BABI NA UKU

129 10 2
                                    

*_FIKRAH WRITERS ASSOCIATION_*

*RABON AYI*

*©FAREEDA ABDALLAH*

*3)*

'So dai? aljanun ne suke so na? A duniya in rasa suwa za su so ni sai aljanu? ni kam yau wace irin mummunan rana ce a gare ni?

_'Fareeda kar ki tafi gidan bikinnan, in dai ni mijinki ne kuma na isa da ke ban baki izinin ki tafi gidan bikinnan b..._'

_'Haba Baby haba haba don Allah? me yasa kake irin haka ne wai? Jiddah ce fa za tayi aure ba wata ƙawata can nesa ba. Fisabilillahi duk yadda muke da Jiddah ace bikinta ya zo bazan samu halarta ba? haba ai duniya ma sai ta zage ni, ka tuna yadda tayi uwa tayi makarɓiya a bikinmu..._

_Ni na sata dole tayi? na dai faɗa miki kar ki fita ko ina, gobe zan dawo. Idan kuwa kika fita wallahi tallahi duk abinda nayi miki ke kika jawo wa kanki. Domin a wannan karon zan ɗauki mummunan mataki a kanki. Ƙit ya katse wayar ba tare da ya sake sauraren abinda zan ce ba._

A cikin ɗan taƙaitaccen lokaci taƙaddamar da muka kwasa da mijina Mukhtar a ɗazu da safe ya faɗo min arai, da yake ni ɗin mai kunnen ƙashi ce tsautsayi da rabon ayi yasa nayi fatali da hanawarsa, kashedinsa, rantsuwarsa nayi fitowata bayan ƙawata Fatima ta shirya ta biyo min har gida da direbanta.

"Baiwar Allah kiyi haƙuri, kibar kuka, yanzunnan za mu ɓamɓare hannuwanta daga jikin ƙafafunki, ki nutsu, kiyi hakuri babu abinda za tayi miki."
Ɗaya daga cikin ƴan uwan Aunty Adama ta faɗa min haka, da sassanyar murya mai ɗauke da alamun rarrashi don kwantar min da hankali.

Sannan ta kalli matan suke tsattsaye cirko-cirko a falon ta buɗe murya ta ce
"Ina Hafizai mahaddata Alƙur'ani? ku marmatso kusa da ni kuyi aikin lada"
Sai tayi zaman dirshan a gabana tayi basmala da zazzaƙar murya ta fara rero karatu cikin suratul-baƙarah.

Tsoro ne ko kuwa rashin iya karatun ne oho! a cikinmu babu wacce ta tayata karatun, sai zazzaƙar muryarta ne ya ci gaba da ratsa dodon kunnuwanmu cikin wani daddaɗan saut da iya ba ko wace kalma haƙƙinta.

Bata yi mintuna bakwai cikakku tana karatun ba naji hannuwan da sukayi ram da ƙafafuna sunyi sanyi laƙwas, ina motsawa naji zan iya janye ƙafafuna ai a saba'in na matsa can gefe guda ina zazzare idanu kamar wacce tayi ƙarya a gaban sarki, sai kallon Adama nake yi da wani irin kallo mai bayyana tsananin tsana da ƙyama, a zuciyata babu abinda nake ja mata sai Allah ya isa na firgici da tashin hankalin da ta ƙara jefani a ciki, a daidai wannan lokacin na tabbata da za a auna jinina za aga ya hau.

"Alhamdulillahi! Yau an taki sa'a, sun jirge da gaugawa."
Uwar bikin ta faɗi haka fuskarta na bayyana matsanancin farin ciki, wani abu a cikin kwalba mai kama da magani ta miƙawa wacce tayi karatun tana faɗin
"Ungo nan Aliyah, yi sauri ki shafa mata a goshi, idan tayi barci ta tashi za ki ganta garas kamar ba ita ba."

Ana gama shafa mata suka yi kama-kama tana layi kamar wacce tasha ta bugu suka kaita cikin ɗaki, sannan suka dawo cikin falon.

Umarnin zama suka mana sannan wannan wacce tayi Ruƙya ta fara mana nasiha tana janyo ayoyi da hadithai, a ƙarshe ta dire da haɗamu da girman Allah da na ma'aki kan duk wacce ta ɗauki jakar nan ta dawo da shi cikin mutunci da lalama ba tare da anyi tsiya-tsiya ba.

Hajiya Mariya ta ƙara da cewa
"Ni wallahi ba kuɗin jakar ne ma yafi damuna ba, akwai wasu muhimman takardun His Excellency a cikin jakar! I'm sorry to say idan ba'a ga jakar nan ba gaskiya daga nan sai dai a kwashe mu zuwa station din gidan gayu..."

Da rarrafe na ƙarasa gabanta saboda tsananin tashin hankali
"Hajiya... don ya rasulillahi ki rufa min asiri kamar yadda Allah ya rufa miki. kin sanni tun ba yau ba wallahi bazan taɓa ganin abin wani in ɗauka ba. Ki min rai ki sallameni in koma gida, bikinnan ba da izinin mijina na taho ba, ga shi yayi min saƙo yanzu haka yana hanyar shigowa kaduna. Idan ya dawo ya tarar bani a gida na mutu kawai, na tabbata a zafin rai da rashin hakuri irinna Mukhtar igiyoyin aurena da suke hannunshi tsaf zai tsittsinka su..."

"Kiyi haƙuri Fareeda, a al'amarin sata irin wannan kowa ma abin zargi ne, kinga har ƙannaina ban cire su a cikin ɓarayin ba."

Tsabar tashin hankali yasa ban ankara da waya take dannawa a hannunta ba sai da naji tana cewa
"Hello... Inspecter..."

*_Assalamu alaikum Ƴan'uwa😍 Ina neman afuwarku bisa jinkirin posting ɗin babi na uku, hakan ya faru ne saboda wasu ƙwararan dalilai da suka sha kaina. Domin gyara, sharhi, ƙorafi, shawarwari a tuntuɓeni ta private a lambar wayata. 07039080978,_ _pls ku yaɗa wannan labarin aduk wasu groups na novels da kuke ciki😘_*

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jan 21, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

RABON AYIWhere stories live. Discover now