*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
*8*
Idanuwan Turaki da Zaytuna suka ware akan Maama da ta shigo fuska babu yabo babu fallasa, suka bita da kallo har ta zauna kan kujera ta harɗe ƙafafu tana girgiza su. Dukansu suka sauke numfashi mai nauyi dan sun san tunda suka kalla fuskarta a haka to lallai akwai damuwa."ɗauki wayar nan ki kira min Bello". Muryan Hajiya Madina ta fito da wani irin amon sauti.
Zaytuna ta ɗauki wayar Turaki dake kan cinyarsa, tabi kiran Bello da suka gama waya da Turaki babu jimawa. ta miƙe ta isa ga kujerar da ta ke ta bata wayar, a kiran farko bai picking ba sai ana biyu, shima sai daya kusa katsewa tukunna.
Daga ɓangaren Bello yace,"Turaki ya dai?".
Hajiya Madina ta numfasa tace,"Bello ba shi ba ne".
Jin muryarta yay saurin gyara zama daga inda yake, ya gyara yanayin muryarsa, cike da ladabi ya gaisheta, ta amsa masa tare da tambayarsa ya aiki, yace mata aiki alhamdulillah.Shiru na ƴan sakanni ya biyo baya, Turaki dai kallonta kawai yake, kiran Bello da tayi na menene?, me zata ce da shi?, to me ya faru ma tukunna?, dan yanayin fuskarta kaɗai yana shaida cewar there most be something behind.
"kana jina Bello?". ta faɗa a sanda ta ke yiwa Zaytuna nuni da dining area, inda a lokacin Zaytuna ta miƙe ta isa wurin dining ɗin, ta ɗauki cup ta tsiyaya watermelon juice aciki, ta ajiye jug ɗin sannan ta dawo ta miƙawa Maama.
"ina jinki Maama".
lemun dake hannunta ta kurɓa kamin tace da shi,"application for annual leave, ina ce ka miƙa musu ko?".Yace,"ehh Maama na miƙa tun a washe garin ranar da yay accident ɗin".
Tace,"good, how many months kasa?".
yace,"munyi waya da shi yace na saka just 1 week".ta ɗago ido ta yiwa Turaki wani kallo na ashe baka da hankali, hakan kuma yasa yay saurin sauke idonsa ƙasa, duk da bai san akan mene kallon ba tunda ba jin abinda Bello yace yake ba, amma wannan kallon yasan ba a banza ba.
Ta kalla goshinsa da ƙaton plaster ke manne a wajen, sannan ta tsurawa kafaɗarsa ido, tana hasko yanda wajen ke nannaɗe da bandage kwanaki biyar da suka wuce kamin jiya a kwance, ai har yanzu hannunsa na hagu baya moving sosai, amma shine saboda bai da cikakken saiti, yay wannan mummunan accident ɗin sannan yace wai hutun just 7days ya ɗauka, which means monday zai koma aiki.
Tai gajeren tsaki, ta lura Turaki nema yake ya kashe kansa a bautar company kawai, yafi damuwa da aikinsa akan lafiyarsa da rayuwarsa, to ita ba ƴar iskar uwa ba ce. Ko da yake shima Bello ba shi da hankalin ai, yana kallo har kusan fitar da rai sukai da Turaki, basu taɓa zaton zai farka ba saboda mugun ciwukan daya ji, amma shine har yake biye masa da ɗaukan hutu na kwana bakwai kawai.
Daga ɓangaren Bello so yake yay magana amma yana gudun faɗan da zai biyo baya, dan shima sai bayan daya kai takardar yaga yayi rashin tunani. ta katse tunaninsa da cewan,"then write a resignation letter ka ƙara kaiwa".
Turaki da Zaytuna duka a lokaci guda suka ɗago ido suna kallonta da mamaki tsantsa, hatta Bello daga inda yake bai san lokacin daya miƙe daga zaune ba, yana daɗa tambayarta abunda tace.
"ehh resignation letter nace, takardan barin aiki ba, And if you can't tell me sai na saka Khalil ya rubuta ya kai".
Bello ya haɗiye wani yawu yace,"amma Maama hakan sai nake ganin will not be the best solution, we should just add him a days more off...idan ya dawo sai a san zaman da za'ai da Manager to let him know what is going on".a fusace tace,"karka rubuta ka bari zan rubuta sai na bawa wanda na isa da shi ya kawo, kuma ai dama ban kira na faɗa maka don neman shawaranka bane, umarni nake baka tunanina cewar na isa matsayin mahaifiyar amininka".