4

168 25 4
                                    

🦎 *KAƊANGARUWA*🦎

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
( *home of expert and perfect writers*)

           *NA:* *SLIMZY*✍🏻
          Wattpad@slimzy33

                        *4*
Cikin fushi Amina take tunda take babu mahalukin Daya taba bata Mata Rai haka babu Wanda ya taba wulakantata babu Mai tabata ya zauna lafiya haka Amina ta rinka rikida cikin fushi babu kalar K'ADANGARUWAR da Bata koma ba a haka ta rikida ta koma bakar K'ADANGARUWA wadanda tunda take rikida bata taba komawa Baka BA sai yau lallai yau sun tsokalo tsuliyar dodo Amma da sannu zasusan waye ita rimi tayi ta Zama katuwar kadangaruwa harta kere katangar gidan hango wata mota tayi ta nufo gidan tayi saurin zubewa Kasa sharafff karar zubewar Amina yasa ummah zabura ta Mike tana duba Daya daga cikin Yan matan uku dake parlorn wankan tarwada wadda ita kadaice batayi magana ba "sameeha ya dai tun dazun dik abinda akeyi Baki tanka ba sai cigaba da kikeyi da daddana waya tamkar bakiji me mukeba yanzun karar meye wanan?"yatsina fuska sameeha tayi cike da takaici ta dubi ummah take taga sameeha tayi kwal kwal da Ido tasan meye kishin ganin Amina na kallon hoton abba shine tun dazun ta Kasa magana murmushi ummah tayi "taho nan yar ummah nasan abinda ya hanaki magana ki kwantar da hankalinki babu abinda abba zaiyi da wanan bakauyar"ta jinjina Kai sai hawaye "ummah nidai jinina Sam Bai hadu da itaba balle daga zuwanta ta kafemun abbah da Ido a koreta kawai"

Murmushi ummah tayi "sameeha na tabbatar wanan bakauyar bazata iya aikin gidan nan ba Dan haka dole Zan sallameta hayaniya ce ta cika gidan nan ummah suka saki maganar da sukeyi ummah ta soma musu oyoyo Yan samari biyu ne da Yan Mata biyu sai karamar kanwarsu "oyoyo oyoyo oyoyo mutanen Abuja saukar yaushe?"dukkansu wuri sukayiwa kansu cike da gajiya nan ummah tacewa sameehah jeki kiramun waccen yarinyar ta kawo musu abinsha,
Da sauri sameeha ta Mike dama neman yadda Zata hadu da Amina takeyi ta zagaya ta Baya bata ganta ba ta dawo har Zata Shiga ciki ta hangota tsaye ta rike kwankwaso tsayuwar ma a lakwashe tayita ta taho cike da kishi ta fuzgo Amina da sauri Amina ta juyo taga waye sai taga Daya daga cikin Yan matan Wanda batayi magana ba dik cin Kashin da Ake musu,galala Amina tayi tana kallonta Dan tsayuwar da tayi tana tunanin ita kadaice Mai kirki Kila Kota wajenta zataji sanyi saitaga dik kanwar Ka ce...idonta ne sukayi wani Kala Wanda take sameehah taji yarrrr saidai masifa ta hanata Jin tsoron sosai cikin tsawa tace "ke meye haka kike kallona kamar wata mayya?ko nida mijin nawa zaki hadamu ki cinye kamar yadda kikeda niyyar cinyemunshi?"Sam Amina bata fahimci me sameeha ke nufiba sai ma kallonta da takeyi wani iri ta langabar da Kai sameeha ta cigaba da magana "to ki Bude kunnenki da kunnen basira ki saurareni wanan da kikaga hotonsa a parlor kika kureshi da Ido mijina ne Kar insake ganin kin kafeshi da idanuwan nan naki Masu kama da Bana mutane ba"sai lokacin Amina ta gane Mai take nufi cije lebe tayi cike da takaici ko minti arbain batayiba da zuwa Amma wadanan mutanen sun nuna Mata kalarsu a fili kalar Yan birni dama ance haka Yan birni suke yau gashi ta gani ji tayi kanta na juyawa tana neman zubewa a Kasa cikin sauri ta durkusa ta dafa hannunta Kasa tana kokarin saita natsuwarta sai hawaye "dalla tashi muje makira hajiya tayi Baki ki kawo musu abinsha muje"ta dagota wani nauyi taji tayi saurin sakinta tace "sai shegen nauyi anci tuwon dawa Dana masara a kauye"haka Amina ta biyo bayanta har cikin parlorn ummah nata hira da bakinta "yauwa ke bakauya nace ya sunanki?"take wadanda ke parlorn suka tuntsire da dariya Yan matan Banda samarin har suna hada Baki wajen fadin "ummah kin bamu dariya sunanta kenan bakauya suka sake shekewa da dariya",Amina ta sadda kanta Kasa bataga laifinsu ba sai laifin ummah Dan itace ta tozartata kin magana tayi ummah ta sake fadin "ke bazaki fadamun sunanki ba saina kwada Miki Mari"Amina tayi saurin dagowa ta kalleta cikin ranta tace shine Mafi kuskuren da zakiyi a rayuwa ki mareni ni Amina K'ADANGARUWA.....sai tace cikin wata irin murya a dakile "sunana Amina"parlorn yayi shiru suna saurarenta ummah ta dubi sameeha tace "jeki hada Mata lemu da ruwa ta kawo musu kinsan yau aka kawota batasan Kan gidan ba sai zuwa kwana biyu",sameeha tadan bata Rai jimm kadan sanan ta Mike tayi gaba Amina tabi bayanta suna Shiga kitchen nan Amina ta shagala da kallon kitchen ko ina binsa takeyi da kallo Komi kall kall kamar baa rayuwa shin aikin me zatayi a nan take tambayar kanta samm ta tafi duniyar tunani Saida sameeha ta daka Mata tsawa tana Mika Mata tray din lemu da ruwa na gora "ke karbi nan bakauyar daji ki Kai ki dawo ki dauko na cups"wani kallo Amina tayi Mata ta jinjina Kai kawai tayi gaba.....
  Shiru sameeha tayi tana nazarin kallon da Amina tayi Mata sai kawai tayi kwafa ta kwaso drinks din ta biyota dashi ta ajiye ta juya abinta Amina kuwa tana direwa juyawa tayi Zata fice ummah ta tsaidata "ke Amina jeki kitchen Zan turo fadeela ta Nuna Miki yadda muke abinci dikda nasan ba iyawa kikayiba dole ma mu nemi Mai aikin abinci"ta jinjina Kai kawai ta fice,Daya daga cikin samarin dake parlor yace"ummah halan dai kurma ce yarinyar nan ko Naga kawai ko magana akayi Mata da Ido take bada amsa ko da Kai"

