*Kanin mijina*Na
*Ummkulthum Ahmad*
*A.k.A Aunty Divaa*
*12th June ,2021*
(2)
❤️😍❤️😍❤️😍
Aanch matashiyar mace me ji da kyau da tarbiyya ,ta dai zaunu a gida kafin tayi aure,dan tana da shekaru 27 tayi aure,auren ma nata dududu shekarar sa guda,Se da tasha surutu kan tayi aure.ace wannan ace wanchan har se da lokacin yazo sannan tayi shi, sedai har yanzu Kuma Bata haihu ba.
Mijinta Maanch soyayya ce a tsakanin su wacce tafi gaban misali,a ranar da Maanch ya fara ganin ta yayi imanin cewa itace wacce ta dace dashi.ita ce wadda yake gani a baccin sa amman tafiyar ta kawai ake nuna mishi,se Kuma tsananin Jin kunyar ta.toh ko da ya ganta ya yarda ba tantanma itace,musamman yadda yaji gaba dayan jikin sa ya amsa,tsigar jikin sa ya bala'in tashi.don Shima daman ya dade be yi auren ba ya zama tuzuru ..
A ran da ya ganta be Mata magana ba,Amman yabi ta a hankali ya ga gidan su.Ba Bata lokaci ya Kai magana gun Baban sa,koda aka zo aka fara magana manya suka shiga aka Sha aure,dukkan su suka gane daman Dan junan su akayi su..
Wata iriyar tsaftataciyar soyayya suke gudanar wa a gidan su,shi Maanch shine me assasa soyayyar a fili,ita kuwa Aanch komai nata da kunya take yinsa, amman akwai zallar soyayyar ta maanch a makale a kasan zuciyar ta.
MUN KOMA labarin
Washegari jirgin karfe 10 ya biyo zuwa kano.kano ta dabo tumbin giwa ko da me kazo an fika.
Gidan shi ya fara yada zango,ya Kuma samu ya shiga gidan da farin cikin shi ya tarar da annashuwa, yaje ya tadda matar sa ta Mai abincin da yake so ,tayi gyaran gidan ta,tayi kwalliya me kwantar da hankali ga Wani sassayan kamshi me ni'imal da take fidda wa,ga gidan nata kamshin turaren wutan da ta jona kawai yake yi..
Da shigar shi gidan ya ganta a tsaye tana dakin shigowar shi, dan daman ta ji an bude gate,so ta tabbatar shine ya shigo.dan daman shi mafi akasari yafi taho wa gida abun shi a taxi.yana sauka a Airport yake shigo wa mota yayo gida abunsa baya Wani jiran azo a dauko shi.
Shi be cika son bawa mutane wahala ba..
Yana da motar hawan sa guda Daya kirar Honda Accord 2016 sport.amman a gida yake barin ta dan Aanch ce ke zuwa makaranta da ita.toh shi me zeyi da mota? Mutumin da ba anan yake aiki ba. Iyaka in yazo nan ne yake dan hawa in ze fita fa..
A Lagos yake aiki,a chan Kuma yana da wata yar End of discussion da yake Hawa yake Yan harkokin shi da ita a chan Kuma ta ishe shi.
Daman wannan ma ita ce Asalin motar shi.ita Accord din dama ran daurin Auren sa aka Mai kyautar ta,Sarkin Kano ne ma ya bashi ita a saboda Gwani na Allah.wato Mahaifin Maanch.
A tsaye ya tadda ta tana ta murmushi,shiko hannu ya bude mata yana jiran ta iso gare shi,a kunyace ta nufe shi ta fada jikin shi,chukwuikwuye ta yayi yana auna yadda yayi kewar ta a satin da yayi kawai be ganta ba.
A tare suke sauke ajiyar zuciyar su,dan ma Aanch na ta kokarin boye nata.
A hankali ya rada mata "ana so ana Kai wa kasuwa" a kunne
Dan motsi tayi me nuna alamar Bata so.
Dago ta yayi yana mamakin yadda akai be ji shashakan ta ba,ya Saba duk sanda ze dawo ko ze tafi se tayi masa kukan ta na ka'ida..Ilai kuwa kukan take a kirjin shi tayi mukwui.
Shi ya rasa gane kukan nan nata takamaimai na mene take yi,abu guda ya sani,shine kukan bana tsiya bane,na arziki ne shiyasa be cika damuwa da irin su ba.da dadewa ya Gabe maanch irin matan nan ne da suke expressing komai nasu da hawaye,irin su ne mata masu tattare da rauni a kan komai na rayuwar su se su makale a bayan hawaye..
YOU ARE READING
KANIN MIJINA
RandomLabari akan Aanch da Maanch da suka kasance ma'aurata,suna son junan su a zahiri,sedai a badini Kuma akwai cin Amana..