54

83 7 0
                                    

Dawowanshi daga masallaci kenan,har yanzu yana teaching hospital din BAZE,tattara yanashi yanashi yayi ya hada suitcase dinshi ya fito da sauri sabida anyi laasar kuma yasan 4 lectures dinta zai kare,tausaya mata yayi albarkacin iyayensu zai bi ya dauketa tin da ba nisa sosai sai ma ya kaita wajen ummin da ta daga mishi hankali tinda last saturday their wedding was three weeks,har yazo zai shiga motarshi a parking lot yaga anshigo da emergency,ya saka abubuwanshi a motar ya shiga yazo zai wuce ta wajen da aka fito da wanda aka kawo din idanshi ya sauka akanta,zabura yayi ya fito sabida hango exactly Abayan dake jikin amnah da kuma macece saidai baiga fuskarta ba,da wani irin sauri ya karasa wajen bai koh samu nutsuwar rufe motar ba ya dai tura kofar mutanen yadinga ratsawa har ya isa inda aka kusan shigar da ita,wani irin jiri yaji yana dibanshi saka makon ganin amnah kwance fuskarta rufe da jini,har wajen ya karasa yana fadin"amnah,amnah mai yafaru" sai kawai ya saki salati ya riqe kanshi,itace,how,meyasameta waya mata haka,yaushe shi da ya barota lafiya kalau a school,doctors din da zasu yi mata aiki ne suka karaso,kwaya daya ne yasanshi a cikin su yasanshi da mamaki yace"Doctor lafiya"
Kallanshi kawai yakeyi dan yama manta da profession dinshi,bai ma san shi aka addressing as a doctor din ba,yana cikin shock sai da doctor din ya tabashi yace"calm down kasantane"
"She is my wife" ya fada ahankali not knowing daga ina maganar tasa ta fito,da sauri aka shigar da ita cikin ACCIDENT AND EMERGENCY,duk da police case ne kuma baa sanar dasu ba amma ganin Haieyder din aka shigar da ita sabida jinin da take zubarwa,har ciki ya shiga though he has no role to play a ciki,kawai yana tsaye yana kallan yanda ake saving dinta yama rasa mai zaiyi kwakwalwarshi ya cunkushe ya rasa yadda zaiyi,ahankali yaji anja hannunshi suka fita a ciki,doctor din dazunne dan suna gaisawa sosai suna respecting juna har sukan zauna suyita hiran duniya randa Haieyder yaga dama,a kofar suka tsaya ya kalli Haieyder yace"calm down,Allah zai bata lafiya Insha Allah kayi tawakkali,she has lost alot of blood sabida wani minor ciwo da taji a bayan kanta probably inda ta buge,so she need blood transfusion" ya fada very calmly da assurance acikin voice dinshi  da kuma kwantar da hankali,daga kai kawai Haieyder yayi yace"muje a dibi nawa,blood group dina is O"
"Alhamdulillah komai yazo da sauki,muje" ya fada...
After series of tests,blood dinshi is normal zai kuma iya donating,aka diba akaje aka saka mata...
Yana zaune a office dinshi ya rasa courage din kiran gida ya fada musu,har anyi magriba,anyi nasarar tsayar da bleeding din nata kuma ba internal bleeding,dazu bayan ya fito daga inda aka debi jininshi akace ana nemanshi,koh da yaje babban mutum ne amma bazaiyi sa'an su abba ba,ya karasa suka gaisa,kawai ya fara ba Haieyder hakuri,he explained the incident kuma bashi da laifi daga yanda Haieyder ya fahimta,tou koh ma yana dashi mai zaice mutum babba haka daya kusan sa'an mahaifinshi yamasan ya haifeshi,haka yace mishi bakomai ya karba iya abubuwanta da aka kawo tare dashi,Allah ya rufa asiri ma ba gudu yakeyi ba..
Blaiming kanshi kawai yakeyi akan dukkan abunda ya faru,tin farko da yabi shawarar kamal ya tafi office da duk hakan bata faru ba,he is guilty,ya rasa yadda zaiyi bashida courage da karfin kiran gidan nasu,time ya kalla it past 8,tashi yayi ya nufi dakin da aka kwantar da ita ya tura ahankali,tinda aka dawo da ita bata farka ba har yanzu kuma yakamata ace ta farka karasawa yayi ya zauna yana kallan face dinta that looks innocent,yes she looked innocent koh dan
