*RAYUWATA*
*WRITTEN*
*BY*
*AYSHA ISA (Mummy's friend)*
*Vote me on wattpad @ AyshaIsah*
_____________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com*A TRUE LIFE STORY*
_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_
_*Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin halittu wanda ya bani ikon sake zuwa maku da wannan labarin. Ina rokon Allah ya bani ikon rubuta abinda zai amfane mu baki d'aya*_
_*Kamar yadda kuka gani a sama wannan labarin ya faru ne da gaske, dai sai sunaye da bambanci gari, sai wani ƙarin da zai sanya labarin ya ƙara armashi.*_
_*Banda yarda wani ko wata ta canza mani labari ba, don haka a kiyaye.*_
PAGE 1Sa'if! Sa'if!! Sa'if!!! Oh ni Hunaisah wai Sa'if ba ka jin ina ta kwala maka kira ne?.
" Na'am Mummy..." Sa'if ya amsa yana mai ƙarasowa inda nake, " Mummy gani" yace bayan ya iso.
Allah ya shiryar min da kai Sa'if, wato sai yanzu ka gama daman amsa ko?.
"Ayyah Mummy ina fa toilet ne, shi yasa kika ji ni shiru. Am sorry love" ya ce cikin kalar tausayi.
Bakomai Sa'if, daman so nake kazo suje can family house ɗinku da Aunty Ubaidah ku amsa min flask da zan zuba abinci gobe.
" Ok Mummy bari naje na kira Aunty Ubaidah sai mu tafi yanzu don Malam ya ce zuwa 4:00pm kawo yana islamiyya" Sa'if ya ce sannan ya nufi idan ƙannena da matar ƙanina, sannan matar cousin brother na ke zaune suna inkar alaiyahu, gaida su yayi, suka amsa cikin sakin fuska.
Ɗaya daga cikin ƙannena sai suna Fa'iza tace " angon walima yau babu islamiyya ne?"
"Akwai anty amma sai 4pm aka ce mu zo" Sa'if ya bata amsa cike da girmamawa.
"Ok toh, Allah ya taimaka" cewan Sumayyah.
"Ameen" cewan Sa'if sannan ya cigaba da faɗin " Aunty Ubaidah Mummyna ta ce wai ki rakani family house ɗin mu, mu amso flask da za'a zuba abinci gobe."
"Ok muje" Ubaidah ta ce ta karkaɓe hannunta.
Ɗakin ta nufa ta ɗauko hijabi sannan suka nufa inda aka aike su.
Wani irin ajiyar zuciya ta ja ganin inda gidana yake cike da juma'a tun a yau, duk domin tayani murna wani ɗan tilo wanda zai kasance gobe. A gaskiya idan nace ban gobe ma Allah ba nayi butulci, domin ƙannena da na nesa da kusa duk sun zo, mazajen kuma sun wakilta matayen su domin ba duka zasu samu ikon zuwa ba, ga kuma makwabtana da suma ba'a barsu a baya ba, amma wani abun mamaki babu wanda yazo daga cikin ƙannen mijina don tayani aiki, illa matar ƙaninshi kawai da tazo duk da kuwa naji ance hatta ƙanwarshi dake aure a wani gari can dabam tazo amma har yanzu babu wanda ya tako gida. Allah nagode maka da ka bani 'yan uwa da makwabtan arziki da yau ban san inda zan yi ba, miƙewa na fito daga daki don dama maggin da za'ayi amfani dashi naje ɗauka, na dawo naki gurin da ake girki don baƙin da suka sauka ɗazu.
Mutanen sai hada hada ake babu wanda ya zauna, masu yin zobo nayi, masu kunun zaki nasu, masu shara nayi, kai kowa dai da abinda yake domin babu wanda ya yi zaman banza.
Sa'if kuwa tun ɗazu suka dawo, tuni na saka shi ya shirya ya tafi islamiyya. Haka dai sisters ɗina suke da tsokanata wai ina maida masu yaro kamar ƙaramin yaro duk da yanzu ya kai shekara goma sha uku, nikam wallahi har yanzu yaro nake ganin shi don bani da kowa bayan shi.
