Chapter tree

1.3K 46 2
                                    

                 *MAJNOON!!*
              (The innocentmad)

*Writting By*
Fatymasardauna
Wattpad
@fatymasardauna

*(This Book is mainly for those that pay, if you know you didn't pay please don't read it. Here is the account number for people that are willing to pay-0002214625 Abubakar Muhammed Sardauna Jaiz bank. AMOUNT 300. WhatsApp Number 07069917168)*

*Freepage*
                  *Chapter 3*

Idanu Dr. Mouhammad ya tsurawa screen din wayar nasa dake ta faman ruri, tamkar me nazartar wani abu.
Duk da cewar yasan Billonaire DAWOUD Saraki. Bazai kirasa haka kawai ba, lallai dole saida wani abu.
Amma yana tsoron ace masa jikin MAJEED ne ya sake tashi.

Hannunsa ya mik'a da niyar d'aukar wayar, saidai kafun yakai ga d'auka, kiran ya katse.

D'an Jim yayi yana me tunanin bin kiran, saidai sanin da yayi cewar mai kiran nasa, zai sake kira ne yasa shi sauke ajiyar zuciya, tare da fesar da numfashi.
Anutse ya koma kan kujera ya zauna.
Yana me tunani  acikin zuciyarsa, ta yanda zai sake fuskantar matsalar MAJEED.

Idanunsa da suka dan kawo ruwa, ya lumshe saboda tunowa da wasu abubuwa da yayi.


Acan waje b'angaren su Soumaya kuwa har yanzu babu wani wanda yayi kyakkyawan motsi, daga cikinsu haka kuma babu wani wanda yake cikin yanayi mai dad'i.
Sai Moudou wacce ta k'osa da komawarta gida, saboda duk tagaji da zaman asibitin, gashi kuma har yanzu basu san awani Hali Abboun yake ciki ba.

"Idan ya mutu ne ai sai sufito suce ya mutu."

Ta fad'i haka acikin ranta tana mejan tsaki kasa kasa, tare da wurgawa Soumaya harara, wacce ta cusa kanta acikin tsakankanin cinyoyinta.

Gaba d'aya jin duniyar takeyi babu dad'i,  acikin zuciyarta kuwa, ak'agare take da sanin halin da mahaifinta ke ciki.

K'aran sautin takun takalmin da taji acikin kunnuwanta ne,  yasa ta d'ago kanta, tare da kallon inda takejin sautin takun, da kumburarrun idanunta.

Ganin Doctor'n d'azu da tayi yana  kokarin k'arasowa garesu ne,  yasa ta zuba masa ido, domin hakanan taji zuciyarta na bugawa tamkar zata faso kirjinta ta fito.
Bata fatan jin wani mummunan labari daga bakinsa.
Dan tayi imani cewa jin hakan zai iya sa zuciyarta tarwatse wa.

Ganin da tayi har ya kusa k'arasowa garesu ne kuma, yasa ta sanya hannu ta d'an dafe kirjinta, tare da rumtse idanunta.
Saboda batason ji da ganin wani mummunan abu.

"Likita ya ake ciki dai, kodai har yanzu bai farfad'o bane? Ko kuma ya rasu ne kuke b'oyewa?"

Moudou ta jefowa likitan tambayar, da yasa zuciyar Soumaya rugurgujewa, sannan yasa jinin jikinta daskarewa.
Saboda tambayar da Moudou'n tayi ne kuma, yasa bisa dole ta ware idanunta tana kallon likitan, zuciyarta cike da fargaban amsar da zai bawa Moudou'n.

Dr. Hafiz wanda shima yana d'aya daga cikin manyan Doctors din dake cikin asibitin, kallon Moudou yayi cike da mamakin irin tambayar da tayi masa.
Saidai kuma rashin sanin wace ce ita awajen marar lafiyan, yasa shi kawar da mamakinsa, kamar kuma yanda yakasance acikin tsarinsu akwai iya tausasa harshe, da kuma samawa mutane nutsuwa hakan yasa shi, girgiza kai kana cikin kulawa yace.

"Calm down patient dinku zai samu lafiya Insha Allah, domin munyi nasarar ceto numfashinsa, sauran bayani kuma zakuji shi ne daga bakin, Dr. Mouhammad, zaku iya zuwa ku sameshi a office yanzu."

Ya kai karshen maganan yana me nuna musu, hanyar office din Dr. Mouhammad Boulama.

K'akk'arfar ajiyar zuciya mai tafiya da k'warin guiwa, da kuma sanyin zuciya Soumaya ta sauk'e.
ahankali kuma siraran hawaye masu sanyi suka Zubo daga cikin idanunta.

MAJNOON!Where stories live. Discover now