(5)

171 2 0
                                    

Kanin mijina

By

Ummkulthum Ahmad

Aka Aunty Divaa

(5)

❤️❤️❤️❤️❤️❤️
🔥🔥🔥🔥🔥🔥
❤️❤️❤️❤️❤️❤️

Kallon shi ta sake yi yayin da yake tukin sa hankali kwance,se dai Yana kallon duk abunda take yi ta gefen idon sa.

Cewa tayi "kayi hakuri Maanch,kar kaga kamar na maka shisshigi a al'amuran ka kaji?"

Daga mata Kai yayi cike da wani Salo na yarinta ya koma dai dai ita .

Yadda yayi mata ne ya sa ta samu kwarin gwiwar fara magana .

Tace "dama fa akan maganar ukti ce.."

Seda ta dago Kai ta sake kallon shi sannan,saboda tana so taga yadda yanayin sa yake kafin ta cigaba da maganar.

Cikin sa'a kuwa taga yana yanayin nishadi nishadi.

Shi Kuma ganin tana ta dar dar ya sa shi maida abun wasa se ya fara rawa da Kansa yana dan yin wasu  abubuwa da bakin shi.

Yasan zata saki jiki ta gaya mishi koma mine abun

Ta samu dukkan kwarin gwiwar yin maganar .se tace "dama Maanch ni Ina ganin da ka daina yiwa ukti irin wannan fadan a halin da take ciki yanzu ze dan fi.

Kasan masu juna Maanch an fi son a ruga jawo su a jiki ana sasu farin ciki da walwala shi ke taimaka musu wajen samun ingantacciyar lafiya .

Kaga fadan da ka mata yanzu,ba  abunda baze iya janyo mata ba Maanch saboda tsoro ko tashin hankali da ta shiga ciki .

Ba ita kadai ba,hatta babyn ze iya zama affected.

Gashi ko ita a kan kanta ma ba son wannan haihuwar take ba Maanch,tace mun wallahi har kunya take ji yadda take haihuwa,kan ta yaye ta samu wani cikin.

A kan kanta tana so tayi planning tun haihuwar ta ta biyu,amman baban su Aslam yace in tayi planning ba da yawun shi ba be yafe mata ba.

Toh a nan kaga ba yadda zatayi Dan kamar an Fi karfin ta ne..

Wallahi har kuka take yi akan wannan cikin se ni ke ta bata hakuri,abun ya dameta as it is,so be kamata a runga Kara mata Wani ba on top of her problems ba.

Gashi kaga bata da karfin yin fito na fito da mijin ta Indai har tana son shiga Aljanna dole se an danne ta Kuma a dole ta hakura..

Ba shine (Arrijalu qawwamuna Alan nisa'i) ba,kaga wannan ma ai Kai zaka jawo mana Gwani na..

Abu daya na sani ni dai,tunda tana gaya mun matsalolin ta,ni Kuma Ina Iya bakin kokarina wajen ganin na bata shawarwarin da zata yi amfani dasu na alkhairi a dai dan iya sani na da nake da shi,Wanda  har za ta iya shawo kan shi ya yarda tayi tsarin iyalin.amman fadan baze yi mata ba har tafi bukatar kulawar ku a kan tsangwamar da kowa ke mata ,ga wasu sunaye da ake Kiran ta dasu Wanda ko ni ma banajin dadin Jin ana Kiran ta da su din ballantama ita..

Harfa Wani iya rututu,ko uwar garke,ga aunty bataliya ake gaya mata..

Ba ma ya Kai da duk cikin ku tafi so Kuma take ji dashi har zuciyar ta,se gashi Kai ne kafi mata fada akan damuwar da ita ma damun ta take yi..

Allah Maanch abun ba dadi,sannan Kuma shi baban su Aslam din baka ga yadda yake kulawa da ita ba yana sonta kam sosai,ni shaida ce Dan abun har mamaki yake bani..yanzu ko a dazu 150k ya Aiko mata yace suje da Yara suci dadin su,at least Yana kokarin ganin cewa ya tsaya musu,ko da wannan ai se yaci darajar haka ko?

KANIN MIJINAWhere stories live. Discover now