Haka dai baki sukai ta sauka wanda suke daga nesa har da ƙawata da muka yi karatu tare amma ba ita ba anan cikin garin Kaduna suke zaune ba tana zaune Udawa wanda wani ƙauye, kafin ita kuma ƙanne da suke Birnin-Gwari duk sun sauka ko.
_________________________________________________________________________________________________________________________
*Gidansu Ma'aruf*
A bangare guda kuwa gidansu Abban Sa'if wato Ma'aruf kenan suma can suna ta fama da tasu hada-hadan duk da Sa'if ya faɗa min cewa ba wani aiki yaga suna yi ba illa kaji kawai da yaga suna gyarawa, kamar dai ba wani gayyata suka yi, tunda dama kawun nashi wanda shi ke matsayin uwa a gareshi ya ce shi ba wani taro zai yi ba domin bai fi wata biyu ya aurar da 'ya ba. A zuciyata kuma faɗi nayi wannan damuwar tasu ce ba nawa domin kuwa babu wanda na roƙa ko taro a gurin shi balle ace na damusu, kuma babu wani daga cikin su da ya bani sile nashi, ban ƙi ba dai ko sun baiwa Ma'aruf ɗin.
Ƙawar shi kuwa Suhaima wacce ta taho daga Udawa bini-bini tana kan waya, inda kuma zata yi wayan sai ta fita daga ɗakin inda sauran yaran kawunta suke ciki kamar dai akwai abinda take ɓoyewa. Koma menene zamu sanin nan gaba.
___________________________________________________________________________________________
Misalin ƙarfe shida ina kitchen ina wasu ayyuka Jamila ƙanwata tazo ta ƙira ni wai Abban Sa'if na nema na, haka ta tafi na same shi a tsakar gida inda yake tsaye don ɗakina cike yake da jama'a.
Bayan mun gaisa, haɗa tambayata ya jama'a, Ma'aruf ya fara bin zance wanda ya sanya na cika da mamaki, bamu gama magana kar saida aka fara kiraye-kirayen magrib. Haka na koma ɗakina cikin sanyi jiki da mamakin da har yanzu na ƙasa dainawa.
Jamila da Hamida ( cousin sister ɗin) na sa Halima (ƙanwata) ta kira min sannan ƙanwar mahaifiyata Inna Jumma wacce dama tana ɗakin zaune, sai ƙasar Karima daba kira daga baya nake sanar dasu abinda Abban Sa'if ya faɗa min.
Babu wacce jikinta bai yi sanyi ba da jin wannan batun. Ana cikin haka ne Ubaidah ta shigo ɗakin tambayata kafin ma ta kai da magana a koreta a ɗakin dama kuma Sumayyah ce ta aiko ta, komawa ta yi ta ce " Aunty Sumayyah ina jin kamar akwai abinda ke faruwa, don ban ma kai ga faɗin abinda kika aiken ba Inna Jumma ta koreni."
"Toh! Allah dai yasa lafiya, *meke faruwa*?. Bari dai inje kiji ko menene" Sumayyah ta ce sannan ta nufi ɗakin Aunty Hunaisah inda suke tattaunawa har yanzu.
_*Ya kuka ga wannan labarin?*_
_*Kuna ganin zai bada ma'ana?*_
_*Ku a gani ku mai Ma'aruf ya sanarwa Hunaisah wanda ya sa jikinsu yayi sanyi.*__*Please do like*_
_*Share and*_
_*Comment*__*Domin shi zai yi determining how often zanyi posting.*_
_*Mummy's friend ce*_
YOU ARE READING
RAYUWATA
Spirituallabarine wanda ya ƙunshi tausayi, ha'inci, cin amana da sauransu. Hunaisah mutum ce wai matuƙar haƙuri da kawaici, amma rayuwa ya canza mata wanda yasa dole da tanka domin haƙuri idan yayi matsala ce wani sa'in. Kudai ku biyo ni kuji yanda wannan l...