🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
RUƊIN ƘURUCIYA
RUƊIN ƘURUCIYA PAYMENT.
Dan Allah Dan Annabi, in kin san zaki sai littafi na dan ki fitarmin, ki barmin abina Please 🙏
Normal group 300 (posting ba kullum ba)
VIP 600 (posting kullum)
SP 1k (game son a dinga tura masa ta pc da zarar nayi typing)
Wanda zasu bi book ɗin akan Manhajar AREWABOOKS, suma zasu dinga samun posting kullum insha Allah.
A tura kuɗin ta wannan account ɗin
0009450228
Aisha Adam
Jaiz BankSe a turon evidence of payment 07063065680.
Tafiyar na da tsayi yanzu a aka fara, ba za kuyi dana sanin siyan book ɗin RUƊIN ƘURUCIYA ba Insha Allah.
Cool taku ce 🙏
(Bonus page)
31A hankali ya ƙaraso in da Farhan ke tsaye, yasa tattausan hannunsa ya riƙo nata, ya matse a hannunsa ya kalli cikin idonta. Hakan ya saukar mata da kasala ta sunkuyar da kai daga kallonsa saboda kwarjinin da yai mata.
A hankali cikin wata irin murya da ita kaɗai take jin meyake cewa yace "A karo na biyu bayan neman soyayyar ki, zan nemi Alfarma a gurinki Farhan, dan Allah ki amince na gaji da abunda suke min akanki Please Farhan"
Shiru tayi tana jin yadda zuciyarta ke wani irin bugawa, gumi keta keto mata kota ina, ba ta gama yanke hukunci ba, taji Sadik ya haɗata da jikinsa, ya haɗe bakinsa da nata.
Wata irin tsuma jikinta yake yi, ta rasa gane a wani yanayi take, tsoro ko kuma haushin Sadik, duk da yadda Sadik ɗin ya riƙeta gam, amma ji take tamkar zata faɗi ƙasa, dan haka ta sa hannu ta rirriƙe shi karta faɗi.
Wani irin ihu da shewa suka ɗauka a gurin nan Gaba ɗaya, seda mintuna uku suka cika cif sannan Sadik ya cika Farhan.
Idanunta sunyi rau rau kamar za tai kuka, se ajiyar zuciya take kamar wadda tai gudu.
Nan akaita tafa musu, Nas yace "Weldon gaskiya abokinmu da his wife to be, kun burge kun ƙayatar kuma ka tabattar mana da cewa kai....." Se kuma yaƙi ƙarasawa.
Aka yanka cake amma sam Farhan hankalinta baya jikinta, ji take tamkar ta aikata wani gagarumin zunubi da Allah baze yafe mata ba, take taji nadamar zuwa gurin partyn ta baibaye ta.
Da sauri ta silale ta tafi in da aka shiryata, ta cire rigar jikinta ta ɗau kayanta ta saka, wasu irin hawayen nadama suka shiga zarya a fuskarta.
Ta fito harabar gurin tana ƙoƙarin fita Sadik ya biyota yana ƙwala mata kira, amma taƙi tsayawa, cikin hanzari ya koma ya ɗakko mota, yaja ta da gudu yabi bayanta.
Su Nas kuwa dariyar mugunta suka dinga yi, Amin yace "wannan ne karonsa na farko da yayi, amma kamar ƙwararre dama can a matse yake, da haka da haka dai"
Babba yace "Aiku kuka ɓata abun da kuka hana ai amfani da ƙwayar nan wallahi"
"Dan ubanka idan anyi amfani da ƙwaya muyi yaya da su a gurin nan? Kuma ka san ba komai ake bashi ya karɓa ya ci ba, amma sannu a hankali se mun sa shi a layi"
Amin yace "hakane, Amma a hakan ma muny nasara ai"
Suka cigaba da dariyar mugunta.
Wani wawan parking Sadik yai a gaban Farhan, ya sakko yana faɗin "Farhan meye hakane kikeyi? Ki tsaya in maida ke gida mana"