💎💎💎💎💎💎💎💎💎
💎💎💎💎💎💎💎💎
*ITACE SILAH*
      📲(wayar Android)📲
     ~*it based on True life story*~
💎💎💎💎💎💎💎💎💎
💎💎💎💎💎💎💎💎
💎💎💎💎
💎💎💎
💎💎
💎

*Labari da rubutawa*:Faridat Husain Mshelia(Ummu-Jidda).

*FREE PAGE*
shafi 10 zan yi na kyauta Dan haka kuyi kokarin biyan na ku Dan littafina na kudi ne ga duk mai bukatar siya yana iya tuntubar wannan numbar.   0815 314 4521 ta  hanyar turo min katin 200👌🏻na Glo ka yi screenshot ka turamin ta WhatsApp zan yi adding na ka\ki to the group ,group din maza daban na mata daban.

*Wannan shafin na ki ne Maman Ameera ta Mshelia's Hausa novels tabbas kin nuns min kauna ta hanyar siyan littafin nan da kudi mai rahusa Allah ya bar soyayya*

*SHAFI NA UKU*

Jagwab  ta zauna ta na jin tamkar ta kwarara ihu dan tsabar tashin hankali,ji ta yi hawaye ya daina kwarara a idon ta tsabar kunan zuciya da toshewar kwakwalwa,zufa ke tsatstsafo mata ta kowani mashigar gashi na jikin ta,

dan haka ta fara tunanin da ya sa kan ta shirin tarwatse wa,

"Tabbas yau na shiga 3" zuciyar ta ya nakalto mata" na tabbatar ba zan kara rayuwa cikin jindadi ba matukar na damka ma kamshi ragamar rayuwa ta,Amman bai kai hatsarin rabuwa da gudan jinina ba(mijina)Dan shine mabudin farinciki na"matukar ya San mai na ke aikata wa tabbas zai rabu dani,rabuwa irin na wulakanci Wanda ba na fatar ace masoyi na yayi mani irin wannan tsanar,

"Amma mecece mafita?

"Yaya zan yi?

"wani hanya zan bi dan kauce ma rayuwa cikin inuwar Rashida kamshi?"

"Nabeel shine kadai Wanda zan samu wannan amsar daga gurin shi Amman yau na San baxai saurare ni ba tunda nasan yaga abinda na muka aikata ni da kamshi,na San shi na kuma San halin shi,mutum ne mai matukar kishin jaraba Sam ba zai saurare ni ba wayyo Allah na!!!ta dafe kan ta hade da rushewa da kuka ta shafe fiye da awa 1 tana Abu 1 ganin kuka baya magani ya sa ta fara rarrafawa domin ta dakko wayar ta daga kan gado ganin hakan ya gagara yasa ta dinga Jan gindi har ta cimma wayar,

rawa hannun ta ya shiga yi zuciyar ta na bugawa jin yana ringing Amman har ya katse ba'a dauka ba, daman ta San za'a Rina wai an tsinci zanin mahaukaciya Nabeel da kishin masifa balle ya ga zahiri canza shawara ta yi dan haka ta mike tana layi har ta samu ta shige cikin bandaki.

wankan tsarki ta fara gabatar wa hade da dauro alwalla dan tana ji ajikin ta lokacin sallah ya Dade da wucewa,nan ta gabatar da sallan azahar tare da yin kukan nadama cikin sujjadar ta na karshe,tana cikin addu'a ta ji sallamar yaran ta da suka dawo daga makaranta,

Nan tabbatar da 3 ya yi ga shi  ko girki ba ta daura ba ,sannu da gida su ka yi mata nan suka fara kokarin cire kayan su tana taimaka musu jikin  ta Sam ba dadi,kudin da rashida ta ajiye mata ta Kalla nan ta xari dubu 1 aciki ta aika aka siyo ma yaran soyayyen dankali dan ba ta jin za ta iya girki,ba ta d'aga daga in da ta ke ba sai da ta sallaci sallar La'asar nan wani wahalallen bacci ya yi awon gaba da ita cike da munanan mafarkai.

*NABEEL*
Wanda ya samu ya lallaba ya fita daga zauren Gidan su kai tsaye majalisar da ya San zai sami abokin shi Farouq ya tafi tun daga nesa ya hango mazaunin abokin na shi wayam yasan cikin biyu za'a yi 1 ko dai yana can yana sana'ar ta shi a gida ko kuma bai dawo daga kodago ba,dan haka ya juya akalar tafiyar ta shi zuwa dakin shi Inda tun daga nesa ya tabbatar da yana ciki jiyo sauti na tashi tamkar zai ta da gurin,da karfi yake dukan kofar har yaji an bude a zuciye irin an takura Wanda aka ziyarta Amman ganin Wanda ke bugun  ya sake fuska,

"ya dai baabah na gan ka a yamutse ko abin ne ya motsa in bar maka chikar da na samo yau"ya furta hakan yana mai miqa mishi hannu su ka yi musabaha,girgiza mishi kai ya yi alamun "a'a" bayan ya kai duba kan katifar shi wanda mace ke kwance jikin ta babu maraba da tsirara,dauke kan shi yayi daga gareta cike da damuwa yace"Rancen kudi na zo nema ina son zuwa Suleja da yamman nan in zan samu"

"Ahhh ka ce yau masoyi zai hadu da masoyiyar shi,za'aci dadi asha dadi,ya furta yana mai kashe mi shi ido irin na tatattun yan iska,

"Amman ya na ga your not happy at all?ko wani ne ba lafiya?