Atana kwance ne oho,shi kanshi yanzu in zaa daureshi ace meyasa ya tsaneta bashida abun cewa sai dai yace"batada kunya",gani yake koh mutuwa tayi bata farfado ba laifinshi ne,kallanta kawai yakeyi yana tunani kala kala,yana tuna iya zamansu na three weeks din nan da yan kwanaki,yana tuna yanda take saka shi magana,ajiyar zuciya ya sauke yana kawai adduar Allah ya bata lafiya...
Ahankali ta bude idanta,ta kare ma saman kallo sannan ta juya kanta daya mata nauyi,yana zaune akan sallaya dan koh masallaci bai da karfin zuwa koh masallaci yanzu ya idar da isha...juyowa yayi tayi saurin rufe ido tanaso ta tuno abinda ya faru da ita amma ta kasa,the only thing she could remember is ta fito bayan tafiyan ameerah daga nan kuma tana cikin tafiya taji kaman abu ya bigeta da karfi daga nan batasan inda take ba sai yanzu da ta farfado,ji tayi ta tsane ganinshi,dama ba san ganinshi take ba..
Daga yanda yake ganin idanta na motsi yasan idanta biyu kawai rufewa tayi,tashi yayi ya nade sallayan ya karasa inda take ya mika hannu ya taba temperature dinta?ya ji jikin nata da dan zafi,ahankali kamar mai rada yace"How are you feeling" kin kulashi tayi?dan da ya saka mata hannu a goshi ma ji tayi kaman ta ture hannun amma ta shareshi,,"mai ke miki ciwo" sake kin kulashi tayi yace"tell me" fashe mishi tayi da kuka..kuka sosai takeyi kallanta ma ya tsayayi dan ya rasa mai zai ce,ahankali yace"toh menene"
"Ni wajen ammi zanje" ta fada cikin kuka kamar wata karamar yarinya,yarinyar nan so take ta kasheni yau,,"its late gobe insha Allah zasu zo"
Kuka ta cigaba dayi batareda ta saurareshi ba,ji yayi shima nashi kan yana ciwo yayi shuru kawai yana kallan yanda take kuka,shi tinda yake bai taba tsintar kanshi a cikin rudani da damuwa irinta yau ba,koh bude baki baiyi ba sai dazu ne ma daya dawo daga masallaci kafin ya taho wajen ta ya samu damar shan ruwa a office dinshi,"kinaso in kaiki wajen ammi right" ya fada ta sigar rarrashi,daga kai tayi ahankali batareda tayi magana ba yace"stop that tears now and answer me",ahankali ta ke rage kukan amma bata dena gaba daya ba,"ina ne keh miki ciwo" kanta ta nuna mishi da hannunta,"sai kuma ina" sai ta girgiza mishi kai,yace"okay,mai zakici toh"
"Babu" ta fada kamar ba yunwan takeji ba,batareda ya tsaya saurarenta ba yatashi yace"i will be back"
Fita yayi ya sa nurse ta tafi wajenta,ita ta taimaka mata tayi alwala dan jikinta kawai yan bruises ne sai ciwon dake bayan kan nata,a zaune tayi sallahn dan in ta tashi jiri takeji tana idarwa da magrib da isha sannan nurse din ta taimaka mata ta koma gadan Doctor daya yazo ya sake dubata sannan ya fita..
Eatery din da yake kusa yaje ya musu take away,not because yanasan cin abincin eatery amma sabida yanajin yunwa kuma itama ya kamata taci abinci...
Ahankali ya tura kofar dakin da sallama,nurse din na ganinshi ta tashi ya mata godiya sannan ta fice,yanaso ya tambayi amnahn mai ya faru da ita amma kuma she need to rest tukunna dan doctor din yace kar adameta da surutu da hayaniya,,tana kwance amma ba bacci takeyi ba ta juya mishi baya,,Kan karamin drawer din dake gefen gadon ya ajiye leather din hannunshi,,he can't even remember koh ya taba kiran sunanta inba dazu da aka kawota ba,ahankali yace"amnah tashi kici abinci" bai masan maiyasa yaketa dawainiya da itaba amma yafi mayar da hakan sabida laifinshi ne,koh inda yake bata kalla ba bare kuma yasaka ran zata kulashi,sake maimata mata yayi ya kara da koh bakisan zuwa wajen ammin,tashi tayi,ya zauna a bakin gadon ya miqa mata karba tayi ahankali ta faraci,dan bata da wani karfi ga yunwar da takeji,bata wani ci sosai ba taji ya isheta ta ajiye a gefe,bai takura mata ba ya miqa mata drink,ta dan sha yafi rabi sannan ya dauke ya ajiye akan bedside din...
"Kinyi sallah?"
Daga mishi kai tayi ya sauka a gadan dama ta matsu ya sauka dan ta tsani ta dinga jinta kusa dashi haka dukda jikinsu ma baya taba na juna,sallaya ya shimfida ya zauna yaci abincinshi.....

Married To Doctor HaieyderWhere stories live. Discover now