzanta a ciki shi..sedai Kash Maanch din nata,da kan shi,shi ya katse mata mafarkin nata da take Yi a kansu ..
"Assalamualaikum" tace bayan ta daga wayar cikin wata iriyar murya me jan hankali.murya me cike da natsuwa,hankali tare da farin cikin jin masoyin ta..
Zaki,da gardin murya na daya daga cikin baiwar da Allah ya wa Aishatu,a dalilin muryar, ta daga bangaren me Kiran kuma..
A dayan bangararen seda tsikar jikin shi ta tashi,yayin da ya gyara kwanciyar shi,ta yadda zefi jin dadin yin wayar da kyau Malam.
Cewa yayi .."wa'alaikissalaam Hasken Maanch,farin cikin maanch ,annurin ruhi , zuciya da gangar jiki na,sanyin Rai na,matar Aljanna,my baby Aanch ya Akai, bacci ake ne ?"
Hakika Aanch ta narke tamkar yadda butter take narke wa yayin da aka Saka ta a rana,ta nutse tamkar yadda Allura ke nutsewa in aka sake ta a cikin ruwa,gaba dayan ta ta dulmiye saboda tsabar yadda shaukin wannan Kakkaurar soyayyar ta buge ta..
YOU ARE READING
KANIN MIJINA
RandomLabari akan Aanch da Maanch da suka kasance ma'aurata,suna son junan su a zahiri,sedai a badini Kuma akwai cin Amana..