"kowa kalau, ya amsa a takaice Dan  ya matsu ya juya ya tafi,

"kai dai zan samu ko kuwa?"

Za ka samu Amman meyafaru? me yasame ka?

Dafa shi ya yi ganin yanda idon shi ya kada ya yi jajur tamkar zai yi kuka yace ,

"ka fada min pls Share your problem with me, half will solved insha Allah"

Nuni ya yi mishi da budurwan shi da ke kwance duk ta kosa su gama ta ji ta tare da shi ya mishi alamu da ba zai iya fad'in maganan a gaban ta ba,

Dogon wandon da ke yashe a k'asa ya dauka ya sa dan haka su ka fice waje.

A wulakance shu'uma ke bin bayan farouq  da kallo cikin zuciyar ta tana mai son kasancewa da Nabeel Wanda ta yi ma laqabi da "Mr Arrogant"tana da burin mallakar shi ko ta halin qaqa dan kalar namijin da ta ke burin samu kenan,siffar shi da ajin shi sun yi mata,a rayuwar ta tana son namiji mai kirar tsire dan ta tabbatar za ta samu jindadin da ta ke bukata daga Gare shi dalilin hqkan ya sa ta shige ma abokin shi farouq wanda ya kasance mai kwashe-kwashe tun farkon haduwar su da farouq a wajen wani Party  ta ke farautar Nabeel dan a tare ta gan su amman tsare gida irin na Nabeel ya sa ta gagara tunkarar shi,

"ga dama ta samu gare ki yanzu shu'uma yi maza kije ki jaraba sa'ar ki" shaidaniyar zuciyar ta,ta umurce ta dan haka ta mike zumbur rigar kimono na cikin ta sanya da abayar shi akan matsiyatan pant da bra da ba su da maraba da babu ta nannade kan ta da baqin gyale tare da ficewa,

Akan dakalin Gidan su Farouq ta hango su ganin yanda Nabeel ke magana tamkar zai yi kuka ya sa ta gyara takun tafiyar ta tana wani irin karairaya tamkar tarwada hade da turo kirjin ta gaba tana juya mazaunai tamkar mai shirin zuwa gasar tafiya,

"Ya dai Baby?"

farouq ya furta hakan yana mai taryo ta, dan bai son ta tafi ta bar shi a bukace ya ke da ita Sam shu'uma ba kalar Matan da ya ke wasa da su ba ne shiyasa ma bai shayin kawo ta dakin shi rana tsaka dan bai tsoran uban kowa a kan ta,

"I have a lot to do na ga abokin ka kuma needs your attentions so lemme go gobe ma hadu" ta furta hakan ta na mai satar kallon Nabeel cikin wani shu'umin murya da ba ko wace mace ke mallakar shi ba duk dan ganin yana kallon directions din su,ban baki ya fara yi mata tana turjewa Wanda hakan ya tilasta ma Nabeel mik'ewa dan shi ba ya daukar raini a rayuwar shi yace"ka ga Malam in zan samu in  kaba ni in wuce dan dare na yi, ni ba kasafai na cika daukar iskanci ba"hararar shi farouq ya yi tare da zarar ATM card daga aljihun shi ya mika mishi gashi can katafi da jarabar ka mutum sai masifa da zuciyar banza sai kace kuturu,kwafa ya yi ya juya yana takun fad'i yi yayi tamkar zai tashi sama tsabar hands zuciyar ke azalzalar shi ga haushin yanda farouq ya mai da kan shi namamajo da take yi dan shi Beelah CE kadai macen da Allah ya jarabce shi da kaunar ta  da gaskiya duk da ya San Matar aure ce wacce ta hayayyafa kuma ba su tab'a had'uwa face to face ba sai  dai ta "WAYA",duk mata kallon sakarkaru ya ke musu saboda yanda suke masifar son shige mishi wasu har makudan kud'ad'e su ke ba shi domin ya tara da su Amman shi ba kasafai ya cika son shige ma mata ba Beelah CE kadai ta ciri tuta.

Galala Shu'uma ta bi bayan shi da kallo cike da shaawa dan ita komai na shi burge ta ya ke yi,kama daga tafiyar shi maganar shi,kwalisar shi da yanayin yanda ya ke shashshare mata shi ya fi sa ta ta ji shi a zuciyar ta, saukar hannun farouq cikin na ta shi ya dawo da ita daga tunanin da ta tafi cikin son basarwa ta fisge hannun ta tare da wuce shi a hanzarce.

*Har free page din ya ishe kune na ga bakwa comments sosai Facebook fans?in kun gaji in daina turowa nagode masoya*


*Ummu-Jiddah*

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Feb 03, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

 ITACE SILAH(Wayar Android).Where stories live. Discover now