🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
RUƊIN ƘURUCIYA
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P. W. A
*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)Writer of
WATA KISSAR..(Sai mata)
ABDUL JALAL
AƘIDATA (paid book)
WUTA A MASAƘA
NOW RUƊIN ƘURUCIYA (paid book)_Labarin RUƊIN ƘURUCIYA, na iya zuwa da wani salo, wanda baku saba ganinsa a rubutuna ba, hakan ya biyo bayan akan abunda aka gina labarin, wani abun ze ɓoyu wani Abun baze ɓoyu ba sakamakon labari ne akan teenegers, yara masu tashen Balaga, but hakan ba ya na nufin na sauka daga kan tsarin yadda nake Rubutu bane, ƙofata a buɗe take dan karɓar ƙorafi, gayra ko shawara_
⚠️⚠️⚠️ƘIRƘIRARREN LABARI NE, BAN YADDA A JUYAMIN SHI TA KOWACE SIGA BA SEDA IZININA ❌❌‼️
SHIN KUNA DA LABARIN MANHAJAR AREWABOOKS KUWA?
MANHAJA CE DA TAZO DA TSARIN DAN SAUƘAƘAWA MARUBUTA DA MAKARANTA SAUƘIN CINIKAYYAR LITATTAFAI.
TA IN DA ZAKU IYA SIYAN KOWANE FEJI AKAN KUƊI ƘALILAN, DAI DAI DA ALJIHUNKU.
INA FARINCIKIN SANAR DA KU CEWA, DA ZARAR NA KAMMALA FREE PAGES, ZAKU CIGABA DA SAMUN CIGABAN LITTAFIN RUƊIN ƘURUCIYA, AKAN MANHAJAR AREWABOOKS.
KARKU BARI A BAKU LABARI, AKWAI TARIN DARASIN RAYUWA A CIKIN LITTAFIN.30
Sosai Lilly take kokawa da numfashinta, dan ya dinga sauka cikin huhunta da sassan jikinta, amma abu ya gagara.
Sadik da ya taho daga ajinsu ne yai karo da ita a hanya a ƙasa.
"Subhanallah, ke meyafaru meya sameki haka?" Ya tsaya yana tambayar ta.
Ba ta iya magana, se numfashinta da ke tayin sama yana ƙasa.
Rasa abunyi Sadik yayi, ana haka sega su Nas, sun dawo daga inda suke zuwa shaye shayensu.
Nas yace "lafiya ita kuma wannan meya sameta take kwance a ƙasa?"
Sadik yace "nima ban sani ba, na taho ne kawai na ganta a kwance a nan"
Amin yace "to ai kamata yai ka ɗagata da ga ƙasan nan, ko Clinic ka kaita"
Sadik ya kalleshi yace "waye ze ɗagatan?"
"Kai mana" Nas y faɗa yana nunashi.
"Bana taɓa abunda ba nawa ba" Sadik ya basu amsa.
"Dallacan banza, ji wata ƙaryar wofi wai baya taɓa abunda ba nasa ba"
Sir Nazir ne ya sakko daga kan bene, hannunsa riƙe da litattafai alamar aji za shi, har ze tafi ya hangi su Sadik a tsaye a guri ɗaya.
Takawa yai ya ƙarasa in da suke tsaye, yaga Lilly a baje a gurin.
"Yasalam, meya sameta haka?"
Sadik ya ɗage kafaɗa alamar i don't know, ya ja da baya a hankali ya bar gurin.
Nazir yace "this is an emergency case, you are not supposed to stand just watching at her, what if her breath seize.
Be saurari me za suce ba, yasa hannu ya ɗagata yace suje ajinsu Lilly su kira masa mutum biyu a ƙawayenta, daga nan ya nufi Clinic da ita.
![](https://img.wattpad.com/cover/294853033-288-k55787e.jpg)