"Ba kurma bace sudais tsabar iskanci ne irin Na kauye inkana neman tattacen Dan iska to kasamu Dan kauye"suka sheke da dariya yace "wai Kam yaushe mutanen turai zasu dawo?"

Shiru ummah tayi tace "kamar karshen wata yace yanada hutun sati biyu Dan haka gida zaizo"sudais ya jinjina Kai.....

*****
Kauye.....

Ahmadi zaune yake yayi zugum tunda abun nan ya faru dashi yake cike da tunanin yarinyar nan nemanta yakeyi ya roki gafararta dikda an tabbatar musu da ba mutum bace Amma yanaji a jikinsa mutum ce  kawai dai itadin wata halitta ce ta daban...runtse idonsa yayi fuskarta yake hangowa irin kallon da take masa wani juyi yayi ya mike kafarsa ya tungular da kofin kunun da aka ajiye masa da kosai kusan awa biyu,

Mahaifitarsa da mahaifinsa Malam iro a tare suka yaye labulen dakin hade da sallama...yayi nisa a duniyar tunani idonsa na kallon wani sashi na dakin kallon juna sukayi sai kawai mamansa ta fashe da kuka "shikenan Malam nafada maka gamo yaron nan yayi kuma Mai maganin nan Bai Fadi daidai ba Malam kawai dai an jefarmin yaro ne Dan anga yadanyi karatun nan nazamani shine akeso aga bayansa ta hanyar amfani da aljana"Malam iro ya girgiza Kai "ko Daya innar Amadu kawai dai Shi yasan meyayiwa wanan aljanar ta jefasa cikin wanan garirin"

Ahmadi kuwa ajiyar zuciya yayi ya dubesu cike da damuwa "Baba yaushe Zan sake sata a idanuwana inaso inganta inaso in roketa gafara kuma in taimaketa Dan alamu sun Nuna tana neman taimako a yanayin Dana ganta tamkar batada gata"

Innar ahmadu ta Kara fashewa da kuka tace "kajiko kaji abinda yake fada Malam gaskiya bazan yardaba Malam mu canja wajen Mai magani"

"Innah nifa babu wani waje dayakemun ciwo kawai dai inajin K'ADANGARUWA nayimun yawo a cikin jikina ne wani lokacin sanan Dana rufe idona ita nake gani"Malam iro yayi shiru cike da dimuwa yace "innar ahmadu barin garin nan zamuyi da ahmadu ya tafi birni kawai ya tafi can Kano wajen Dan uwana ya zauna har yasamu lafiya tunda dama sunso sashi a kasuwanci a can Kano din hakan batasamuba sakamakon uzura musu da nayi Akan su dawomin dashi ya koma Gona kinga Yana kasuwancinsa Ya koma karatun kawai"....samm innah batason komawar ahmadi tasawa Malam iro kuka "Dana kwaya Daya tilo ace ya koma birni ya koma dabiu irin na Yan birni a hakan ma ya aka cika dik kauyen nan cewa akeyi yanada wulakanci da izgili"
Malam iro yace "to waye yasani ko Abunda yayiwa aljana Kenan take horashi"itadai ficewa tayi Malam iro ya nemi waje ya zauna gefen ahmadi yace "kayita addua muna tayaka Amma tabbas dole zaka koma can Kano wajen Dan uwana"ahmadi ya jinjina Kai Sam bayason magana so yakeyi mahaifinsa ya fita daga dakin yasamu Damar tunaninta ,minti goma Malam iro Yana tofeshi da addua bacci ya dauke ahmadi cikin baccinsa kuwa mafarki yayi......

********
  Tsaye take tana kallon yadda fadeelah ke gabatar da Komi dikda itama gwajin gwala takeyi ba iya abincin tayi ba harde hannuwanta tayi tana kallonta daga bisani tayi murmushi ta juya Baya....cikin store fadeela ta Shiga ta dibo shinkafa a razane ta fito tana kwalla wata gigitacciyar Kara Wanda tuni ummah da sauran Yan matan suka runtumo aguje....Amina kuwa sulalewa tayi ta fice daga kitchen din suna Shiga kamar an rufe kofar dasu nan ummah da sameehah numfashinsu ya Shiga kokawa da juna irin zabgegiyar K'ADANGARUWA da take tsaye Akan kafafuwanta tana tunkarosu......



*Repost*......*free book ne ina bukatar ganin comments ko in ajiye alkalamina*✍🏻😎

*SLIMZY*✍🏻

K'ADANGARUWAWhere stories live. Discover now