Page Fifty 50

458 53 7
                                    

🌕🌕🌙

                  🌕LELEWAL🌕
              🦋FARIN WATA🦋

                                                     🌕🌕🌙

STORY AND WRITTEN BY:- Fatima Muhammad Gurin.

MARUBUCIYAR:-
ZUHRAA
HAMRAH
IGIYAR RAYUWA
NOOR IMAAN and
RUWAN SAMA.

FOLLOW ME ON WATTPAD @Gureenjoh6763

SADAUKARWA:- wannan littafin gabad'ayanta sadaukarwace gareku @68Billygaladanchi wato Anty billy and my dearest sister haneefah Muhammad Gurin thanks for your Advices and support Allah ya bar kauna.

JAN HANKALI:- Toh masoya na ga ni da sabon labari kaman yadda kuka dad'e kuna tsumayi, am not perfect but I promise to give you all my best on this, akwai tufka da warwara masu matukar sarkakiya a wannan labari. Kaara d'aya zuwa biyu nake bukata daga gareku please ku Nuna min jin daad'inku ta hanyar comments and share ta yadda ze karad'e ko ina, wannan littafi kyauta ne domin jin daad'inku masoyana. Na gode🥰🙏.

EXQUISITES WRITERS FORUM 📝
(Home of exquisite writers')

    Godiya ta tabbata ga Allah me kowa me komai.
—————————————————————————

🅿️..........50

Kamshin shi ne ya fara karad'e parlorn kan bayyanarshi cikin dakakken shadda fara sol da ta ji kud'i da d'inki irin na manya, walwala ne kwance fuskanshi, idanu ya zuba mata kaman yadda itama ta zuba mishi nata d'an ta'be baki yayi kan ya maida idanunshi kan Zaheera dake kuka bilhakki da gaskiya akan kafan uwar, shugabar 'yan aikin gidan ce tsaye da wasu masu aiki biyu da suka taimakawa ummu zaheerar ta farka.
  Direct gaban Tv ya isa ya d'auki remote ya kunna shi, daidai yana kan gotel ta'be baki yayi se kuma ya juyo ga ummun yace

"Zaki iya barinshi nan, za kuma ki iya kaiwa ABC ko ma NTA yola duk abu d'aya ne na san ze kasance heading d'insu nan da anjima kede kar ki kauce kina da bukatar ganin hakan... ya ma?"
Yayi wa kanshi tambayar yana kallon sama se kuma ya saki murmushi yace "Yauwa... ni ni kad'ai ce gidan nan dan haka namiji be isa yiwa 'yar cikina kishiya ba sbd Bata tashi ta gani a gidansu ba.... right? Did I said it Exactly ko akwai gyara ne?".
Cikin rashin fahimtar d'abi'unshi na yau tace
"Me ke faruwa ne your excellency? Wani abu ya faru tafiyar da kayi ne?"

Girgiza kai yayi yana kallon zaheera dake kallonshi hannunshi hard'e a baya yace
"Ko d'aya fah... yanzu dae banda time in na dawo zaki iya tambayar da kike so, Miss Rebecca..!"
Cikin tsantsar ladabi tace
"Yes your excellency"
A kausashe yace
"Ina me bada umarni a d'auke duk wani ma'aikaci dake sashen First Lady da zaheera ki tabbatar baki barsu da maid ko d'aya ba, this is an order"
A ladabce tace
"Ohk Sir"
Daga haka ta juya da sauri, sauran ma bayanta suka bi don cika umarni har ransu daad'i suka ji za'a rabasu da waennan masifaffun musamman ma zaheera da take azabtar dasu.

Ummu ta kauda zaheera dake kan kafanta a fusace ta sha gabanshi tace
"Ahmad me kake nufi ne?"
Yana murmushi yace "mene? Tambayata kike?"
Ajiyar zuciya ta sauke tace
"In don zaheera ce ya kamata ka tsaya ka sauraremu kan ka yanke hukunci, this is not fair taya zaka bada goyon bayan cin amanar 'yarka? Taya don mijinta ba mutumin kirki bane daga barinta gida se ya jaji'bi aure? Ba tare da amincewarta ko saninta ba?"
Karamar dariya yayi sbd yau yana cikin nishad'i yace
"Ashe aure ya zama cin Amana? Mijin da ya kara aure ya zama mutumin banza? Toh fah ki shirya mutanen banza kam yawa ne dasu"
Daga haka ya zagayeta ya wuce bayan ya kalli agogon dake d'aure hannunshi.
Ajiyar zuciya ta sauke kan ta nufi zaheera
"Wai ke kam wace irin mace ce? Sbd banza namiji shine zaki zauna kina wannan kukan kaman ni aka ce miki na mutu? He should go to hell and burn to ashes, idan kina wannan kukan ne ma ze ji daad'i ya nunawa duniya yayi nasara a kanki"
Cikin kuka tace
"Ummu kin san bilkeesun kuwa? Ummu Kinga kyaunta? Shegiya munafuka ashe mijina take hari? 'Yar aikina fah ni Aayan ze tozarta ya had'ani kishi da 'yar aiki?"
Se kuka, lallashinta ummu ta ci gaba dayi cikin tunanin hukuncin da ya kamata su d'auka kan Aayan inda matsalar take ta gama fahimtar Aayan ba son zaheera yake ba, kawai dae ana zaune ne don mutunci, wannan ya sakata wani tunani cikin ko In kula tace
"Zaheera to ki rabu dashi mana, dole ne auren ga maza dayawa a gari 'ya'yan manya masu hannu da shuni, zaki tsaya yana wulakantaki a banza yana auro miki er aikin gidanki?"
Wani dariyar takaici tayi tace
"Ummu In rabu dashi fah kikace? Uhmm ummu you are not serious" daga haka ta mike ta fice fuuuuuu

🌕LELEWAL🌕(Farin wata)Where stories live. Discover now