*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
_All thanks be to Glory Almighty Allah for giving me the ability to write this book...the entirely book is dedicated to *Hafsat Abdullahi Hassan,* & *Halima Nuhu Muƙaddas,* my special greetings to you guyz masu halin ƙwarai🥰...my lovely fans that have been waiting for my new book i greet you all with respect😍ina yi maku barka da sallah fatan mun sha ruwa lafiya Allah ya karɓi ibadunmu Ammeen._
_Before the trip began let me said this out, i won't be updating daily so don't expect much, zan ke yin updating ne a duk lokacin da na sami dama due to some projects da nake kai, and as soon as ASUU call of the strike to fa sai yanda ku ka gani😅,hope you will understand me🥰and i hoped u will enjoy the story._
_*LULLUƁIN BIRI* its a fictional story. the names, characters, places and everything are all the product of author's imagination, so any resemblance to actual person a ɗauki hakan a matsayin coincendence...__Ina fatan zan sami haɗin kanku tun daga farkon wannan tafiya har zuwa ƙarshe. yanda na fara lafiya Allah yasa na gama lafiya._
*1*
*APRIL 20th 2021.*
*American Hospital Dubai, 2:30pm.*_"hey don't move, we are us navy seals...God! Damn it...we have a tango in the north wing every week. stop! stop! stop!...great team work guys, yeah we will mark you for the assist on this one."_
sautin dake fitowa kenan daga cikin ƙatuwar plasma ɗin dake manne a bangon ofishin, cikin wani american film me suna Steel Brigade. dai-dai lokacin da sojojin suka kama mutumin da ke sanye da mask, dai-dai lokacin Yusuf dake juyi akan kujerarsa yasa tafukan hannunsa duka biyu ya shafo fuskarsa tare da fitar da iska daga bakinsa. "ohh dammm it".
"ai na faɗa maka sai sun kama shi". Kalid wanda har yanzu bai ɗauke idonsa daga kallon tv ɗin ba ya faɗa a sa'ilin da duka haƙoran gabansa ke bayyana a waje alamar yayi farin ciki da abinda ya faru.
Yusuf ya ƙara juyawa akan kujerarsa zuwa gefe guda sannan yay guntun tsaki yace,"ko waye producer ɗin nan sam bai iya tsara film ba".
"hhh to ai hakan shine dai-dai, kai kana kallon sojojin nan kasan bana banza ba ne...kuma gwara a kama shi tun a farko, wasan zai fi tafiya dai-dai".
"kuma wataƙila ya suɓuce masu ba".
"ta ya ya?, macece fa ai da kamar wuya ta iya ƙwacewa"."wannan ai ba mace ba ce".
"bari su buɗe fuskar zaka gani, ai yanayin gudun kaɗai zaka fahimci macece, itama ba me kamar maza ba".shirun Kalid ɗin ya haɗe da sanda sautin maganar film ɗin ta ci gaba da tafiya, nan sukai shiru suna ci gaba da kallon.
_"get the mask!!...there is no harmful in the air we already checked, expect for the thorpe's breath."_ ɗaya cikin sojojin yay maganar a tsawace inda a take ya fizge mask ɗin daga fuskar mutumin, kuma lokaci ɗaya zaton Khalid ya bayyana, hakan kuma ya wanzar da dariya a fuskarsa, nan ya juyo ya kalli Yusuf dake aikin jan gajeran tsaki babu ƙaƙƙautawa alamun ba hakan yaso ba.
lokacin da Yusuf ya buɗi baki zaiyi magana lokacin ƙofar ofishin tayi ƙara, aka turota a hankali inda wata matashiyar budurwa ta bayyana hannunta riƙe da wasu takardu, jikinta kuma sanye da unifom na ma'aikatan jinya. ta mayar da ƙofar ta rufe sannan ta ƙaraso cikin ofishin tana ƙarasawa gaban tebirin da Yusuf ke zaune kan kujera yana juyawa gefe zuwa gefe a hankali.
cike da girmamawa ta rissinar da kanta tare da aje fayel ɗin hannunta akan teburin tana tura su zuwa gaban Yusuf. "Ranka ya daɗe ga result ɗin da aka samu". ta faɗa sanda ta ke harɗe hannayenta zuwa baya.
"ta farka ne?". Yusuf ɗin ya tambaya a sa'ilin da yake buɗe fayel ɗin yana dubawa.
"ehh ranka ya daɗe ta farka wajen ƙarfe ɗaya da minti goma sha biyu, amma bata fi sakan huɗu ba ta koma, da alamu dai har yanzu da saura kamin ta dawo hayyacinta".