BABI NA BIYU

86 10 10
                                    

_*FIKRAH WRITERS ASSOCIATION*_

*RABON AYI*

*©FAREEDA ABDALLAH*

2)

Kafin Fatima ta ce wani abu ɗaya daga cikin hamshaƙan matan da suke zaune can wani ɓangare na falon ta miƙe tsaye a fusace ta kalli tsigaggiyar nan ta fara maida mata martanin maganganunta cikin fushi
"Wai wane irin zancen banza kuke yi haka? ku kalle mu nan mun ci, mun sha, mun rufa mun tada kai balle har ayi tunanin za mu gani mu ɗauka. Sata dai? in dai da gaske ne anyi satar to kuwa na tabbata ko rantsuwa nayi babu kaffata ɓarauniyar baza ta wuce a cikin ku ƴan'uwanta na jiki-jiki da kuke zaune a cikin uwarɗakinta ba..."

Maganar da tayi sai ya zama kamar mabuɗin bakin ko wace mace da take zaune a falon, nan take aka fara cece-kuce da ƙananan maganganu, wannan figaggiyar tana masifa ana maida mata martani, ko wacce mace na ƙoƙarin kore gaskiyar zancen anyi satar balle har a maƙalawa ɗaya daga cikinmu mazauna falon.

Aminiyata Fatee ta gallah min harara, ta fusge hannunta daga cikin nawa, cikin fushi da ƙarfin hali ta fara min magana da faɗa-faɗa.
"Ke dallah banza ki nutsu ki kwantar da hankalinki, to miye don ba'a barki ba kika fito? kanki farau satar fita? da wannan mutsu-mutsu da zare-zaren idon da kike yi ai sai ki zama abar zargi a cikin mat..."

Wani mahaukacin ƙaƙƙarfar ihu mai cike da amo da amsa kuwwa da aka ƙwallah daga cikin ɗakin uwar bikin yasa kusan duk mazauna falon muka miƙe tsaye a tsorace, tsit kake ji duk hayaniyar mata ya tsaya cak kamar ɗaukewar ruwan sama.

Hankalinmu bai ƙara mugun tashi da ɗugunzuma ba sai da wannan ƙatuwar da aka kira da Aunty Kubura ta fara jero sallallami tana tafa hannaye haɗe da cewa
"Shi ke nan! Ta faru ta ƙare anyiwa mai dami ɗaya sata. Abinda muke gudu ya faru. Mugayen aljanun Aunty Adama ƙanwar Hajiya Mariya sun tashi. Wallahi duk wacce tasan ta ɗauki jakar nan ina bata shawara ta fito salin-alin sawunta a likkafa tun kafin a fito da ita a tozarce a wulaƙance.

Don wallahi aljanunta ƴan fallasa ne, kuma duka suke yi, idan suka zuciya ba ruwansu, kan mai uwa da wabi suke yi da wacce taji da wacce bata gani ba su haɗa su jibga..."

Kayan cikina ne suka tattaru suka cure guri ɗaya, lokaci ɗaya jikina ya ɗauki rawa kamar ana kaɗa min ganga, hanjin cikina sai mazari suke yi kamar ana tsakiyar hunturu. A ƙanƙanin lokaci idanuna suka cicciko da hawaye, sai ga su sun zubo shar...

Na kalli Fatima ita ma ta kalle ni, a wannan gaɓar ƙuru-ƙuru na hangi matsanancin tausayina a idanunta, domin ta san Mugun tsoro ne da ni, na tsani aljanu, na tsani tashin aljanu a gabana, tun ina ƴar ƙanƙanuwar yarinya duk idan naji labarin wata wacce na sani tana da aljanu ni da ita haihata-haihata.

Ko a cikin dangi ne nakan guje ta faufau balle kuma a cikin ƙawaye ko kuma ƴan ajinmu, a islamiyarmu na canza aji fiye da sau biyar saboda tsoron tashin aljanu.

Kafin wata a cikinmu tayi wani yunƙuri don motsawa ko cewa wani abu sai muka fara jin buge-buge daga cikin ɗakin kamar ana watsi da kayayyaki, ko kuma ana mugun dambatuwa, can sai kuma muka ji an sake yanka ƙaƙƙarfar ihu a karo na biyu, sai ga wata gajeriyar mace mai kama da wada wacce da alama ita ce Aunty Adama ta fito falon a guje daga cikin ɗakin, daga ita sai shimi a jikinta, ƴan uwanta suna biye da ita da gudu suna yunƙurin riƙeta, fuskokinsu cike da maɗaukakin damuwa.

Abin mamaki da tsoro Aunty Adama tana zuwa kusa da ƙafafuna ta zube ƙasa kirif, takai wa ƙafafuna wani mugun damƙa da wawaso da yasa nayi taga-taga kamar zan faɗi sai na damƙi ƙugun Fatima da take kusa da ni, Aunty Adama kuwa ta riƙe ni ƙafafuna tamau, tsananin tsoro da firgici yasa na ƙame a tsaye kamar wata mutum-mutumi.

Sama-sama nake jiyo ringing ɗin wayata a cikin jaka tana rera waƙar
"Fareeda gimbiya..."
Ringing ɗin da idan na ji ta na tabbatar mijina Mukhtar ne yake kira na...
'Na shiga uku!!!'
Na ayyana hakan a zuciyata wasu sabbin hawaye suka sake ɓalle min kamar an buɗe famfo.

A Fusge kamar daga can nesa naji muryar wata mata tana cewa
"Baiwar Allah ki nutsu, ki kwantar da hankalinki. Da alama aljanunta suna son ki ne..."

Ƙaƙƙarfar kukan da na buɗe baki na fashe da shi yasa mai maganar ta kasa aje numfashin maganarta daidai.
'So dai? aljanun ne suke so na? ni kam yau wace irin mummunan rana ce a gare ni?'

_Wannan gajeren labari ne don faɗakarwa da nishaɗantarwa, shi yasa za kuga pages ɗin gajejjeru🤣. Tukwuicin da za kuyi min shi ne ku tura wannan labarin aduk wasu groups na novel da kuke ciki domin sauran mata su ilmantu. Domin sharhi, ƙorafi, shawarwari a tuntuɓeni ta private a lanbar wayata 07039080978🥰_

RABON AYIWhere stories live. Discover now