RUƊIN ƘURUCIYA 23-24

221 5 3
                                    

🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️

RUƊIN ƘURUCIYA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

Writer of

WATA KISSAR..(Sai mata)
ABDUL JALAL
AƘIDATA (paid book)
WUTA A MASAƘA
NOW RUƊIN ƘURUCIYA (paid book)

_Labarin RUƊIN ƘURUCIYA, na iya zuwa da wani salo, wanda baku saba ganinsa a rubutuna ba, hakan ya biyo bayan akan abunda aka gina labarin, wani abun ze ɓoyu wani Abun baze ɓoyu ba sakamakon labari ne akan teenegers, yara masu tashen Balaga, but hakan ba ya na nufin na sauka daga kan tsarin yadda nake Rubutu bane, ƙofata a buɗe take dan karɓar ƙorafi, gayra ko shawara_

⚠️⚠️⚠️ƘIRƘIRARREN LABARI NE, BAN YADDA A JUYAMIN SHI TA KOWACE SIGA BA SEDA IZININA ❌❌‼️

SHIN KUNA DA LABARIN MANHAJAR AREWABOOKS KUWA?
MANHAJA CE DA TAZO DA TSARIN DAN SAUƘAƘAWA MARUBUTA DA MAKARANTA SAUƘIN CINIKAYYAR LITATTAFAI.
TA IN DA ZAKU IYA SIYAN KOWANE FEJI AKAN KUƊI ƘALILAN, DAI DAI DA ALJIHUNKU.
INA FARINCIKIN SANAR DA KU CEWA, DA ZARAR NA KAMMALA FREE PAGES, ZAKU CIGABA DA SAMUN CIGABAN LITTAFIN RUƊIN ƘURUCIYA, AKAN MANHAJAR AREWABOOKS.
KARKU BARI A BAKU LABARI, AKWAI TARIN DARASIN RAYUWA A CIKIN LITTAFIN.

23_24




A hankali Sadik ya sauke ajiyar zuciya, ya saki hannuanta yace

"Farhan"

A hankali ta ɗago ido ta kalleshi, yai unlocking Motar yace "nagode Sosai da halartar bikin yayana, ki gaisarmin da Abba"

Ba tace masa komai ba, ta ɗau kayan da ya bata ta fita daga Motar, sedai gaba ɗaya taji jikinta yai sanyi.

Haka ta nufi layinsu dan kama hanyar gida.

Se da ta ƙule sannan Sadik ya kunna motar ya koma gurin taron bikin.

Yana komawa su Nas suka cigaba da tsokanar sa akan Farhan, su kai ta iya shegen su san ran su.

Sedai gaba ɗaya jikin Prince ɗin a sanyaye yake, ya dake ya ɓoye halin da ke damunsa, ya dinga biye musu.

Nas yace "Prince, wai ya batun movies ɗin da aka tura maka ne, ka kalla kuwa, kaga yadda ake madarar Love, ba irin wanda ku keyi ba, sekace masu wasan yara, dan Allah kai ba ka ji kunyar ka dinga nuna wannan Yarinyar kace budurwarka ce ba? Kalli kayan jikinta ta jibga uban mayafi kamar wadda zata ja salla....

Wani irin warning glance Prince yaiwa Nas, hakan ya sa Nas ɗin yin shiru.

Daf da magariba amma har a lokacin zuwa ake, har 'yan ajin su Farhan ma sun halarci taron bikin.

Sedai gaba ɗaya Haseena ta kasa sukuni, saboda kyan da Sadik yai a idonta, babban abunda yasa ta tsani Farhan bakomai bane illa kishi, gashi Sadik ɗin ba shi da fuskar da za tai masa shishshsigi, amma harga Allah yana matuƙar burgeta.

Yau ta ƙara tabattar da Sadik ƙyakyawa ne na gaske, dan ba ƙaramin cika ido da kwarjini yai a cikin manyan kaya ba, duk da ƙarancin shekarunsa, Allah yai masa ƙirar manya, dogo ne ga shi da jiki, wannan jikin ne ke ɓoye ainihin ƙuruciyar sa.

RUƊIN ƘURUCIYAWhere stories live. Discover now