Page fourty-Four 44

372 45 3
                                    

🌕🌕🌙

                  🌕LELEWAL🌕
              🦋FARIN WATA🦋

                                                     🌕🌕🌙

STORY AND WRITTEN BY:- Fatima Muhammad Gurin.

MARUBUCIYAR:-
ZUHRAA
HAMRAH
IGIYAR RAYUWA
NOOR IMAAN and
RUWAN SAMA.

FOLLOW ME ON WATTPAD @Gureenjoh6763

SADAUKARWA:- wannan littafin gabad'ayanta sadaukarwace gareku @68Billygaladanchi wato Anty billy and my dearest sister haneefah Muhammad Gurin thanks for your Advices and support Allah ya bar kauna.

JAN HANKALI:- Toh masoya na ga ni da sabon labari kaman yadda kuka dad'e kuna tsumayi, am not perfect but I promise to give you all my best on this, akwai tufka da warwara masu matukar sarkakiya a wannan labari. Kaara d'aya zuwa biyu nake bukata daga gareku please ku Nuna min jin daad'inku ta hanyar comments and share ta yadda ze karad'e ko ina, wannan littafi kyauta ne domin jin daad'inku masoyana. Na gode🥰🙏.

EXQUISITES WRITERS FORUM 📝
(Home of exquisite writers')

    Godiya ta tabbata ga Allah me kowa me komai.
—————————————————————————

🅿️..........44

Ko da Aadil ya dawo samun yayan nashi na bacci yasa ya ajiye karamar trolley da ya had'o mishi gefe, be zauna ba se safa da marwa da ya fara cikin tsantsar damuwa, me yasa ne kam wai se shi? Me yasa baze ji daad'in rayuwa kaman kowa ba? A hakan haramun ne don ya auri bilkees? Ba fa abinda ze rageta dashi, har Alkawarin Bata farin ciki fiye da kowanni miji a duniya yayi wa ubangiji, me yasa basheer ke so se ya wargaza mishi sauran rayuwar da yake kakkamtawa? Vibration na wayanshi ne ya dawo dashi daga duniyar tashin hankalin da yake ciki, kallon gadon yayi se lokacin ya tuna ashe nan ya bar wayan ya tafi, da sauri ya d'aga kar ya tashi Aayan da be san already ya tashi ba tun shigowarshi d'akin.

"Dr. Basheer" ya gani rubuce fuskan wayan, karkata kai gefe da gefe yayi idanunshi na cika da kwallah, zuciyarshi ba abinda yake se bugawa, d'agawa yayi cikin muryar gajiya yace
"Basheer Farin cikina ne baka so ko? Sauran rayuwar tawa kake so in karar cikin kun ci ko?"

Yadda ya sanyaya murya yasa basheer sauke ajiyar zuciya, ya lumshe ido tare da furta
"Sam Aadil ba farin cikanka ne bana so ba sede na fi son farin cikin bilkees fiye da naka, ta sha wahalar rayuwa ba kad'an ba ya kamata ace at least ta samu dawwamammiyar farin ciki a gidan auren ta, ya dace kuma In har tsakani da Allah kake sonta you should let her go sbd disabilities Dinka"
Kallon Aayan yayi ganin har lokacin be motsa ba yasa yace "I'm coming to your office, maganan da zan yi da kai yau shine na karshe akan bilkees Basheer"
Daga nan ya juya ya fita, da ido Aayan ya bi Bayan shi yana wani nazari, ba tare da second taught ba ya dira daga kan gadon ya bi bayanshi, har office d'in basheer daga kofa ya tsaya tare da kasa kunne inda Allah yayi shi me kaifin ji hakan yasa yake jin maganganun nasu rad'as, tun suna yi a hankali har Aadil ya fara d'aga murya cikin muryar kuka, a lokacin da abinda suke magana akai ya shiga kunnen Aayan be san jiri ya kwashe shi ba, se ji yayi yana niyyar zubewa kasa cikin zafin nama ya dafe gini, bibbiyu ya fara gani sbd wani irin sarawa da kanshi yayi, da sauri cikin kuma karfin hali ya nufi komawa d'akin shi daddafe da gini, a gado ya zube yana sauke numfashi dake son fisge mishi.
"Innalillahi wainna ilaihi rajiun" yayi ta nanatawa tun yana yi a zuciyarshi har ya fito fili, gabad'aya ya rud'e ya rasa tunanin wa ze fara Bilkees ko Aadil?
Me ze faru idan ya yi Shiru?
Runtse idanunshi yayi da karfi, idan har yayi shiru tabbas bilkeesu zata fi cutuwa, ya mata adalci kenan? Idan yayi magana kuma kaninshi ba karamin cutuwa ze yi ba After all wahalhalun rayuwa da ya sha, wata zuciyar tace to ita bilkeesu bata sha wahalar rayuwa bane?.
Ya mata rashin kyautawa a farko yanzu be dace ya kuma ba sbd idan har hakan ya faru ba zata ta'ba yafe mishi ba....

🌕LELEWAL🌕(Farin wata)Where stories live. Discover now